1
Vacin Tafarkin
Da Aqidojinsu
Bugu na Uku
Na
Umar Muhammad Labxo
Tsohon Shugaban Jami’ar Musulunci
Ta Katsina
2
Abubuwan Dake Ciki
Gabatarwar …………………………………
Babi na Xaya: Tarihin Shi’a da Rabe-Rabensu……..
Sunan Qungiyar…………………………
Vullar Shi’a……………………………..
Yaxuwar Shi’anci………………………
Qungiyoyin Rafilawa da Ressansu…….
Babi na Biyu:Aqidojin Shi’a………….
Aqidar Bada…………………………..
Aqidar Sauya Qur’ani…………………
Aqidar Imama…………………………
Aqidar Shi’a Dangane da Sahabbai…..
Aqidar Raja’a…………………………
Aqidar Taqiya…………………………
Babi na Uku: Matsayin Shi’a a Cikin Al’umma……
Shi’a da Ahlul Baiti……………………
Ahlul Baiti da Shi’a……………………
Maganar Ali binu Abi Xalib…………..
Maganar Hassan binu Ali……………..
Maganar Hussain binu Ali……………
Maganar Ali binu Hussain……………
Maganar Muhammad binu Ali………..
Maganar Ja’afar binu Muhammad……
Shi’a da Ahlus Sunna…………………
Sukansu ga Muqatil…………………..
Sukansu ga Muhammad binu Sirina….
3
Sukansu ga Zuhuri……………………
Sukansu ga Sha’abi……………………
Sukansu ga Imaman Mazhabobi………
Sukansu ga Imam Abu Hanifa…………
Sukansu ga Imam Malik……………….
Sukansu ga Imam Shafi’i………………
Sukansu ga Imam Ahmad………………
Sukan Rafilawa ga Malaman Hadisi……
Sukansu ga Imam Bukhari……………..
Sukansu ga Imam Muslim…………….
Ahlus Sunna da Shi’a…………………
Maganar Sufyan Althauri…………….
Maganar Imam Abu Hanifa………….
Maganar Imam Malik………………..
Maganar Imam Shafi’i………………..
Maganar Imam Ahmad………………..
Maganar Imam Bukhari……………….
Maganar Imam Xahawi……………….
Maganar Alqali Iyal…………………..
Maganar Ibnu Taimiya………………..
Maganar Muhammad binu Abdulwahhab..
Maganar Mujaddadi Xanfodiyo…………
Mugun Nufin Rafilawa ga Al’umma…….
Baqin Tarihin ‘Yan Shi’a………………..
Babi na Huxu: Fiqihun ‘Yan Shi’a………
Mutu’a: Auren Wucin Gadi………………
Falalarta…………………………………..
Ladanta……………………………………
Gargaxi ga Wanda ya qi Yinta……………
Xaurin Auren Mutu’a……………………..
Sadaki ko Lada?…………………………..
4
Da Wa Ake Mutu’a?……………………...
Ana Yi da Matar Aure!…………………...
Ana Yi da Qaramar Yarinya……………...
Mai Mutu’a, Matanka Nawa?…………….
Aron Farji…………………………………
Babi na Biyar: Yaxuwar Shi’a a Nijeriya..
Alzakzaki da Yaxuwar Shi’a…………….
Dalilan Yaxuwar Shi’a a Nijeriya……….
Dalili na Farko: Gazawar Malamai………
Dalili na Biyu: Jahilci……………………
Dalili na Uku: Talauci……………………
Dalili na Huxu: Tavarvarewar Zamantakewa………
Dalili na Biyar: Gazawar Masu Mulki……
Yanayin Yaxuwar Shi’a a Yau…………...
Rufewa……………………………………
5
GABATARWA
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai
Lallai godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, muna neman gafara tasa. Muna neman tsari da Allah daga sharrin kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Wanda Allah ya shirye shi, babu mai batar da shi kuma wanda ya batar babu mai shiriya tasa. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa Muhammad bawansa ne, kuma Ma’aikinsa ne. Tsira da aminci su tabbata a gare shi, da Alayensa, da Sahabbansa, da wadanda suka bi Sunnarsa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka babu shakka wanda duk ya yi darasun Shi’a, ya karanci tarihinta da akidojinta da manufofinta, zai sani a yakini cewa kungiyar an kafa ta ne kawai domin yakar Musulunci da kokarin rusa shi daga ciki. Yahudawa da Majusawa, wadanda Musulunci ya buwaye su a fagen fama, sun koma bin turbar munafunci da yaudara suka kafa Shi’a a matsayin kungiyar asiri wacce suka yi fatan amfani da ita domin cimma manufarsu ta ganin bayan Musulunci.
6
Shi ya sa akidojin Shi’a suke warware akidojin Musulunci daya bayan daya, kamar yadda manufofinta suke karo da manufofin sa. Wata babbar illa wacce take nuna mugunyar manufar wadanda suka assasa Shi’a shi ne yadda suke tarbiyar mabiyansu a kan kiyayya ga Musulmi da son ta da hankali da kishin zubar da jini.
A farkon fitowar wannan littafi shekaru shida da suka wuce mun yi gargadi cewa yaduwar Shi’a a kasar nan MATSALA CE TA TSARO, ba wai kurum ta addini da zamantakewa ba. A yau abubuwan da suka faru tun daga wannan lokaci sun tabbatar da ingancin wannan gargadi. Bayan kisan gilla da ‘ya’yan wannan kungiya suka yiwa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, kuma hukuma da kanta ta bincika makarantu, gidaje da ofisoshin wannan kungiya inda aka gano muggan makamai da bayanai masu nuna mugun nufi da aikata laifi. A sakamakon irin wannan bincike da aka yi a Sakkwato, ga misali, gwamnatin jihar ta dauki matakin rushe babbar cibiyar ‘yan Shi’a da suke kira Markaz a garin, kuma da yawa daga cikin ‘ya’yanta da shugabanninta an gabatar da su gaban shari’a inda aka same su da manyan laifuka.
Wajibi ne gwamnatocin sauran jihohi kada su jira sai abinda ya faru a jihar Sakkwato ya faru a garuruwa da
7
biranensu. Tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa hakki ne a kan hukuma kuma riga-kafi ya fi magani. Ba ya daga cikin hikima a jira sai barna ta afku sa’an nan a kafa kwamitocin bincike, a koma ana fadan goggo a kofa. Lallai ne gwamnati ta dauki matakai na hakika a kan duk wata kungiya wacce take dauke da makamai ba bisa ka’ida ba.
Su kuwa daidaikum Musulmi wajibin da yake a kansu shi ne su taimaka, kowa daidai gwargwadon sa, wajen yakar wannan kungiya da ceto ‘yan uwa wadanda aka jarraba da fadawa cikin halakarta. Malamai da almajirai da masu hannu da shuni dole kowa ya bayar da tasa gudummuwar saboda yaduwar Shi’a musifa ce wacce ta shafi dukkan al’umma baki daya.
A karshe ina rokon Allah Madaukakin da ya amfani mutane da wannan bugu na uku kamar yadda ya amfanar da wadanda suka gabace shi. Ubangiji ya sa ayyukanmu duka su zama tsarkaka don zatinsa. Allah ya azurta mu da shiriya da istikama. Allah ya cika mana ladanmu, ya nauyaya mizaninmu.
Kaduna U.M. Labdo
Yuni, 2010
8
9
10
Babi Na Xaya
Tarihin Shi’a da Rabe-Rabensu
Shi’a a matsayinta na xaya daga cikin qungiyoyin bidi’a vatattu, tana da tarihi mai tsawo. A wannan babi, za mu duba wannan tarihin tun daga vullar qungiyar da rawar da Yahudawa suka taka wajen kafuwar ta, matakan yaxuwarta da kuma ressan da suka fita daga qungiyar. Amma bari mu fara daga farko.
Sunan Qungiyar
11
Al’ada ta gudana da kiran wannan qungiya da sunan Shi’a kuma a kira mabiyanta ‘yan Shi’a, koda yake akwai kuskure a cikin wannan ambato. Dalili shi ne, sunan Shi’a ya na nufin masu qaunar Sayyidina Ali binu Abi Xalib da goyon bayansa da mara masa da jivintar sa. Wannan suna a tarihance ya haxa qungiyoyi guda uku mabambanta. Waxannan su ne:
Ta Xaya: Galiya ko Gulat. Waxannan su ne qungiyar da suka wuce gona da iri wajen son Ali da jivintarsa. Bayan sun fifita shi a kan Sahabbai duka kuma sun yi da’awar annabta gareshi. Suka ce wai Jibrilu kuskure ya yi da ya kawo wahayi ga Annabi Muhammad (SAW); Ali ya kamata ya kawowa. Waxannan babu mai shakkar kafircinsu.
Ta Biyu: Zaidiya, watau mabiyan Zaidu binu Ali. Su suna fifita Ali binu Abi Xalib a kan dukkan Sahabbai, amma kuma suna jivintar sauran Sahabban kuma suna son su. Suna girmama Abubakar da Umar matuqa, suna ba su haqqinsu a matsayinsu na manyan Sahabbai kuma sun yarda da shugabancinsu amma suna ganin cewa da Ali aka gabatar a kansu wajen shugabanci da ya fi dacewa.
12
Ta Uku: Rafilawa. Waxannan suna da’awar cewa Annabi (SAW) ya yi wasiya a fili cewa Ali ya zama halifa a bayan sa amma, a cewarsu, sai Sahabbai suka sava wannan wasiya, suka naxa Abubakar a bayan Annabi. Saboda wannan, su Rafilawa suna barranta daga dukkan Sahabbai waxanda a ganinsu sun ci amanar Annabi, sun sava umarninsa, saboda haka sun yi ridda. A ra’ayin Rafilawa, dukkanin Sahabban Annabi, waxanda ake lasafta su da dubunnai, sun yi ridda bayan Annabi (SAW) sai mutum bakwai kawai.
To wannan kashi na uku su ne yawancin Shi’a da muke da su a duniya a yau. Ashe ka ga kure ne a ba su sunan Shi’a saboda wannan suna yana game su da sauran kashi biyu na farko da aka ambata. Saboda haka abinda ya fi kyau a riqa kiran su da sunansu Rafilawa. Idan kuma an ce Shi’a, to ya kamata a game sai a ce Shi’a Rafilawa.
Vullar Shi’a
Mutum na farko da aka sani ya yi kira zuwa ga aqidojin Rafilawa shi ne Abdullahi binu Saba’i wanda
13
yake bayahude ne ya musulunta a zamanin Sarkin Musulmi Usman binu Affan (R.A). Sai dai ga alama, wannan bayahude na qasar Yaman ya shiga Musulunci ne don munafinci domin da shigarsa ya riqa kewayawa biranen Musulmi da garuruwansu domin haddasa fitina. Kuma miyagun aqidoji da ya yaxa su suka kai ga tasowar fitina ta farko a tarihin Musulunci.
Imam Xabari ya ruwaito a cikin littafinsa, ya ce, ‚Abdullahi binu Saba’i ya kasance bayahude ne daga mutanen garin San’a kuma uwarsa baqa ce. Ya musulunta a zamanin Usmanu sa’annan ya riqa yawo a qasashen Musulmi yana qoqarin vatar da su. Ya fara da qasar Hijaz, sa’an nan Basra, sa’an nan Kufa, sa’an nan Sham, amma bai samu biyan buqatarsa ba a wajen mutanen waxan nan qasashe. Sai aka fitar da shi har ya tafi qasar Masar ya zauna a cikinsu. Ya riqa faxi daga cikin abubuwan da yake koyarwa, ‚Abin mamaki ga wanda yake riya cewa Annabi Isa zai dawo amma yana qaryata cewa Annabi Muhammadu zai dawo alhali kuwa Allah yana cewa: ‚Lalle ne wanda ya farlanta Alqur’ani a kanka, haqiqa, mai mayar da kai ne zuwa makoma.‛ To Muhammadu ai shi ya fi cancanta da komowa daga
14
Isa.‛ Sai mutane suka amsa masa wannan. Shi ke nan sai ya kafa musu aqidar Raja’a, watau komowa, sai suka yi ta yaxa ta. Sa’an nan bayan nan sai ya ce musu, ‚A da an yi annabawa dubu kuma ko wane annabi yana da mai wasici. Kuma Ali shi ne mai wasicin Annabi.‛ Sa’an nan bayan nan ya ce, ‚Muhammad cikamakin annabawa ne, kuma Ali cikamakin masu wasici.‛
‚Sa’an nan daga baya sai ya ce musu, ‚Babu azzalumin da ya fi wanda ya qi zartar da wasiyar Annabi kuma ya qwace lamarin al’umma daga hannun mai wasicin Manzon Allah (SAW).‛ Sa’an nan ya ce, ‚Usman ya karvi halifa ba da haqqi ba, kuma ga xan wasicin Manzon Allah yana kallo. Sai ku tashi ku taimake shi….‛ Da haka wannan fitina ta kankama, suka riqa yaxa ta cikin qasashe.‛ (Tarihin Xabari, 4/340).
