An shardanta Azumin a dukan addinan da ke bin
koyarwan Ibrahim
Addinan Yahudu, Nasara da Musulunci duk sun ayyana yin azumi. Musa ya yi azumi
na kwana arbai’in a Dutsin Sinai a lokacin wahayin Dokoki Goma. (Exodus 24:18) Duk
da an rage yi yanzu, al’adan Yahudawa ne a yi azumi lokacin makoki ko kuma a cikin
tsoro. Yawancin Yahudawa da ke aiki da koyar war addini suna azumi a Ranar
Atonement kuma aa sati-daya na juyayin rusa Jerusalem a 597 B.C. Isa of Nazareth,
tsarki ya tabbata a gare shi, yayi azumin Ranar Atonement da kuma kwana arba’in da
Musa yayi azumi dan ya kauce wa wasiwasin shaidan.
“Sai Ruhi ya ingiza Isa zuwa hamada don Shaidan ya kwadaitar da shi. Bayan azumin
wuni arba’in da dare arba’in, sai ya ji yunwa.” (Matthew 4:2)
Kristoci da dama suna yin azumin kafun Easter na kwana arba’in, ko da yake yanzu ya
kunshi kiyayewa daga wasu daga cikinkayan abinci ne maimakon dukan abinci da ruwa.
Musulmai suna azumin watan Ramadana kuma suna iya azumi a mafi yawn shekaru na
shekara, ba a tilasta ba.
Allah Daya ya umurci azumi wa muminai; kuma tana da falaloli masu yawan gaske.
Kayan ji dadi na duniya ana iya jimlace su cikin abinci da na sha, jima’i, da nishadi.
Azumi yana bukatan kiyayewa daga wadannan ababe, yin abu sabanin ababen da jikin
Mutum a tsarin shi yake kiran shi da ya yi don yabi umurnin Allah.Wannan yana ginawa
da kuma karfafa iya juriyan da mutum ke da shi, ya kais hi ga kusanci da Mahaliccinshi.
Wasu falalolin azumi sun kunshi:
Azumi yana koyar sa hakuri, ya koyar da juriya da yin da’a.
Azumi yana kara jin kai ga marasa galihu.
Azumi na gina dagewa a aikin gyara ruhi da kuma rushe damuwa da son duniya.
Azumi yana da amfani da dama ga lafiyar jiki.
Azumi na iya zaman dalilin samun rabauta daga zunubi da kuma samun lada mai yawa.
Azumi na daga cikin tsari mai kwari na gyara ruhi da jiki.
Azumi na juyayin lokuta masu muhimmanci na addini.
Azumin Musulmai na watan Ramadan chigaban dogon tarihin azumi na masu bin
addinan da suke bin koyarwar Ibrahim. Karuwan da ake yi na gyaran kawuka in anyi
azumi ya maida shi hanya mai muhimmanci wajen kara imanin mutum da kuma aiki da
koyarwan addini.
“Da maza masu azumi da mata masu azumi…Allah ya shirya
masu gafara da lada mai yawa.”
( Alkur’ani 33:35)
Me azumin watan Ramadan ya kunsa?
A takaice, azumi ya kunshi gujewa daga dukan abinci, shaye-shaye, maganan banza, da
jima’i ga ma’aurata daga kafun ketowan alfijir lokacin da sama yayi haske za a iya
bambanta bakin zare daga farin zaren horizon, har zuwa bayan faduwar rana lokacin da
jan launi ya bar rabin Gabashin sama. Wasu mutane basa iya azumi dan shekaru sun ja,
rashin lafiya, yanayin juna biyu, da sauransu, sai a bada sadaka a maimakon, da/ko kuma
a maida azumin da aka sha daga baya.
Ko da yake asalin ruhin watan Ramadan ya kece kiyayewa daga wasu abubuwa ‘yan
kadan kawai. Lokaci ne da za a dage da karfafa kwazo dan samun kamala a lamarin
neman kusanci ga Allah.
“Kuna jin kishi da yunwa, ku ji shi ku yi rayuwa cikin shi, anan kuma yanzu, ku kawo a
hankalinku tsananin wahala da kaifin kishi da yunwa da zai kasance yanayin ranan a
Ranan tashin Kiyama.
Bada sadaka wa talakoki da marasa galihu.
Darajta iyaye da manya.
Yin kirki da nuna soyayya ga ‘yayanka da yara.
Kula da nuna kaunaga ‘yan uwa .
Kiyayayewa daga ba wa harce abun da bai kamata ba a ko rada shi ba.
Kulle idonka daga abun day a kasance ba mutunci a kale shi.
Toshe kunnenka daga abun da zai kasance sabo mai tsanani a ji shi.
Ka zama mai tausayi,hankali da kirki wa marayu saboda in ba ka nan, yaranka, in
da bukata, su ma za su kula daga wajen wasu.
Ka tuba zuwa ga Allah ka samu kusanci da shi.”
- Annabin Tsira,tsarki ya tabbata a gare shi da iyalin shi
Ban da yin azumi da kokarin hali na kwarai, Musulmai suna bada lokacin su da karfin su
wajen sallah da addu’a zuwa ga Allah daya kadaitacce. Cikin wassu dararruka na
wannan watan, Musulmai za su kasance a farke dukkan daren suna ibada.
Bayan rana na karshe na watan Ramadan, Musulmai suna bikin Eid ul Fitr dan su
karrama gama azumi. Su na taruwa dan sallah, cin abinci, da kuma rarraba guzuri
daiden gwargwado (musamman ma yara). Ban da haka, rana ne mai cike da jimami,
saboda watan Ramadana mai albarka da dukan dama da yake badawa na tuba da lada ya
wuce sai wani shekara.
“Ina neman tsari da kirkin da Ka fi karkata ga, Ya Ubangiji, kar karshen wannan
daren ya waye, ko watan Ramadana yazo karshe, kuma na kasance ha ilau cikin
wanda aka kama cikin (ba a yafe ba) zunubi, wanda za a iya azabtarwa, a Ranar da za
a tsai da ni a gaban Ka.”
[Daga addu’ar ranar karshe na Ramadan, wanda Imam Jafar as-Sadiq,tsarki ya
tabbata a garish, ya koyar]
via: www.ibnnasiry.blogspot.com, www.mrnasir.blogspot.com and www.ibnnasiry.wordpress.com