Wannan shi ne farkon vullar Shi’a kuma shi ne tushen fitina wacce wutarta ta riqa ruruwa a hankali har ta kai ga faruwar munanan abubuwa, na farkonsu kisan Sarkin Musulmi Usmanu da yaqoqan da suka biyo baya tsakanin Musulmi.
15
Ibnu Taimiya ya ba da tushen Shi’a a taqaice inda ya ce, ‚Malamai sun ambata cewa, tushen Rafilanci ya kasance daga Abdullahi binu Saba’i zindiqi. Shi ya bayyana Musulunci ne ya voye Yahudanci kuma ya nemi ya vata Musulunci kamar yadda Bulus (Paul) na Kirista wanda shima bayahude ne ya vata addinin Nasara.‛ (Alfatawa, 28/483).
Alaqar Abdullahi binu Saba’i bayahude da vullar Rafilanci da aqidojinsa abu ne wanda ko su yan Shi’a ba sa musun sa. Manyan malamansu kamar Ash’ari Alqummi, Alkashi, Alnobakhti da Almamiqani duka sun tabbatar da wannan a cikin littafansu. Duka sun ruwaito cewa, ‚Malamai daga cikin mabiyan Ali (AS) sun hakaito cewa Abdullahi binu Saba’i ya kasance bayahude ne sai ya musulunta, ya bi Ali, ya jivince shi. Ya kasance a lokacin da yake kan Yahudanci yana qudure wasicin Annabi Musa ga Yusha’u binu Matta. A lokacin da ya musulunta bayan rasuwar Annabi (SAW) sai ya qudure wannan aqida dangane da Ali. Shi ne farkon wanda ya fara bayyana aqidar wajabcin imamar Ali kuma ya bayyana barranta daga abokan gabansa. To ta nan ne waxanda suka savawa Shi’a suke cewa tushen
16
Shi’anci an same shi ne daga Yahudanci.‛ (Duba Almaqalat na Alqummi, 61; Rijal na Kashi, 71; Firaqul Shi’a na Nobakhti, 22 da Tanqihul Maqali na Almamiqani, 2/184). Wannan magana daga manyan shaihinnan Rafilawa guda huxu tana tabbar da cewa ko su basu da ja dangane da rawar da yahundawa suka taka wajen kafa qungiyarsu da sanya aqidojinta.
Idan muka lura da kyau za mu ga cewa an saka qwan Rafilanci kuma an qyanqyashe a tsakanin abubuwa guda biyu miyagu. Waxannan abubuwa su ne munafunci da jahilci. Dangane da munafinci wannan a fili yake, domin Zindiqi Binu Saba’i shi ne farkon wanda ya fara bayyana aqidar wajabcin Imamar Ali kuma ya barranta daga abokan gabarsa, kamar yadda malaman Shi’a su da kansu suka shaida. Abokan gabarsa a nan suna nufin dukkan Sahabbai baki xaya in banda bakwai, kamar yadda za mu gani a nan gaba in Allah ya so. Amma dangane da jahilci idan muka koma ga maganar Imam Xabari inda ya bayyana cewa Binu Saba’i ya yawata qasashen Hijaz da Basra da Kufa da nufin vatar da mutane amma bai ci nasara ba sai da ya je qasar Masar. Dalilin wannan shi ne waxannan qasashe uku na farko
17
suna cike da Sahabbai da almajiransu Tabi’ai don haka Binu Saba’i bai samu dammar yaxa miyagun aqidojinsa a cikinsu ba. Amma qasar Masar a wancan lokaci akwai qarancin Sahabbai a cikinta kuma ba ta daxe ainun da shiga Musulunci ba; wannan ya sa aka samu jahilci wanda ya zama gurbi da Binu Saba’i ya saka qwansa. Waxannan miyagun abubuwa guda biyu, munafinci da jahilci, su ne qashin bayan Rafilanci kuma su ne sifofi guda biyu waxanda ‘yan Shi’a ba su tava rabuwa da su ba a tsawon tarihinsu.
Bayan rasuwar Sarkin Musulmi Usmanu da hawan Ali binu Abi Xalib matsayin halifa, nashaxin Binu Saba’i ya qaru inda a yanzu ya tare a hedkwatar daular Musulmi a wannan zamani, watau Kufa, ya fake a qarqashin fitinu da suka wanzu sakamakon yaqoqa tsakanin Musulmi a junansu, ya yi ta yaxa miyagun aqidojinsa. Mabiyansa sun qara yawa kuma sun qara nutsawa cikin vata. A wannan yayi, Rafilawa sun kasu gida uku gwargwadon nutsawarsu cikin vata da nesantarsu ga hukunce – hukuncen Musulunci da koyarwarsa. Akwai Gulatu, waxanda suka wuce gona da iri har suka ce Ali Allah ne. Waxannan Sarkin
18
Musulmi Ali binu Abi Xalib ya qone su da wuta bayan ya ba su kwana uku su tuba amma suka qiya. Akwai kuma Sabbaba, watau masu zagin Sahabbai, musamman Abubakar da Umar (RA). Waxannan Halifa Ali ya nemi kashe su sai yawancinsu suka gudu. Na uku su ne Mufaddila waxanda ba su yi zurfi ba ainun, ba su allanta Ali ba kuma ba sa zagin sauran Sahabbai amma sun yi imani cewa Sarkin Musulmi Ali ya fi Sahabbai duka, har da Abubakar da Umar. Irin waxannan, Ali ya yi musu hukuncin mai qazafi, ya ce, ‚Ba’a zuwa mun da wani wanda yake fifita ni a kan Abubakar da Umar face na yi masa bulala haddin mai qazafi.‛ (Duba Fatawa, 35/184 – 185).
To haka dai Shi’anci ya vulla a duniyar Musulunci kuma itaciyarsa ta tsira, itaciyar Yahudanci wacce aka yi mata ban ruwa da munafinci kuma aka sa mata takin jahilci. Abu guda da ya wajaba a lura da shi a nan shi ne koda yake wannan bidi’a ta vulla a zamanin Sahabbai, amma babu xaya daga cikinsu wanda ya shige ta. Babu shakka an samu wasu Sahabbai waxanda suka fifita Ali a kan Usman, amma babu Sahabi guda wanda ya fifita Ali a kan Abubakar da Umar. Sahabban Annabi
19
dukkaninsu sun haxu a kan fifita Abubakar da Umar a kan Ali, amma sun yi savani dangane da wane ne gaba tsakanin Usman da Ali. Mafi yawan Sahabbai sun fifita Usman; ‘yan kaxan ne suka fifita Ali a kan Usman. Haka nan kuma babu sahabin da yake zagin Sahabbai ‘yan uwansa, ko yake musu qazafi ko yake qin su; kai ko a cikin Tabi’ai babu mai yin haka sai munafiki mara addini ko jahili sabon shiga Musulunci.
Yaxuwar Shi’anci
Qunkiyar Rafilawa ta taka matakai huxu kafin ta zama qungiya mai ‘yanci wacce ta sha bamban da sauran qungiyoyi a wajen sunanta da aqidojinta da ra’ayoyinta. Waxan nan matakai su ne:
Mataki na xaya shi ne zamanin da Abdullahi binu Saba’i bayahude ya yi kira a voye zuwa ga aqidoji da ra’ayoyi waxanda suka zama harsashe wanda aka xora ginin Rafilanci a kai. Waxan nan aqidoji sun haxa da aqidar komowa da ya ce wai Ali binu Abi Xalib zai komo duniya bayan mutuwarsa; da aqidar wasici wanda ya ce wai Manzon Allah (SAW) ya yi wasiya da a naxa
20
Ali shugabancin Musulmi bayan rasuwarsa, amma sai Sahabbai suka qi zartar da wannan wasiya suka naxa Abubakar maimakon Ali. Haka nan da aqidarsa dangane da Sahabbai wacce ta fara da sukan su da sifanta su da ha’inci da zalunci saboda qin zartar da wasiyar Annabi (SAW) a riyawarsu; sa’an nan ta qasaita har ta kai ga la’antarsu da kafirta su xungurum.
Abubuwa biyu sun taimakawa Binu Saba’i samun nasarar yaxa miyagun aqidojinsa a wannan mataki. Na farko shi ne ya zavi wuri mai nisa (qasar Masar da iyakokin Sham da Iraqi) don yaxa manufofinsa. Waxan nan wurare sun yi nisa da cibiyar daular Musulunci, Madina, kuma akwai qarancin Sahabbai a wuraren idan aka gwada su da sauran vangarorin daular. Wannan ya ba shi dama ya ci karensa ba babbaka. Na biyu shi ne Binu Saba’i ya yaxa da’awarsa da farko a cikin sirri ta yadda ba ya gabatar da wannan da’awar sai ga mutanen da ya gamsu da gafalarsu da qarancin ilminsu, ko kuma mutanen da ya san suna da qiyayya a cikin zukatansu dangane da Musulunci, kamar Farisawa waxanda suke gaba da Musulmi Larabawa saboda rusa daularsu ta Majusanci da Sahabbai suka yi.
21
Mataki na biyu shi ne zamanin da waxanan aqidoji suka fara fitowa fili. Wannan ya faru bayan kashe Sarkin Musulmi Usman binu Affan (RA) da shagalar Sahabbai wajen qoqarin kashe wutar fitina wacce ta biyo bayan kashe shi xin. Wannan hali na rashin kwanciyar hankali ya baiwa Binu Saba’i da magoya bayansa damar ninka nashaxi wajen yaxa aqidojinsu a tsakanin jama’a.
To sai dai duk da haka, har yanzu qungiyar ba ta kankama ba domin shugabanninta ba sa daga cikin manyan mutane masu faxa a ji kuma yawan mabiyanta bai kai ya sa qungiyar ta samu wani tasiri na kuzo ku gani ba.
Mataki na uku shi ne zamanin da Rafilawa, a karo na farko, suka taru a qarqashin jagoranci guda, suka haxa qarfinsu wuri xaya. Wannan ya faru bayan kashe Hussain binu Ali binu Abi Xalib, jikan Manzon Allah (SAW) kuma shugaban samarin aljanna. Imam Xabari yana ba mu labari a cikin tarihinsa kamar haka, ‚Lokacin da aka kashe Hussain kuma ragowar rundunarsa suka dawo zuwa Kufa, sai ‘yan Shi’a suka zargi kansu, suka yi nadama (saboda su suka yi sanadin mutuwarsa). Daga
22
nan sai suka tattara a qarqashin shugabancin Sulaiman binu Surad Alkhuza’i wanda ya tara runduna mai kimanin dakaru dubu ishirin da nufin yaqar mutanen Sham (Halifar Banu Umayya da rundunarsa). A daidai wannan lokaci ne kuma Mukhtar binu Abi Ubaidin Althaqafi ya isa birnin Kufa ya ishe Rafilawa a qarqashin shugabancin Sulaiman binu Surad. Sai ya fara kira zuwa ga imamancin Muhammad binu Ali (Binul Hanafiya) kuma ya ba shi laqabin Mahadi. To daga nan sai Shi’a suka kasu biyu: qungiya guda a qarqashin shugabancin Sulaiman waxanda manufarsu ita ce xaukar fansar kisan Hussain da kuma qungiya guda a qanqashin Mukhtar waxanda manufarsu itace kira zuna ga imamar Muhammad binul Hanafiya. To wannan shi ne karo na farko da ‘yan Shi’a suka haxu wuri guda.‛ (Duba Tarihin Xabari, 5/551 – 552).
Bayan nan Sulaiman binu Surad ya tafi Sham da rundunarsa inda ya gwabza yaqi da mutanen qasar, yaqin da ya qare da mutuwarsa da watsa rundunarsa. Bayan da ragowar rundunar Sulaiman suka komo garin Kufa, sai suka haxe da rundunar Mukhtar Althaqafi wanda ya qarasa haxe kan Shi’a a qarqashin shugabancinsa.
23
Mataki na huxu shi ne zamanin da ‘yan Shi’a suka yiwa imaminsu, Zaid binu Ali, tawaye a shekara ta 121 bayan hijira. Zaid ya yi yaqi da Halifa Hisham binu Abdilmalik kuma dukkan ‘yan Shi’a sun goyi bayansa. To daga cikin rundunarsa sai wasu suka bayyana sukan Abubakar da Umar a fili. Zaid wanda yake shugaba ne mai ilmi da tsoron Allah, sai ya hana su wannan mummunan aiki. Daga nan sai suka qi shi, suka yi masa tawaye, suka ware daga rundunarsa. Waxanda suka ware sai aka sa musu laqabin Rafilawa, su kuwa waxanda suka rage a cikin rundunar Zaid binu Ali sai aka ba su laqabin Zaidawa.
Wannan shi ne mataki na qarshe a yaxuwa da kuma ci gaban tafarkin Shi’anci. Daga nan ne ‘yan Shi’a masu matsakaicin ra’ayi waxanda ba sa zagin Sahabbai kuma ba sa qudure miyagun aqidojin da Binu Saba’i ya koyar, suka ware daga ‘yan Shi’a masu zagin Sahabbai suna kafirta su waxanda aka kira Rafilawa. Wannan shi ya sa a baya muka yi magana a kan tantancewa wajen suna idan aka tashi kiran ‘yan Shi’a na wannan zamani namu. Muka ce ya fi kyau a kira su Rafilawa domin
24
suna qudure dukkan miyagun aqidojin da bayahude Abdullahi binu Saba’i ya koyar.
Qungiyoyin Rafilawa da Ressansu
A bayani da ya gabata a sama, mun raba Shi’a gida uku. Wannan rabo gwargwadon manyan rukunansu ke nan da suka bayyana a farkon vullarsu. Bayan wannan zamani, tsawon lokaci da rashin wani tushe guda da suka dogara a kansa wajen samo ra’ayoyinsu da koyarwarsu ya sa sun karkasu zuwa qungiyoyi masu yawa kuma su ma qungiyoyin suka karkasu zuwa rassa. Wannan rabe-rabe nasu ya wanzu ne, kamar yadda muka ambata, sakamakon rashin wani tushe guda wanda suka dogara da shi wajen tunaninsu. Domin Rafilawa ba su xauki Alqur’ani da Sunna a matsayin tushen addini ba. A taqaice ma dai, su a wurinsu wannan Alqur’anin da yake hannun Musulmi ba dai-dai yake ba; domin akwai qari da ragi da yawa a cikinsa. Dangane da Sunna kuma, ‘yan Shi’a suna da nasu hadisai da suka ruwaito daga imamansu goma sha biyu waxanda suke qudurewa cewa sun fi annabawa. Don haka ya zama mutanen ba su da
25
wani tushe guda takamaimai sai dai bin son zuciya. Wannan hali shi ya kawo rarrabuwarsu zuwa qungiyoyi guda biyar kuma ko wace qungiya ta kasu zuwa ressa masu yawa. A qasa za mu yi bayanin waxannan qungiyoyi da ressansu a taqaice.
1. Kaisaniya. Waxannan su ne mabiyan Kaisanu. Shi Kaisanu bawan Ali binu Abi Xalib ne da ya ‘yanta shi, a wata ruwayar kuma aka ce a’a bawan xansa ne Muhammad binul Hanafiya. Mabiyan wannan mutum sun nutsa ainun wajen girmama shi da xaukaka shi har suka wuce da shi matsayinsa, inda suka qudure cewa shi ya kewaye da dukkan ilmai na sarari da na voye kuma wai a wajen Sarkin Musulmi Ali da xansa Muhammad binul Hanafiya ya samu waxannan ilmai.
Babbar aqidar Kaisaniya ita ce faxinsu cewa ba kome ne addini ba sai biyayya ga mutum. Abinda suke nufi da wannan shi ne, dole ne kowa ya samu wani mutum da yake koyi da shi, yana xaukar umarninsa yana hanuwa da haninsa a addini. To su mutumin da suka xauka shi ne Kaisanu. Zurfin wannan aqida a zuciyarsu ya sa sun fassara rukunan Musulunci, watau Sallah, Zakka, Azumi da Hajji, da cewa duka mutane suke nufi.
26
Saboda haka, idan mutum ya yi dace da samun mutumin da ya kai matsayin a bi shi, to sai ya bar waxancan rukunai duka. Har yau daga cikin aqidojinsu akwai aqidar Tanasuhi da Hululu. Tanasuhi shi ne fitar ruhi daga wani ruhin kamar yadda za’a yi kofe na takarda daga wata takardar sai su zama abu biyu kuma abu xaya dai – dai wa daida. Watau mutumin da suke bi a matsayin addini idan ya rasu sai a yi kofen ruhinsa a sanya a cikin wani jiki sai ya dawo ya sake rayuwa a duniya. Hululu kuwa shi ne tashin ruhin mamaci zuwa ga wani mai rai da ci gaba da rayuwa a cikinsa. Banda waxannan aqidoji guda biyu, Kaisaniya suna qudure aqidar Raja’a, watau dawowar mamaci ya rayu a duniya da jikinsa da ruhinsa baki xaya.
Qungiyar Kaisaniya ta kasu zuwa rassa huxu kamar haka:
(a) Mukhtariya mabiyan Mukhtar binu Abi Ubaidin Althaqafi wanda muka gabatar da ambatonsa wajen magana a kan mataki na huxu na yaxuwar Shi’a. Daga cikin aqidojin da wannan reshe ya qudure akwai aqidar Bada wanda take nufin Allah yana canja
27
nufinsa bayan ya gano wani abu wanda a da bai san shi ba, wal iyazu billahi!
(b) Hashimiya mabiyan Abu Hashim binu Muhammad binul Hanafiya. Sun qudure cewa imama ta tashi daga kan ubansa bayan rasuwarsa ta komo kansa.
(c) Bayaniya mabiyan Bayan binu Sam’an Altamimi waxanda suka qudure cewa ya gaji imama daga Abu Hashim. Shi Bayan yana daga cikin ‘yan Shi’a gulatu waxanda suka yiwa Ali da’awar allantaka.
(d) Rizamiya, mabiyan Rizam binu Razm. Daga cikin aqidojinsu suna qudure cewa addini abu biyu ne kawai: sanin imani, da tsare amana. Wanda duk waxannan abubuwa suka tabbata gare shi, kome ya aikata kuma kome ya bari ba zai cuce shi da kome ba. Don haka suka bar ayyukan farilla kamar sallah da azumi da sauransu.
2. Alzaidiya, mabiyan Zaid binu Ali binu Hussain binu Ali binu Abi Xalib (RA). A ra’ayinsu, imama a cikin zuri’ar Faxima take, babu bambanci tsakanin
28
‘ya’yan Hassan da na Hussaini, ko wane yana iya xaukar imama. Kuma sun halasta a samu imamai biyu a lokaci guda kamar yadda suka halasta imamar wanda ya cancanta alhali akwai wanda ya fi shi cancanta. A kan wannan aqidar ne imam Zaid ya gina matsayinsa dangane da Abubakar da Umar da Usman. Ya ce Ali binu Abi Xalib ya kasance shi ne mafi cancantar Sahabbai da shugabancin Musulmi bayan rasuwar Annabi (SAW), to sai dai Sahabbai sun naxa Abubakar da waxanda suka biyo bayansa saboda maslaha da kaxe fitina da tabbatar da zaman lafiyar Musulmi. Ya ce kakansa Ali ya kashe mushirikai da yawa a yaqoqan da ya yi tare da Annabi kuma wannan ya sa ya yi maqiya da yawa ta yadda idan da an naxa shi imama bayan rasuwa Annabi da ba’a samu zaman lafiya ba. Don haka sai Sahabbai suka naxa wanda ya cancanta, Abubakar, duk da cewa ga wanda ya fi shi cancanta, watau Ali. Ta wannan hanya ne Zaid ya kaucewa zargin Sahabbai da cewa sun zalunci Ali ko kuma sun gaza zartar da wasiyar Annabi (SAW) kamar yadda sauran qungiyoyin Shi’a suka qudure kuma wannan ya jawo masa savani da wasu magoya bayansa waxanda suka varke daga
29
shugabancinsa kuma daga nan aka sa musu suna Rafilawa, kamar yadda muka gabatar da bayani a sama.
Ana iya lura a nan cewa, qungiyar Zaidiya, idan aka xauke ta a dunqule, tana da sassaucin ra’ayi ainun. Wannan kuwa ba da banza ba; domin shugabansu, imam Zaid, yana daga cikin mafiya yawan ilmi a cikin dukkan imaman Shi’a. Don haka ne galibin Ahalus Sunna suke xaukar koyarwarsa da ra’ayoyinsa na Fiqihu a matsayin mazhaba ta biyar, watau bayan mazhabobin Sunna guda huxu: Hanafiya, Malikiya, Shafi’iya da Hanbaliya.
Zaidiya tana da manyan rassa uku:
(a) Jarudiya, mabiyan Abul Jarud Ziyad binu Abi Ziyad. Suna qudure cewa Annabi (SAW) ya yi wasiya da naxa Ali a bayansa amma sifanta shi ya yi ba sunansa ya ambata ba. Suka ce Sahabbai ba su yi qoqarin gane mai wannan sifa ba sai kawai suka naxa Abubakar da son zuciyar su saboda haka suka kafirta. A nan ana iya gani a fili cewa Abul Jarud ya savawa imaminsa Zaid wanda bai da wannan mummunan quduri dangane da Sahabban Annabi.
30
(b) Sulaimaniya, shugabansu Sulaiman binu Jarir. Ya kasance yana cewa, imamar Musulunci tana tabbata da shura, watau zave, ba gado ko wasiya ba. Don haka ya tabbatar da shugabancin Abubakar da Umar, koda yake yana ganin Sahabbai sun yi kuskure wajen zaven su alhali ga Ali wanda shi ya fi cancanta. To amma wannan kuskuren bai kai ko matsayin fasiqanci ba balle kafirci, saboda kuskuren mai ijtihadi ne. Sai dai yana sukan Usmanu mummunan suka har ma yana kafirta shi a kan wasu abubuwa da suka faru a zamaninsa kamar yadda yake kafirta Aisha da Zubair da Xalha a dalilin yaqin da ya faru a tsakaninsu da Ali.
Wannan shi ma ya kaucewa sassaucin imam Zaid kuma ya vata vata mai nisa a yayin da ya kafirta waxanda Allah da Manzonsa suka shaida da imaninsu da xaukakar darajojinsu a aljanna.
© Salihiya da Batriya. Waxannan ressa ne guda biyu masu quduri da aqidu guda sai dai ko
31
wacce shugabanta dabam. Ta farko ana dangana ta ga Hassan binu Salih binu Hayyi ta biyu kuma ga Kuthair Al’abtar. Qudurinsu dangane da imama kamar qudurin Sulaimaniya ne, amma su ba su yanke hukunci a kan Usman ba. Suka ce su ba za su kafirta shi ba saboda sun samu ruwayoyi waxanda suke nuna cewa yana daga cikin Sahabbai goma waxanda Annabi (SAW) ya yi musu albishir da aljanna, amma kuma ba za su wanke shi ba saboda wasu ayyuka da suka ce ya aikata a zamaninsa waxanda a ganinsu sun sava tafarkin Abubakar da Umar.
Waxannan babu shakka suna da sassauci tunda har suna karvar ruwayoyin hadisi kuma suna izna da tafarkin Abubakar da Umar, watau siyasarsu da hanyarsu ta mulki. Sai dai ga alama qarancin sani ya sanya su cikin ruxi, inda suka dabarbarce, suka rasa ra’ayin xauka.
3. Al’imamiya. Wataqila wannan ita ce mafi girma a cikin qungiyoyin Rafilawa baki xaya. Babbar aqidarsu ita ce abinda suke qudurewa cewa imama, watau shugabancin al’umma bayan Annabi, ita ce mafi muhimmanci a cikin rukunan Musulunci, shikashikansa
32
da ayyukansa gaba xaya. A ganinsu, imama ta fi sallah, zakka, azumi, hajji, jihadi da sauransu. Wannan ya sa aka ba su sunan Imamiya.
Imamiya suka ce, saboda muhimmancin imama ba ta yiwuwa sam a ce Annabi (SAW) ya bar duniya ba tare da ya bayyanawa al’umma wanda zai xauki nauyin shugabancinta ba a bayansa. Suka ce kuma dole ne ya bayyana sunan wannan mutum a fili ta yadda kowa zai san shi kuma dole ya faxi a bainar jama’a ta yadda kowa zai ji don kada a samu savani a kan wannan muhimmin lamari mai haxarin gaske. Don haka suke qudure cewa lallai tabbas Annabi ya ambata a fili wanda zai zama imami a bayansa. Kuma wanda ya ambata shi ne Ali binu Abi Xalib. Kuma ko wane imami dole ne ya ayyana mai gadon sa kafin mutuwarsa.
Amma me ya sa Ali bai zama halifa ba bayan rasuwar Annabi? Imamiya suka ce zaluncin Sahabbai ya sa haka. Wannan ya kawo mu ga aqidarsu ta biyu, qudurinsu cewa Sahabbai azzalumai ne saboda sun hana Ali haqqinsa suka naxa Abubakar maimakonsa, kuma bayan Abubakar Umar da Usman. Haka nan sun qudurce kafircin Sahabbai baki xaya saboda, a cewarsu,
33
sun sava umurnin Annabi (SAW) wanda ya bayar a fili, qarara, ta hanyar da ba wanda zai iya cewa bai sani ba.
Imamiya sun jera imamai kamar haka: Ali sa’an nan Hassan xansa, sa’an nan Hussaini qanin Hassan, sa’a nan Ali binu Hussaini kuma daga nan gayyar ta waste saboda bayan Ali binu Hussaini, imami na huxu a lissafinsu, ba su qara haxuwa a kan wane ne imami ba. Wasu sun baiwa ‘ya’yan Hassan imama a yayin da wasu suka ci gaba da lasafta ta a cikin zuri’ar Hussaini kawai. Wasu ma sun ba da imama ga Muhammad binu Ali wanda aka fi sani da Binul Hanafiya wanda shi xan Ali ne amma ba daga wurin Faxima ba. Shi uwarsa sa-xaka ce; ita ce Hanafiya xin. Haka nan dai abin ya tafi; koda yaushe zamani ya qara nisa sai savaninsu ya qara yawa. Da sannu za mu ga misalan irin wannan savani nasu yayin da muka zo bayani a kan ressansu.
(a) Baqiriya da Ja’afariya mabiyan Muhammad Albaqir binu Ali bin Hussain (imami na biyar) da xansa Ja’afar Assadiq, imami na shida a jerin imaman Rafilawa. Waxan nan ressa biyu sun qudure imamar waxannan shugabanni tare da imamar ubansu Ali binu
34
Hussaini wanda akewa laqabi da Zainal Abidin. Kuma daga cikinsu akwai waxanda suka tsaya a kan waxannan imaman kawai; ba su ba da imama ga ‘ya’yansu ba, akwai kuma waxanda suka jawo imama har cikin zuri’arsu. Har yau, akwai waxanda suka tsayar da layin imama a kan Muhammad Albaqir, suka ce shi ne imami na qarshe kuma zai dawo bayan mutuwarsa.
(b) Nawusiya. Wannan reshe ana dangana shi ga wani mutum da ake kira Nawus; wasu malamai kuma suka ce, a’a ana dangana su ga wani gari ne mai suna Nawusa. Sun yi da’awar cewa su mabiyan Ja’afar Alsadiq, imami na shida, ne kuma wai shi wanzajje ne, ba zai mutu ba sai dai kurum ya faku ne kuma zai bayyana a qarshen zamani ya kashe maqiyan Shi’a. Kuma da yake waxan nan sun rayu a zamanin rayuwarsa, an ruwaito cewa shi Alsadiq da kansa ya la’ance su, ya barranta da su kuma ya qaryata dukkan abinda suke yaxawa dangane da shi.
35
(c) Afxahiya. Sun qudure cewa imama ta tashi daga Alsadiq zuwa babban xansa Abdullahi Al’afxah. Suka ce ubansa ya yi wasiya da ya gaje shi kuma ya nuna wasu alamu waxanda suka dace da shi. Tare da wannan duka, Abdullahi Al’afxah ya rayu kwana saba’in ne kawai bayan uban kuma ya rasu bai bar xa ba.
(d) Ithna Ashariya ko kuma Shi’a ‘yan dozin. Ana kiran su haka saboda aqidarsu ta cewa imamai goma sha biyu ne, na qarshensu ya faku a birnin Samarra, a Iraqi, yana nan ana ba shi ruwa da zuma, ba zai mutu ba sai ya bayyana a qarshen zamani don ya kafa daular Rafilawa kuma ya kashe maqiyan Shi’a. Wannan shi suke cewa Mahadi, a nasu tsarin.
Jerin imamai goma sha biyu a ra’ayin Shi’a ‘yan dozin shi ne, Ali, Hassan, Hussaini, Ali binu Hussaini, Muhammad binu Ali Albaqir, Ja’afar binu Muhammad Alsadiq, Musa Alkazim, Ali Alrida, Muhammad Altaqi Aljawad, Ali binu Muhammad Alnaqi, Hassan Al’askariAlzaki
36
da na qarshensu Muhammad Alqa’im wanda suke yiwa laqabi da Mahadi Almuntazar.
Wannan na qarshen fa a kansa ne dukkan tatsuniyoyin Rafilawa aka gina su. Shi ne zai bayyana a qarshen zamani kuma Allah ya tasar masa da manya – manyan ‘yan Shi’a waxanda suka mutu tun xaruruwan shekaru domin su taimake shi kuma a tasar masa manya – manyan maqiyan Rafilawa domin ya kashe su. Daga cikin waxanda za’a tasar masa da su domin ya kashe su ya more har da Abubakar da Umar (RA). Idan ya bayyana, zai rushe Makka, ya rushe xakin Ka’aba, sa’an nan ya wuce zuwa Madina ya rusa ta kuma ya rusa Masallacin Annabi (SAW) amma kafin ya yi haka sai ya fitar da Abubakar da Umar daga cikin qaburburansu ya kashe su. Da sauran irin waxan nan almarori da abubuwan ban mamaki na shifcin gizo kamar yadda za mu gani a nan gaba, in Allah ya yarda.
Bayan waxanda muka ambata a sama, Imamiya tana da wasu ressa kuma, kamar Shumaidiya, Isma’iliya Waqifa, Musawiya da Mufaddila.
4. Algaliya, ko kuma Gulat. Waxan nan su ne suka wuce makaxi da rawa dangane da kambama imamansu
37
har suka ba su matsayin allantaka. Sun xauko aqidoji daga gyauron addinai da suka gabata kamar Yahudanci, Nasaranci, Hindanci da Barhamanci. Haka nan kuma sun aro ra’ayoyi daga tsoffin falsafofi na mushirikai da maguzawan farko. Miyagun aqidojin waxan nan Rafilawa sun taqaita cikin abubuwa huxu: Tashbihi, watau kamanta Mahalicci da halittarsa; Bada, danganta jahilci ga Ubangiji; Raja’a, komowar mutane bayan sun mutu; da Tanasuhi watau nason ruhin mamaci zuwa ga mai rai. Wannan qungiya suna daga cikin mafi nutsawa cikin vata da nisa da haqiqanin Musulunci kuma suna da rassa da dama.
(a) Alba’iya mabiyan Alba’u binu Zura Aldausi. Da farkon lamarinsu, sun fifita Ali a kan Annabi sa’an nan daga bisani suka allanta shi.
(b) Almugiriya. Shugabansu Mugira binu Sa’id Al’ajali. Ya yi da’awar son imamai da goyon bayansu kuma ya ce ya samu wani sirri daga garesu wanda ya ba shi qarfin ruhi da zurfin basira. Daga bisani ya yi da’awar annabta kuma ya halasta abubuwan da Shari’a ta haramta. Wannan ya sa jahilai da munafukai
38
suka bi shi suka yi ta yaxa varna a bayan qasa.
(c) Alkamiliya, mabiyan Abu Kamil. Sun qudure kafircin Sahabbai baki xayansu saboda wai sun hana Ali haqqinsa na imama kuma suka yi suka ga Alin shi da kansa saboda wai suka ce bai yi qoqari wajen neman haqqin nasa ba.
(d) Almansuriya, mabiyan Abu Mansur Ujali. Da farko Ujali ya danganta kansa da Abu Ja’afar, imami na shida, ya ce shi almajirinsa ne mai gadon sirrinsa. A lokacin da imamin ya barranta daga gareshi sai ya yi da’awar imama ga kansa kuma daga bisani ya yi da’awar annabta da manzanci. Ujali ya halasta wa mabiyansa duk abinda Shari’a ta haramta. Wannan ya sa jahilai suka bi shi, suka yi ta yaxa varna a bayan qasa.
Banda waxan nan ressa da muka ambata, qungiyar Rafilawa Gulat suna da wasu ressan masu yawa kamar su Yunisiya, Nusairiya da Kaiyaliya, waxan da ba mu rattaba su ba domin gudun tsawaitawa.
39
5. Al’isma’iliya. Su kuwa babbar qungiya ce ta Rafilawa waxanda suka karkata wajen tunaninsu da ra’ayoyinsu zuwa ga falsafar al’umman farko. Su a wurinsu, imamai guda bakwai ne, ba sha biyu ba. Sun zavi wannan adadi ne domin ya dace da aqidarsu ta falsafa inda suka danganta abin da ilmin Hisabi da Falaki. Suka ce imamai bakwai ne kamar adadin ranaku bakwai na mako, da sammai bakwai da manyan taurari bakwai.
Suna qudure cewa ba ta yiwuwa ya zam babu imami a bayan qasa; idan ba’a samu imami na zahiri ba to dole a samu imami na voye. Daga nan ne suka samu laqabinsu na Baxinawa. Wannan aqida tasu ta rinjayi sauran aqidojinsu kuma ta yi ta’asiri a kansu fiye da ko wacce a yayin da suka rikixe zuwa qungiyar asiri wacce take xaukar salo daban – dabam da manufofi daban – dabam gwargwadon zamani da kuma yanayi da suka samu kansu. Wannan kuma ya mai da su xaya daga cikin mafi haxarin qungiyoyi a kan Musulmi.
Isma’iliya Baxinawa sun vulla a zamani daban – dabam qarqashin sunaye daban – dabam da manufofi daban – dabam. Amma a koda yaushe suna zama fitina
40
da mugun alkaba’i ga Musulmi. Misali, a zamanin fitinu da tashin tashina, suna vulla a matsayin qungiyar ta’adda masu kashe – kashe da sace – sacen mutane da yankan tafarki, watau fashi da makami.
A lokacin yaqi kuma tsakanin Musulmi da wasunsu suna vulla koda yaushe a sahun abokan gaba inda suke zama ‘yan gari waxanda da su a kan ci gari. A wannan zamani da muke ciki na raunin Musulmi da nashaxin mulkin mallaka da ‘yan mishan, qungiyar Baxinawa sun zama makami a hannun maqiyan Musulunci wanda suke amfani da shi wajen juye kan Musulmi da raba su da addininsu. Ga misali, a qasashen Gabashin Afrika, wannan qungiya ta bayyana da sunan Aga Khan inda suka gina makarantu manya da qanana, da asibitoci waxanda suke amfani da su domin jawo hankalin Musulmi zuwa ga tafarkinsu. A yau, cibiyar wannan qungiya tana birnin London a qasar Buritaniya. (Domin bayani dangane da qungiyoyin Rafilawa da ressansu, sai a duba Almilal wal Nihal na Shahrastani, shafi na 146 – 198).
41
42
Babi Na Biyu
Aqidojin Shi’a
A babin da ya gabata, mun ga vullar Shi’a da yaxuwarta, qungiyoyinta da ressansu kuma a wajen bijiro da qungiyoyin mun gamu da wasu daga cikin aqidojinsu waxanda suka kevanta da wasu qungiyoyi ko ressa. A wannan babi kuma, za mu mai da hankali ne a kan manya – manyan aqidojinsu waxanda suka haxu a kansu waxanda kuma da su ne suka bambanta da sauran qungiyoyin Musulmi. Za mu dogara kacokan a kan littafan Rafilawa wajen rubuta wannan babi domin ya zama mun yi musu adalci gwargwadon hali. Don haka kome muka faxi dangane da aqidojinsu zai zama kamar ya fito daga bakinsu ne kai tsaye.
43
Aqidar Bada
Bada a harshen Larabci yana da ma’ana guda biyu: bayyana bayan vuya da kuma sauya ra’ayi. Abinda ake nufi da bayyana bayan vuya, watau abu ya bayyana ga mutum bayan a da yana voye a gare shi. Wannan yana nufi ke nan ya san abu bayan ya jahilce shi. A sakamakon wannan sabon sani, sai ya sauya ra’ayinsa wanda ya gina a kan jahilci.
Rafilawa suna danganta wannan ga Allah Maxaukaki, inda suke qudure cewa yana yiwuwa Allah ya qaddari wani abu sa’an nan daga baya ya sauya nufinsa saboda faruwar wani abu, ko wasu abubuwa, waxanda a da bai san da su ba. Wannan, babu tantama, danganta jahilci ne ga Allah mai girma da xaukaka.
Bada babbar aqida ce a wajen Rafilawa wacce manyan littafansu suka tabbatar da ita. Ya zo a cikin babban littafinsu da ake cewa Alkafi, wanda shi ne mafi ingancin littafi a wurinsu kamar Bukhari a wurin Ahalus Sunna, cewa: ‚Ba’a bautawa Allah da wani abu (mafi girma) ba kamar qudure Bada.‛ (Alkafi, 1/146).
44
A wata ruwayar, ‚Ba’a girmama Allah da wani abu (mafi girma) ba kamar qudure Bada.‛ (Alkafi, 1/146). Har yau a cikin littafin an ruwaito, ‚Da mutane sun san abinda ke cikin qudure Bada na lada, da ba su gaji da maimaita shi ba.‛ (Alkafi, 1/148).
Waxannan ruwayoyi guda uku suna nuna mana matsayin wannan aqida a wurin ‘yan Shi’a cewa tana daga cikin manyan aqidojinsu waxanda suke bautawa Allah da qudure su.
Kuma wannan ba wai aqidar wasu ‘yan tsiraru ba ce, ko kuma wasu masu tsaurin ra’ayi a cikin ‘yan Shi’a. A’a; wannan aqidar Rafilawa ce baki xayansu, wacce suka haxu a kanta. Wani babban malaminsu mai suna Muhammad binu Nu’uman Almufid yana faxi a cikin littafinsa, Awa’ilul Maqalat, ‚Kuma sun haxu (watau Rafilawa) a kan dangana lafazin Bada wajen sifanta Allah Maxaukaki.‛ (Awa’ilul Maqalat, 48 – 49).
Wataqila zai yi kyau a nan mu yi tambaya: Me ya sa malaman Shi’a suke qudure wannan aqida kuma suke koyar da ita ga mabiyansu? Ko kuma mu ce: Mene ne fa’idar wannan aqida ga Rafilawa? Bayanin wannan tambaya zai bayyana idan muka tuna cewa ‘yan
45
Shi’a suna da’awar cewa imamansu da magadan imamansu, watau malamai, suna sanin gaibu. Saboda haka suna yawan ba da labarin kaza da kaza zai faru a lokaci kaza. Idan abin ya faru kamar yadda suka faxi shi ke nan, idan kuwa bai faru ba sai su ce Allah ya sauya nufinsa. Ka ga ke nan ba za’a ce sun yi qarya ba.
Misali, malaman Shi’a a zamanin da ya gabata, sun sha iyakance lokacin da Mahadi zai bayyana, watau Muhadinsu na Rafilawa. Kuma idan lokacin ya yi sai a ga wayam, babu shi babu labarinsa. To a irin wannan lokaci sai malaman Shi’a su koma ga aqidar Bada domin a fita kunya. Irin haka ne wani babban malaminsu mai suna Muhammad binu Hassan Alxusi, ya yi a cikin littafinsa, Kitab Algaiba. Shi Alxusi ya rayu a zamanin da Rafilawa suke jiran Mahadinsu wanda littafan malamansu na farko suka ambata cewa a wannan lokacin ne zai bayyana. To da bai bayyana xin ba, sai ya rubuta wannan littafin yana cewa, ‚Yadda ya kamata a fahimci waxannan labarai (na bayyanar Mahadi) shi ne a ce, idan sun inganta to tana yiwuwa Allah ya ayyana wannan lokaci da aka ambata (don bayyanar Mahadi), amma lokacin da wasu abubuwa suka faru kuma maslaha ta
46
sauya sai wannan ya sa aka jinkintar da bayyanar tasa zuwa wani lokaci.‛ (Kitab Algaiba, 263). A nan abinda Alxusi yake faxi qeqe da qeqe shi ne, tana yiwuwa Allah ya qaddari bayyanar Mahadi a wannan zamani, amma da wasu abubuwa suka faru waxanda Allah bai san su ba a lokacin da ya yi waccan qaddara, to sai ya canja nufinsa, ya qaddara wani lokaci dabam, wal iyazu billahi!
Malam dubi yadda ake amfani da qarya don a taimaki qarya kuma a vatar da bayin Allah domin biyewa son zuciya. Allah ya tsarshe mu vata.
Aqidar Sauya Qur’ani
‘Yan Shi’a suna qudure cewa Alqur’ani mai girma wanda yake a hannun Musulmi a yau ba cikakke ba ne; domin, a ganinsu, Sahabbai da suka tattara Alqur’ani a zamanin Abubakar da Usman, Allah ya yarda da su, sun sauya abubuwa da dama a cikinsa ta hanyar yin qare – qare da rage – rage a ayoyinsa. Suke ce wannan Qur’ani da muke karanta wa a yau babu abinda yake cikinsa daga abinda aka saukar ga Annabi (SAW) sai kaxan. Kuma wai Sahabbai su ne suka sauya
47
littafin Allah ta hanyar xebe ayoyi masu yawa da aka saukar waxanda suke tona asirinsu da kuma ayoyi da suke nuna falalar Ali da zuri’arsa. Saboda haka a wurin Shi’a, ayoyi da yawa dake cikin Alqur’ani ba maganar Allah ba ce, wannan ya sa suke zavar abinda ya dace da son zuciyarsu a cikin Alqur’ani, saura kuwa su yi burus da shi.
Wani babban malaminsu mai suna Hashim binu Sulaiman Albahrani yana cewa a cikin wani littafi nasa da ya rubuta a kan tafsiri, ‚Ka sani cewa a haqiqanin gaskiya wacce babu kokwanto a cikinta gwargwadon ruwayoyi mutawatirai, wannan Alqur’ani da yake hannunmu sauye-sauye sun faru a cikinsa bayan rasuwar Manzon Allah (SAW) kuma waxanda suka tattara shi bayan Annabi sun xebe kalmomi da ayoyi masu yawa daga cikinsa.‛ (Alburhan fi Tafsiril Qur’an, 36).
A cikin Alkafi, littafin da ya fi ko wane inganci a wajen ‘yan Shi’a, an yi bayanin gwargwadon abinda aka xebe daga cikin Alqur’ani. Mai littafin, watau Kulaini, ya ce, ‚An ruwaito daga Abu Abdullahi cewa Alqur’anin da Jibrilu ya zo da shi ga Muhammad (SAW) aya dubu goma sha bakwai ne.‛ (Alkafi, 2/634). Wannan yana
48
nufi ke nan cewa Kur’anin da yake hannunmu xan ragowa ne kawai; domin kuwa gwargwadon wannan ruwaya waxanda suka tattara littafin a bayan rasuwar Annabi (SAW) sun xebe kimanin sulusi biyu na littafin. Za mu tabbatar da haka idan muka lura da cewa Alqur’anin da yake hannunmu wanda Musulmi suka sani a yau ayoyinsa dubu shida da xari biyu da talatin da shida ne kawai, kamar yadda malaman Sunna suka tabbatar. (Duba Tafsirin Ibnu Kathir, 1/7).
Ruwayoyin da suka tabbatar da wannan mugunyar aqida ta Shi’a a cikin littafansu waxanda suke izna da su suna da yawa ainun. Wani malaminsu mai suna Ni’imatullahi Aljaza’iri da ya qididdige ruwayoyin ya tabbatar da cewa sun fi dubu biyu (Duba Faslul Khixabi, 248). Kuma dukkan rassan Rafilawa sun haxu a kan ita wannan aqida, kamar yadda babban shaihinsu da suke kira Muhammad binu Nu’uman Almufid ya qarrara a cikin littafinsa, Awa’ilul Maqalat, 49.
Wani qasurgumin malamin Shi’a mai suna Hussain binu Muhammad Annuri Alxabarsi ya rubuta wani shirgegen littafi musamman don ya tabbatar da gaskiyar aqidar Rafilawa cewa Qur’ani akwai sauye –
49
sauye a cikinsa. Littafin wanda ya sa wa suna Faslul Khixab fi Ithbat Tahrif Kitab Rabbil Arbab, ma’ana: Yankakkiyar Magana a kan Tabbatar da sauya Littafin Mamallakin Mamallaka, ya qunshi dubunnan ruwayoyi daga imaman Shi’a waxanda Rafilawa ke qudure cewa sun fi annabawa da manzanni kuma sun san gaibu, domin tabbatar da cewa an yi sauye – sauye a cikin Alqur’ani kuma waxanda suka zartar da waxannan sauye – sauye su ne manyan Sahabbai waxanda suka haxa da Abubakar da Umar da Usman, Allah ya yarda da su baki xaya. A cikin littafin har ila yau, an tabbatar da cewa malaman Shi’a kaf, magabatansu da na bayansu, sun haxu a kan wannan aqida (Faslul Khixab, 34), kamar yadda muka ruwaito a baya daga Shaihinsu, Almufid.
Rafilawa suna da nasu Qur’ani dabam wanda suke kira Mushafu Faxima, watau Kundin Faxima. A ganinsu wannan kundi shi ne Qur’ani na gaskiya wanda imamansu suka gado shi daga Nana Faxima xiyar Manzon Allah (SAW) da mijinta Ali binu Abi Xalib, Allah ya yarda da su. Muhammad binu Hassan Alsaffar wanda ake lasaffa shi daga cikin manyan malaman Shi’a magabata (ya rasu a shekara ta 290 B.H.) ya ruwaito a
50
cikin littafinsa, Basairud Darajat, daga Imam Abu Ja’afar ya ce, ‚Babu wani da zai iya da’awar cewa ya tattare Alqur’ani dukkaninsa, zahirinsa da baxininsa, sai masu wasici,‛ watau imamai. Har yau, a cikin littafin ya ruwaito gare shi yana cewa, ‚Babu wani daga mutane wanda zai ce ya tattare Alqur’ani dukkaninsa, kamar yadda Allah ya saukar da shi, sai maqaryaci. Ba wanda ya tattare shi, ya haddace shi kamar yadda aka saukar da shi sai Ali binu Abi Xalib da imamai a bayansa.‛ (Basa’irud Darajati, 213).
Qur’anin ‘yan Shi’a ya sha bamban da Alqur’anin Musulmi ta fuskoki da dama. Mun riga mun gabatar da bayanin bambancinsu ta wajen jimillar ayoyinsu inda Qur’anin Rafilawa yake da adadin ayoyi dubu goma sha bakwai (17,000) dai dai a yayinda namu yake da ayoyi dubu shida da xari biyu da talatin da shida (6,236) kawai. Ta fuskar tsawon surori ma littafan biyu sun sha bamban. Ga misali, ya zo a cikin Kitab Sulaim binu Qais, mashahurin littafin nan na Shi’a wanda saboda ingancinsa a wajensu suke masa laqabi da A.B.C. Din Shi’a, cewa suratul Ahazab wacce take da ayoyi 73 a Qur’aninmu, su a nasu Qur’anin adadin ayoyin Baqara
51
ne da ita, watau 286. Suratun Nur kuma, wacce take da ayoyi 64, su a wajensu ayoyi 160 ke gareta. Suratul Hujurati kuwa, wacce a cikin Qur’anin da muka sani ayoyinta 18 ne kacal, su a nasu Qur’anin ayoyinta 90 ne dai dai wa daida. (Duba Kitab Sulaim binu Qais, 122).
Ta fuskar adadin surori ma, akwai xan bambanci saboda akwai wasu surori waxanda ‘yan Shi’a suke jin an xebe su daga Alqur’aninmu. Misali shi ne suratul Wilaya wacce suka ce wai a cikinta Allah ya yi umarni da a naxa Ali binu Abi Xalib a matsayin Sarkin Musulmi bayan rasuwar Annabi (SAW). Wannan sura ba mu san ta ba, babu ita a cikin Alqur’aninmu, amma Rafilawa na qudure cewa Sahabbai ne suka xebe ta don cin amana, a faxinsu, domin su hana Ali haqqinsa na gadar Annabi, su naxa Abubakar a makwafinsa. Wannan ita ce aqidarsu.
Dangane da kalmomi da lafuzza da ma’anoni, babu wata sura a cikin Alqur’ani kamar yadda muka san shi face ‘yan Shi’a sun zo da savanin kalmomi ko ayoyi a cikinta. Za mu ba da ‘yan misalai kaxan. A Fatiha suna karanta: Ihdinas siraxal mustaqim. Siraxa man an’amta alaihim, gairil magdubi alaihim wa gairid dalin. A suratul Asri, suna karanta: Wal asr innal insana la fi
52
khusr. Wa innahu fihi ila akhirid dahr. Illal lazina amanu wa amilus salihat, wa’atamaru bit taqwa, wa’atamaru bis sabr. Suratul Fili kuma suna fara ta haka: Alam ya’atika kaifa fa’ala rabbuka bi ashabil fili.
Wannan xan misali ne kawai muka kawo domin mai karatu ya ganewa idanunsa. Wanda yake son ya ga waxannan sauye – sauye filla – filla, to sai ya koma ga littafin Alshi’atu wal Qur’an na Ihsan Ilahi Zahir, Allah ya yi masa rahama, domin shi ya tsamo waxan nan canje – canje waxanda suka shafi surorin Alqur’ani guda 114 duka daga littafan Rafilawa kuma ya jera su tsaf tare da ruwayoyinsu.
Wataqila mai karatu ya yi tambaya: Don me ‘yan Shi’a ba sa buga wannan tafkeken ‚Qur’ani‛ nasu, wanda ya ninka na Musulmi ninki uku, su sayar a kasuwa? Amsa ita ce, abinda yake hana su bayyana wannan littafi nasu shi ne taqiya, watau munafunci da yaudara (za mu yi magana a kan aqidar taqiya nan gaba a wannan littafi in Allah ya yarda). A haqiqa ‘yan Shi’a ba Qur’aninsu kaxai suke voyewa ba; aqidarsu ta taqiya tana umarnin su da su voye manyan littafan malamansu waxanda suka qunshi aqidojinsu da manufofinsu sai ga
53
manyan mabiyansu waxanda suka riga suka yi zurfi a tafarkinsu. Kaxan daga cikin littafansu suke sayarwa a kasuwa, sauran sai dai a manyan cibiyoyinsu da makarantunsu. Qur’aninsu kuwa, idan akwai shi cikakke, to babu shakka ba mai ganinsa sai manyan shaihunnansu, sai kuma almajirai amintattu.
Bayan mun gabatar da bayani a kan wannan aqida kamar yadda take a cikin littafan Rafilawa masu inganci a wurinsu, muna ganin babu wani Musulmi da yake buqatar wani qarin bayani dangane da abinda ta tattare na kafirci da jahilci da vata. Amma saboda yankan hujja ga masu kiran kansu Shi’a, za mu yi bayanin kafircin wannan aqida a taqaice.
Da farko dai aqidar ta qaryata Alqur’ani mai girma saboda a cikinsa Allah mai girma da xaukaka ya tabbatar da cewa ya tsare littafinsa ta yadda qari ko ragi ba za su shige shi ba. Ubangiji Maxaukaki ya ce, ‚Lalle mu ne, muka saukar da Ambato (Alqur’ani), kuma lalle mu, masu kiyayewa ne gare shi.‛ (Suratul Hijr: 9). A wata ayar kuma, ya tabbatar da cewa varna ba ta shiga wannan littafi ko ta halin qaqa: ‚Waxan nan da suka
54
kafirta game da Alqur’ani a lokacin da ya je musu, kuma lalle ne, haqiqa, littafi ne mabuwayi. Varna ba za ta je masa ba daga gaba gare shi, kuma ba za ta zo ba daga baya gare shi. Saukarwa ce daga Mai Hikima, Godadde.‛ (Suratu Fussilat: 41 – 42).
Na biyu wannan aqida har ila yau tana qaryata Alqur’ani ta wata fuskar dabam domin tana kafirta ko fasiqantar da waxanda Allah ya bayar da labari cewa ya yarda da su kuma ya yi musu gafara: su ne Sahabban Annabi. Aqidar ta kafirta Sahabbai ta hanyar dangana musu sauya Alqur’ani da voye abinda Allah ya saukar da yin qari da ragi a cikinsa. Allah yana faxi dangane da Sahabban Annabinsa: ‚Kuma magabata na farko daga Muhajirina da Ansar da waxanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare shi, kuma ya yi musu tattalin gidajen Aljanna: qoramu suna gudana a qarqashinsu, suna madauwama a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma.‛ (Suratut Tauba: 100).
Xan uwa mai karatu ka dubi abinda Allah ya ce dangane da Sahabban Annabinsa, har ma da waxanda suka bi su da kyautatawa, sa’an nan ka dubi abinda
55
Rafilawa suka jingina musu na sauya maganar Allah da cin amanar Manzonsa, za ka san cewa lalle ‘yan Shi’a sun yi nisa daga barin shiriya. Muna roqon Allah ya arzuta su da karvavven tuba, amin.
Aqidar Imama
Imama ita ce shugabanci a addini, imam kuma shi ne shugaba, jam’insa imamai. Idan Rafilawa suka yi amfani da wannan kalma, to su a wajensu tana da ma’ana ta musamman. Imama a wajensu ita ce shugabanci a addini amma ta hanyar gado. Zuri’ar Annabi ne, ta hanyar xiyarsa Faxima kawai banda sauran ‘ya’yansa, suke gado ta daga kakansu kuma tare da ita su gado wasu kevance – kevance na annabta. Kalmar imama wani lokaci suna ce mata wilaya, wani yayi kuma wasici ko wasiya. Ko wacce suka yi amfani da ita, abu guda suke nufi.
‘Yan Shi’a suna qudure cewa imama ita ce mafi girman rukunan addini, kuma ita ce tushen Musulunci da imani ta yadda imanin mutum ba ya inganta sai ya qudure ta, kuma ba’a karvar ayyukansa na ibada sai ya yi
56
riqo da ita. Kulaini ya ruwaito a cikin littafinsa daga Abu Ja’afar, imami na shida, ya ce, ‚An gina Musulunci a kan abubuwa guda biyar: sallah, da zakka da hajji da azumi da wilaya.‛ (Mai ruwaya) Zuraratu ya ce, sai na ce: wane ne a cikinsu yake da fifiko? Sai ya ce: Wilaya. (Duba Usulul Kafi, 2/18). A nan mai karatu zai iya lura cewa, daga cikin shika – shikan Musulunci guda biyar kamar yadda muka san su, an xebe guda an musanya shi da wani. Wanda aka xebe shi ne kalmar shahada wacce aka musanya ta da imama. Wannan yana nuna matsayin imama da muhimmancinta a tafarkin Shi’a.
Dangane da matsayin imama har yau, malamin Shi’a mai suna Hashim Albahrani yana cewa, ‚Wilaya, watau iqirari da annabcin Annabi (SAW) da imamar imamai da lazimtar sonsu da qin maqiyansu da masu sava musu, shi ne asalin imani tare da xayanta Allah mai girma da xaukaka kuma addini ba ya inganta sai da haka. Kai ita imama ita ce sababin samar da talikai da gina hukuncin takalifi da sharaxin karvar ayyuka.‛ (Alburhan fi Tafsiril Qur’an, 19). Wani malamin nasu da ake kira Muhammad Baqir Almajlisi yana cewa, ‚Babu
57
tantama cewa wilaya da quduri da imamar imamai (A.S) da biyayya gare su shi ne tushen addini kuma yana gaba da dukkan ayyukan ibada domin shi ne mabuxinsu.‛ (Mir’atul Uqul, 7/102).
Waxannan ruwayoyi daga imaman Shi’a da manyan malamansu suna nuna mana matsayin imama a tafarkin Shi’anci cewa ita ce tushen addini da asalin imani kuma duk wanda bai ba da gaskiya da imama ba to imaninsa bai inganta ba, watau a taqaice shi ba Musulmi ba ne.
Rafilawa suna qudure cewa imamai goma sha biyu ne, kuma da zavin Allah ne suka zama imamai, watau Allah ne ya zave su kamar yadda ya zavi annabawa da manzanni. Ya zo a cikin littafin Kashful Gumma na Ali binu Isa Al’arbali, xaya daga manyan malamansu, cewa Ali binu Abi Xalib (R.A) ya ruwaito Manzon Allah (SAW) yana cewa, ‚Imamai a bayana su goma sha biyu ne. Kai ne na farkonsu ya Ali kuma na qarshensu shi ne Mahadi wanda zai mulki gabas da yammancin duniya.‛ (Kashful Gumma, 2/507). Kuma an ruwaito daga Imam Abu Ja’afar ya ce, ‚Mu imamai goma sha biyu ne; Hassan da Hussain suna ciki, sa’an
58
nan ragowar imaman daga zuri’ar Hussaini.‛ (Duba littafin Alkhisal na Saduq, 428).
Waxan nan imaman su ne:
1. Ali binu Abi Xalib. Laqabinsa a wurin Shi’a Murtada. Idan suka ce Amirul Muminina ko Al’amir to shi suke nufi.
2. Hassan binu Ali. Laqabinsa Mujtaba.
3. Hussain binu Ali, qanin Hassan. Laqabinsa Shahid. Sauran imaman Shi’a guda tara duka daga zuri’arsa suka fito.
4. Ali binu Hussain. Laqabinsa Sajjad. Ahlus Sunna suna yi masa laqabi da Zainul Abidin.
5. Muhammad binu Ali. Laqabinsa Albaqir. Ana yi masa alkunya da Abu Ja’afar.
6. Ja’afar binu Muhammad. Laqabinsa Assadiq. Ana yi masa alkunya da Abu Abdullahi. Waxan nan imamai guda biyu, na biyar da na shida, gare su Shi’a suka danganta yawancin ruwayoyi waxanda a kansu suka gina aqidoji, ra’ayoyi da hukunce – hukuncen tafarkinsu na Rafilanci.
7. Musa binu Ja’afar. Laqabinsa Alkazim.
59
8. Ali binu Musa – Laqabinsa Alrida. Ana yi masa alkunya da Abul Hassan.
9. Muhammad binu Ali. Laqabinsa Altaqi. Shi ma suna yi masa laqabi da Abu Ja’afar.
10. Ali binu Muhammad. Laqabinsa Alnaqi. Mahaifinsa ya rasu yana da shekaru takwas a duniya. Don haka Rafilawa suka yi savani dangane da imamarsa. Amma daga baya an samu amincewar mafi yawansu a kan imamar tasa.
11. Hassan binu Ali. Laqabinsa Alzaki. Ana yi masa laqabi kuma har yau da Al’askari. Alkunyarsa kuma Abu Muhammad.
12. An yi savani dangane da imami na 12. Malamai da dama, ciki har da malaman Shi’a, sun ce imami na 11 bai bar xa namiji ba. (Duba Al’irshad na Muhammad binu Nu’uman Almufid, 339 – 340). A ra’ayin waxan nan malamai, Ja’afar binu Ali, qanin Hassan binu Ali, shi ne ya zama imami na 12.
Wasu malamai kuwa suka ce imami na 11 ya bar xa mai suna Muhammad kuma shi ne imami na 12. Suka
60
ce wannan imami ubansa ya rasu yana da shekaru biyu a duniya kuma yana xan shekara huxu ya shiga wani kogo ya vace kuma zai bayyana a qarshen zamani da sunan Mahadi mai ceton Shi’awa. Wannan yaron ne Rafilawan duniya suke jira tun kimanin shekara dubu da xari biyu har zuwa yau don ya zo ya cece su, ya kafa daular ‘yan Shi’a wacce za ta ga bayan Ahlus Sunna ta hanyar kashe su baki xaya kuma bayan ta gama da su ta taso mamatansu na farko suma ta kashe su.
Rafilawa suna qudure cewa imamar waxan nan imamai tana tabbata da nassi daga Allah mai girma da xaukaka, watau Allah ne ya naxa su da kansa kuma kai tsaye. Daga cikin irin hadisansu, sun ruwaito cewa, ‚An yi mi’iraji da Annabi (SAW) zuwa sama sau xari da ishirin kuma a ko wane karo Allah yana yi masa wasiya da imamar Ali da imamai da za su biyo bayansa fiye da yadda ya yi masa wasiya da ayyukan farilla.‛ (Basa’iruddarajati na Muhammad binu Hassan Alsaffar, 99).
‘Yan Shi’a suna tabbatarwa da imamansu sifofin allantaka. Daga cikin irin abubuwan da suke dangantawa Sarkin Musulmi Ali (R.A) akwai wannan ruwaya cewa
61
ya ce, ‚Ni ne idanun Allah; ni ne hannun Allah; ni ne haqarqarin Allah; ni ne qofar Allah.‛ A wata ruwayar kuma ya ce, ‚Ni ne ilmin Allah; ni ne zuciyar Allah mai kiyayewa; ni ne harshen Allah mai furuci; ni ne idanun Allah masu gani; ni ne haqarqarin Allah; ni ne hannun Allah.‛ (Basa’iruddarajati, 81). Danganta irin waxan nan ruwayoyi na qarya bai tsaya ga Ali ba kawai, har ga Annabi (SAW) suna dangantana. Sulaim binu Qais ya ruwaito cewa Manzon Allah (SAW) ya faxi ga Ali kamar haka, ‚Ya Ali, kai kana daga gare ni, ni ina daga gare ka. An gauraya namanka da namana da jininka da jinina…..Wanda ya yi musun wilayarka ya yi musun allantakar Allah. Ya Ali, kai ne tutar Allah mafi girma a bayan qasa bayana, kuma kai ne bango mai girma ranar Alqiyama. Wanda ya shiga inuwarka ya rabanta domin hisabin talikai duka yana hannunka kuma makomarsu na gare ka. Mizani naka ne; siraxi naka ne; taron Alqiyama naka ne; hisabi naka ne. Wanda ya fake da kai ya tsira kuma wanda ya sava maka ya halaka. Allah ka shaida, Allah ka shaida.‛ (Kitab Sulaim binu Qais, 244 – 245).
Rafilawa suna qudure cewa imamansu sun san gaibu, kuma suna da sanin abinda ya faru tun farkon halitta da
62
abinda zai faru har zuwa ranar Alqiyama. Kulaini ya ruwaito daga Abu Abdullahi ya ce, ‚Na rantse da Ubangijin Ka’aba; na rantse da Ubangijin wan nan gini (Ka’aba) - ya rantse sau uku - da na kasance tsakanin (Annabi) Musa da Haliru da na faxa musu cewa ni na fi su sani; da na ba su labarin abinda ba su sani ba domin Musa da Haliru (AS) an ba su sanin abinda ya kasance ne (kawai); ba’a ba su sanin abinda zai zo da abinda zai kasance ba har zuwa ranar Alqiyama. Mu kuwa (watau imamai) mun gaji wannan ilmin daga Manzon Allah (SAW) gado.‛ (Usulul Kafi; 1/261). Mashahurin malamin Shi’a mai suna Muhammad binu Muhammad binu Nu’uman Almufid yana faxi a cikin littafinsa: ‚Imamai daga zuri’ar (Annabi) Muhammad (SAW) sun kasance suna sanin abinda yake voye cikin zukatan wasu bayi kuma sun san abinda zai kasance kafin kasancewarsa.‛ (Awa’ilul Maqalat, 75).
Rafilawa suna wuce gona da iri wajen son imamansu da girmamasu da kambama su har su fifita su a kan annabawa da manzanni da mala’iku makusanta ga Ubangiji. Ya zo a cikin irin ruwayoyinsu da suke danganawa ga Annabi (SAW) cewa ya ce da Ali:
63
‚Lallai Allah mai girma da xaukaka ya fifita annabawansa manzanni a bisa mala’ikunsa makusanta kuma ya fifita ni a kan dukkanin annabawa da manzanni. Ya Ali, fifiko a bayana ya tabbata a gare ka da imamai masu zuwa bayanka.‛ (Duba Ilalush Shara’i’ na Saduq, 5). A cikin wani littafi nasu mai suna Haqqul Yaqin fi Usulid Din, mawallafin littafin, Abdullahi binu Shabbar, yana cewa, ‚Ya wajaba a yi imani da cewa Annabinmu da alayensa ma’asumai suna da fifiko a kan annabawa da manzanni da mala’iku makusanta saboda hujjoji masu yawan gaske da suka zo da haka.‛ (Duba Haqqul Yaqin, 1/209).
Wannan aqida ta fifita imamai a kan annabawa da manzanni, babban malamin Shi’a na wannan zamani, Imam Ayatullah Ruhullah Khumaini, ya tabbatar da ita inda yake cewa, ‚Kuma lallai imamai suna da matsayi abin godewa da daraja maxaukakiya da wakilci a kan samuwa wanda ko wacce qwayar zarra ta halitta duka take qarqashinsa. Kuma yana daga cikin abinda ya wajaba a qudure a cikin mazhabarmu cewa imamanmu suna da matsayi wanda mala’iku makusanta da annabawa
64
manzanni ba su isa gare shi.‛ (A duba Alhukumatul Islamiya na Khumaini, 52).
‘Yan Shi’a Rafilawa suna qudure cewa wahayi yana sauka ga imamansu. Sun ruwaito daga Abu Abdullahi ya ce, ‚Mu ana ba mu guzuri (na ilmi) dare da rana kuma ba don ana ba mu guzuri ba da abinda yake wajenmu (na ilmi) ya qare. (Mai ruwaya) Abu Basir ya ce: Allah ya sanya ni fansarka, waye yake zuwa muku? Ya ce: Daga cikinmu akwai wanda yake gani da ido quru-quru; daga cikinmu akwai wanda ake jefawa cikin zuciyarsa kaza-kaza; daga cikinmu akwai wanda yake ji da kunnensa amo kamar amon sarqa a cikin tasa. (Mai ruwaya) ya ce: Na ce: Allah ya sanya ni fansarka, waye yake zuwa muku da wannan? Ya ce: Wani halitta ne wanda ya fi Jibrilu da Mika’ilu girma.‛ (Biharul Anwar na Majlisi, 26/53). Ya zo a cikin littafin Basa’iruddarajat, an ruwaito daga Abu Abdullahi, ya ce, ‚Ruhu wani halitta ne wanda ya fi Jibrilu da Mika’ilu girma. Ya kasance tare da Annabi (SAW) yana daidaitar da shi, yana shiryar da shi. Kuma a bayan Annabi (SAW) yana tare da masu wasici.‛ (Duba shafi na 476).
65
Yana cikin aqidojin Shi’a dangane da imamansu cewa su imaman ma’asumai ne, watau Allah ya tsare su kuma ya kiyaye su daga aikata zunubai manya ko qanana kuma ba sa kuskure a cikin lamuran addini. Ba sa rafkanuwa, ba sa mantuwa, ba sa tuntuve, ba sa sha’afa. Malaminsu da suke wa laqabi da Almufid yana faxi a cikin littafinsa: ‚Lallai imamai waxanda suke tsaye matsayin annabawa wajen zartar da hukunce – hukunce da tsayar da haddodi da tsare shari’o’i da ladabtar da talikai ma’asumai ne kamar ismar annabawa kuma bai yiwuwa su yi rafkanuwa a cikin wani lamari na addini kuma ba sa mance wani abu na hukunce – hukunce.‛ (Awailul Maqalat, 71-72). Wani malamin nasu da ake kira Assaduq yana cewa, ‚Qudurinmu dangane da annabawa da manzanni da imamai shi ne cewa su ma’asumai ne, tsarkaka ne daga dukkan wani datti. Kuma cewa su ba sa aikata zunubi, ko qarami ko babba, kuma ba sa savawa Allah abinda ya umarce su kuma suna aikata abinda aka umarce su. Wanda ya kore musu isma dangane da wani abu na lamuransu to haqiqa ya jahilce su, kuma wanda ya jahilce su to shi kafiri ne.‛
66
(An ciro wannan daga Aqa’idul Ithnai Ashariyya na Ibrahim Almusawi Alzanjani, 2/157).
Wannan ita ce aqidar Rafilawa dangane da Imama wacce aka gina addinin Shi’a xungurum a kanta. Daga wurin waxan nan imamai ne, a riyawar ‘yan Shi’a, suka karvo shika-shikan addininsu, aqidojinsu, hukunce – hukuncensu da ibadojinsu. Idan mai karatu ya lura, zai ga cewa yawancin ruwayoyin Rafilawa da hadisansu ana dangana su ga waxan nan imamai ne. Nadiri ne za ka samu ruwayar ‘yan Shi’a an dangana ta ga Annabi (SAW) ko kuma wani Sahabi. A haqiqanin lamari, Rafilawa ba sa gwada maganar kowa da maganar imamai, koda maganar Alqur’ani ce saboda shi Alqur’ani suna da shakku dangane da ingancinsa. Kai ba ma shakku ba, ‘yan Shi’a na haqiqa sun yi imani cewa Alqur’ani an yi qari kuma an yi ragi a cikinsa, kamar yadda muka gani a baya.
Amma aqidar Ahlus Sunna dangane da waxan nan imamai, to su suna xaukar su a matsayin Musulmi na gari kuma manyan bayin Allah masu ximbin daraja saboda kusancinsu da Annabi (SAW). Kuma sun tabbatar cewa dukkan ruwayoyin da Rafilawa ke
67
danganta musu qarya ce tsagwaronta kuma su barrantattu ne daga irin waxannan ruwayoyi waxanda suka sava da Alqur’ani, Sunnar Annabi da hankali. Don haka suna daraja waxannan imamai kamar yadda suke girmama sauran Ahlul Baiti baki xaya. Waxanda suke Sahabbai ne daga cikinsu, kamar Ali da Hassan da Hussaini, suna ba su haqqinsu a matsayinsu na Sahabbai. Waxanda kuma suke Tabi’ai ne ko Tabi’an Tabi’ai, to suna ba su haqqinsu gwargwadon matsayinsu tare da qarin ban girma saboda kusancinsu da Annabi (SAW). Da sannu nan gaba a wannan littafi za mu zo da bayani na yadda waxannan imamai da sauran malaman Ahlul Baiti suka barranta daga ‘yan Shi’a da qarerayin da suka laqa musu.
Dangane da shugabancin al’umma, watau imama, ko kuma khilafa kamar yadda mu muke ce mata, Ahlus Sunna suna qudure cewa tana tabbata ga mutum ta hanyar zave da mubaya’a. Watau dukkan Musulmi namiji wanda ya sifantu da sifofin ilmi da taqawa da adala idan jama’a suka zave shi kuma suka ba shi bai’a sai ya zama imami ko khalifa. Don haka a lamarin babu gado kuma khalifa ba ya sanin gaibu sai dai yana yin aiki da Qur’ani da Sunna gwargwadon iyawarsa tare da
68
sauraron shawarar Musulmi ko kuma shura. A kan wannan qa’ida ne Musulmin farko suka zavi Abubakar ya shugabaci al’umma bayan Annabi (SAW) kuma daga bayansa suka zavi Umar, sa’an nan Usman, sa’an nan Ali, Allah ya yarda da su baki xaya.
Amma su Rafilawa suna ganin cewa Ali ne ya cancanci ya zama Khalifa bayan Annabi saboda shi jininsa ne kuma daga zuri’arsa ne ya kamata a yi ta samun khalifofi ko imamai ta hanyar gado. Don haka suka xauka cewa wai Sahabbai sun yi zalunci a lokacin da suka naxa Abubakar maimakon Ali. Kuma a kan haka suka gina aqidarsu ta gaba da Sahabban Annabi (SAW) da qudure kafircinsu da zaluncinsu da vatansu.
Aqidar Shi’a Dangane da Sahabbai
‘Yan Shi’a suna qudure gaba da qiyayya mai tsanani da jafa’i da nunqufurci da mugun alkaba’i ga Sahabban Annabi (SAW), Allah ya yarda da su baki xaya. Littafansu na da da na yanzu suna cike da mummunan suka da zagi da cin zarafi da shiga irli ga waxannan zavavvun bayin Allah waxanda Allah ya zave
69
su a matsayin waziran Manzonsa don su taimaka masa iyar da aikensa.
Rafilawa suna qudure cewa Sahabbai baki xayansu sun yi ridda kuma sun kafirta sai kaxan daga cikinsu. Babban malaminsu a fannin ruwaya, wanda suke xaukar sa kamar yadda muka xauki Bukhari a fannin Hadisi, watau Kulaini, ya karvo daga Abu Ja’afar ya ce, ‚Mutane baki xaya sun yi ridda bayan Annabi (SAW) sai mutum uku kawai. (Mai ruwaya ya ce) sai na ce: Su waye mutum ukun? Ya ce: Miqdad binul Aswad da Abu Zarrin Algifari da Salman Alfarisi.‛ (Alraulatu minal Kafi, 8/245 – 246). Wani malamin nasu da suke kira Almufid ya savawa wannan ruwaya kaxan inda ya xaga adadin Sahabban da suka rage a kan Musulunci bayan rasuwar Annabi (SAW) zuwa bakwai. Almufid ya qarrara a cikin littafinsa Al’ikhtisas, cewa mutum uku ne kawai daga Sahabbai ba su yi ridda ba. Su ne: Salman Alfarisi da Abu Zarrin da Mikadad amma daga baya wasu mutum huxu sun riske su don adadin ya xaga zuwa bakwai. Waxannan su ne: Ammar binu Yasir, Abu Sasan Al’ansari, Huzaifa binul Yaman da Abu Amrah. (Duba Al’ikhtisas, 6). Almufid har yau, ya
70
ruwaito ijma’in Shi’a a kan kafirta sauran Sahabbai baki xaya. (Duba Awa’ilul Maqalat, 45).
Amma mene ne dalilin wannan tsatssauran hukunci a kan zavavvun halitta bayan annabawa da manzanni? Mene ne dalilin da ya sa ‘yan Shi’a suke kafirta Sahabbai? Dalilan guda biyu ne rak, babu daxi babu ragi. Na xaya shi ne faxinsu cewa wai Manzon Allah (SAW) ya yi wasiya cewa Ali binu Abi Xalib ya zama khalifa a bayansa amma sai Sahabbai suka qi qemadagas su aiwatar da wannan wasiya. Maimakon haka sai suka naxa Abubakar ya zama khalifa kuma daga bayansa suka naxa Umar da Usman. Sai a karo na huxu ne aka baiwa Ali wannan matsayi. Dalili na biyu, a lokacin da fitina ta taso a tsakanin al’umma sakamakon kisan gila da aka yiwa Sarkin Musulmi Usman, yaqi ya auku tsakanin Sarkin Musulmi Ali da jama’arsa a hannu guda da kuma Xalha da Zubair da Aisha tare da magoya bayansu a xaya hannun. To da waxannan dalilai biyu ne Rafilawa ke kafirta Sahabbai: hana Ali imama a farkon rasuwar Annabi (SAW) da kuma yaqi da shi a zamanin imamarsa. (Duba Awa’ilul Maqalat, 45 da Al’anwarul Nu’umaniya, 2/244).
71
Aqidar ‘yan Shi’a dangane da Sahabbai ba ta tsaya kan kafirta su ba kawai, amma suna ganin cewa su Sahabbai su ne mafiya sharrin halittar Allah, wall iyazu billah!! Watau ke nan ko a cikin kafiran ma su tantirai ne. Kuma suna qudure cewa imani da Allah da Manzonsa ba ya tabbata sai an barranta daga gare su, musamman dai manya-manyansu kamar Abubakar da Umar da Usman da Aisha da Hafsa da sauran ire-irensu. Muhammad Baqir Almajlisi, xaya daga cikin manyan malaman Shi’a ‘yan baya (ya rasu a shekera ta 1111 B.H), yana cewa: ‚Aqidarmu ta barranta ita ce cewa mu muna barranta daga gumaka huxu: Abubakar, Umar, Usman da Mu’awiya; da mataye huxu: Aisha, Hafsa, Hindu da Ummul Hakam; kuma muna barranta daga dukkan mabiyansu da magoya bayansu; kuma muna qudure cewa su ne mafiya sharrin halittar Allah a bayan qasa; kuma cewa imani da Allah da Manzonsa da imamai ba ya tabbata sai bayan an barranta daga maqiyansu (watau maqiyan Allah da Manzo da imamai xin waxanda, a ganinsu, su ne Sahabbai). (A duba Haqqul Yaqin na Almajlisi, 519).
72
Rafilawa suna qudure cewa khalifofi guda uku, watau Abubakar da Umar da Usman, da kuma Uwayen Muminai, watau matan Annabi (SAW) musamman Aisha da Hafsa, za’a yi musu azaba mai tsanani ranar Alqiyama tare da mafi sharrin bayi da manyan xagutan kafirai. Ya zo a cikin Tafsirul Qummi na Ali binu Ibrahim binu Hashim Alqummi, xaya daga manyan malaman Shi’a magabata (ya rasu a shekara ta 307 B.H.), a wajen fassarar Suratul Falaq, ya ce, ‚Falaq wata rijiya ce a Jahannama, ‘yan wuta suna neman tsari saboda tsananin zafinta. Sai ta roqi Allah saboda tsananin zafinta a yi mata izini ta yi numfashi. Da ta yi numfashi sai ta qone Johannama baki xaya. A cikin wannan rijiya akwai wani akwati, mutanen dake cikin rijiyar suna neman tsari saboda tsananin zafin akwatin wanda ake kira sunduqi. To a cikin wannan sunduqin akwai mutane shida daga al’umman farko da mutane shida daga al’umman qarshe. Shidan dake daga al’umman farko su ne xan (Annabi) Adamu wanda ya kashe xan uwansa (watau Qabila wanda ya kashe Habila); da Lamaruzu (na zamanin Annabi) Ibrahimu wanda ya jefa Ibrahimu a wuta; da Fir’auna (na zamanin Annabi) Musa, da Samiri wanda ya
73
bautawa xan maraqi; da wanda ya yahudantar da Yahudawa da kuma wanda ya nasarantar da Nasara. Su kuwa mutane shida waxanda suke daga al’umman qarshe su ne: na xaya, da na biyu, da na uku, da na huxu, da mutumin Khawarijawa da Ibnu Muljam (wanda ya kashe Ali), Allah ya la’ance su baki xaya.‛ (Tafsirul Qummi, 2/449). Abinda mai littafin yake nufi da na xaya shi ne Abubakar, na biyu Umar, na uku Usman, na huxu kuma Mu’awiya, Allah ya yarda da su baki xaya. Voye sunayen waxannan khalifofi da yin nuni zuwa gare su da alqaluma abu ne wanda duk mutumin da ya saba karatun littafan ‘yan Shi’a ya sani. Kuma dubi yadda ya qare da la’antar su, saboda a wajensa su ne mafi kafircin al’umman qarshe waxanda suka cancanci zama a cikin wannan sunduqi na wuta.
A wani ya yi suna nuni zuwa gare su da wasu alamu kamar yadda ya zo a cikin wannan nassi wanda muka naqalto daga littafin Tafsirul Iyashi: ‚Za’a zo da Jahannama (ranar Alqiyama) tana da qofofi bakwai. Qofar farko ta azzalumin wanda shi ne xan qaramin mai fatsi – fatsi; qofa ta biyu ta dila; qofa ta uku ta na ukun; qofa ta huxu ta Mu’awuya; qofa ta biyar ta Abdul Malik;
74
qofa ta shida ta Askar binu Husir; qofa ta bakwai ta Abu Salamatu. Waxan nan qofofin (shiga wuta) ne ga waxanda suka bi su.‛ (Tafsirul Iyashi na Muhammad binu Mas’ud Al’iyashi, 2/243).
Masana qwararru dangane da Shi’a da rubuce – rubucensu, kamar Ihsan Ilahi Zahir, sun bayyana cewa, wanda suke nufi da xan qaramin mai fatsi – fatsi shi ne Abubakar saboda fatsin idanunsa. Dila kuwa Umar suke nufi da shi saboda iya janhurunsa. Tana yiwuwa ya zama Askar binu Husin kinaya ce ga wani khalifan Banu Umayya kuma Abu Salamatu, kusan babu shakka, Aisha suke nufi da shi. Haka ‘yan Shi’a suke voye sunayen Sahabbai idan suna nufin zaginsu amma kuma suna jin tsoro, ko kuma suna son su yaudari mutane waxanda ba su gama kama su a hannu ba.
Rafilawa suna nuna qiyayya ta musamman ga Sarkin Musulmi Umar binul Khaxxabi. Daga cikin irin ruwayoyin da suka keve masa shi kaxai akwai abinda wani malaminsu mai suna Ni’imatullahi Aljaza’iri ya ruwaito. Ya ce, ‚Abinda yake xaure kai shi ne, yaya Ali (A.S) ya aurawa Umar binul Khaxxabi (diyarsa) Ummu Kulthum, alhali kuwa miyagun ayyuka sun bayyana daga
75
gare shi kuma ya yi ridda ga barin addini sama da riddar duk wani mai ridda. Har ma ruwayoyi sun taho da cewa (ranar Alqiyama) za’a yiwa Shaixan ququmi da sasari saba’in na baqin qarfen Jahannama sa’an nan a ja shi zuwa ga taron hisabi. Sai ya duba gabansa, sai ya ga wani mutum mala’ikun azaba suna kora shi, an ququmce shi da sasari xari da ishirin na Jahannama. Sai Shaixan ya kusanto shi ya ce: Me mara rabo ya yi har ya fi ni azaba, alhali ni na vatar da halitta baki xaya, na kai su ga halaka? Sai Umar ya ce da Shaixan: Ba abinda na yi sai dai na qwace ma Ali binu Abi Xalib khilafa. Ga alama yana ganin qanqantar abinda ya aikata; bai sani ba cewa duk abinda ya faru a duniya na kafirci da zalunci, ya auku ne a dalilin wannan aika – aika tasa.‛ (Al’anwar Alnu’umaniya na Aljaza’iri, 1/81-82).
Duba ka gani mai karatu, yadda Iblis xan Lis da kansa yake baya da Umar (R.A) wajen azaba saboda wai Umar xin ya hana Ali khilafa. Allah ya fisshe mu vata.
Qiyayyar ‘yan Shi’a ga Sahabban Annabi ta kai matuqa har suka halasta la’antar su. Kai ba ma kawai sun halasta la’antar su ba, a’a sun xauke ta ibada da suke neman kusanci ga Allah da ita. Kuma ko cikin
76
Sahabban ma, qiyayyarsu ta fi tsanani ga shugabanninsu mafifita, Abubakar da Umar. Duba wannan ruwaya da Mulla Kazim ya naqalto, yana dangana ta bisa qarya ga Ali Zainul Abidin binu Hussain binu Ali binu Abi Xalib. Ya ce, Abu Hamza Althumali ya karvo daga Ali Zainul Abidin ya ce, ‚Wanda ya la’anci Jibtu da Xagutu (Abubakar da Umar) la’ana guda, Allah zai rubuta masa lada dubu sau dubu, ya kankare masa zunubi dubu sau dubu kuma ya xaukaka masa daraja dubu sau dubu saba’in. Kuma wanda ya la’ance su da yammaci la’ana guda za’a rubuta masa kamar haka. (Mai ruwaya) ya ce: Sai shugabanmu Ali binu Hussaini ya wuce (bayan ya faxi wannan magana, ni kuma) sai na shiga wurin shugabanmu Abu Ja’afar Muhammad Albaqir na ce masa: Ya shugabana, wata magana ce na ji daga mahaifinka. Sai ya ce: Faxe ta mu ji, ya Thumali. Sai na maimaita masa maganar. Sai ya ce: Haka take, Thumali. Ko kana so in yi maka qari? Sai na ce: E, ya shugabana. Sai ya ce: Wanda ya la’ance su la’ana guda a ko wace safiya ba za’a rubuta masa zunubi ba a wannan wunin har yammaci, kuma wanda ya la’ance su la’ana guda da yammaci ba za’a rubuta masa zunubi ba
77
har ya wayi gari.‛ (Duba Ajma’ul Fala’ihi na Mulla Kazim, 513).
Banda wannan ma, akwai addu’o’i na musamman waxanda aka wallafa su, aka tsara su, waxanda kuma suka qunshi la’ana da tsinuwa da miyagun lafuza ga waxan nan manyan Sahabbai, Abubakar da Umar (R.A) waxanda yan Shi’a suke yin wurdi da su, suna maimaita su safe da yammaci kamar yadda Musulmi yake maimaita Ayatal Kursiyu da Amanar Rasulu da Laqad Ja’akum. Waxan nan irin addu’o’i suna da yawa ainun kuma suna nan cikin littafansu na wuridai da azkaru. Bari mu kawowa mai karatu guda xaya rak a matsayin misali, tare da roqon Allah Maxaukaki da ya gafarta mana zunubin maimaita irin waxan nan addu’o’i, koda yake malamai sun ce: ‚Hakaito kafirci ba kafirci ba ne.‛
Akwai wata mashahuriyar addu’a da suke cewa Du’a’u Sanamai Quraish, watau Addu’ar Gumakan Quraishawa Biyu (suna nufin Abubakar da Umar). Ga yadda addu’ar take a Larabci, kafin daga baya mu kawo fassararta:
‚Allahumma Salli ala Muhammadin wa Ali Muhammadin, wal’an Sanamai Quraishin wa Jibtaihima
78
wa Xagutaihima wa ifkaihima wa ibnataihima allazaini khalafa amraka, wa ankara wahyaka, wa jahada in’amaka, wa asaya Rasulaka, wa qallaba dinaka, wa harrafa kitabaka….. Allahumma il’anhuma fi maknunis sirri, wa zahiril alaniya, la’anan kathiran abadan, da’i’man sarmadan, la inqixa’a li amadihi, wa la nafaza li adadihi, la’anan ya’udu awwaluhu wa la yaruhu akhiruhu, lahum wa li a’awani him, wa ansari him, wa muhibbi him, wal muqtadina bi kalami him, wal musaddiqina bi ahkami him…. Allahumma azzib hum azaban yastagithu minhu ahlun nari, amin ya Rabbal Alamin.‛
Ma’anar addu’ar: ‚Ya Allah ka yi daxin tsira ga Muhammad da alayen Muhammad. Kuma ka la’anci gumakan Quraishawa biyu, da jibtinsu da xagutunsu, da qarerayinsu da xiyansu mata biyu. Waxanda suka sava umarninka, suka yi musun wahayinka, suka butulce ma ni’imarka, suka juya addininka, suka sauya littafinka…. Ya Allah ka la’ance su a cikin voyayyen sirri da zahirin dake sarari, la’ana mai yawa ta har abada, madauwamiya ta dun-dun-dun, wacce babu yankewa ga nisanta kuma babu qarewa ga adadinta, la’ana wacce farkonta zai riqa
79
komowa kuma qarshenta bai tafiya, gare su da masu mara musu da mataimakansu da masu qaunarsu da masu koyi da maganarsu da masu gaskatawa da hukunce – hukuncensu….. Ya Allah ka yi musu azaba, azabar da ‘yan wuta za su riqa neman tsari da ita, amin ya Ubangijin Talikai.‛ (Domin ganin wannan addu’a, sai a duba Miftahul Jinani fi Al’ad’iya wal Ziyarat wal Azkar, ba’a san marubucinsa ba, 113-114).
Mai karatu zai lura da ambaton gumakan quraishawa biyu waxanda, a zaurancen Shi’a, ake nufin Abubakar da Umar da su. Kuma xiyansu mata biyu su ne Aisha xiyar Abubakar da Hafsa xiyar Umar matan Manzon Allah (SAW), Allah ya yarda da su baki xaya.
Wannan mugunyar addu’a tana da matsayi maxaukaki a tsakanin miyagun addu’o’in Rafilawa waxanda suke maimaita su safe da yammaci da niyar bautar Ubangiji a riyawarsu. Daga cikin irin falalarta, sun ruwaito cewa wai Ali binu Abi Xalib (R.A) ya kasance yana qunuti da ita cikin sallolinsa kuma ya ce, ‚Wanda yake addu’a da ita kamar wanda ya halarci yaqi ne tare da Annabi (SAW) a Badar da Uhudu da Hunain
80
kuma ya yi jifa da masu dubu sau dubu.‛ (Ilmul Yaqin fi Usulid Din na Muhsin Kashani, 2/101).
Abinda ya gabata a wannan babi xan misali ne kawai na gabar Rafilawa da qiyayyarsu ga zavavvun wannan al’umma, Sahabban Annabi (SAW). Kuma wannan gaba haka take tun ran da maqiyin Allah, Abdullahi binu Saba’i bayahude, ya saka qwan wannan qungiya ya qyanqyashe. Kuma a kan wannan aqida ne ‘yan Shi’a na wannan zamani suke. Bari ka ji abinda shugabansu kuma babban malaminsu na wannan zamani, watau Khumaini yake cewa. Ya zo a cikin littafinsa Kashful Asrari kamar haka: ‚Mu a nan babu ruwanmu da tsofaffi biyu (yana nufin Abubakar da Umar) da abinda suka aikata na savawa Alqur’ani da wasa da suka yi da hukunce – hukuncen Allah da abinda suka halasta ko suka haramta daga qashin kansu da abinda suka aikata na zalunci a kan Faxima xiyar Annabi (SAW) da kuma sauran ‘ya’yansa. Sai dai mu a nan muna nuni ne zuwa ga jahilcinsu da hukunce – hukuncen Allah da addini.‛ (Kashful Asrari, 126). Kuma Khumaini ya zargi Sayyidina Abubakar da Sayyidina Umar da sauya Alqur’ani ya ce, ‚Lallai Allah ya ambaci nau’in mutane
81
takwas waxanda suka cancanci rabo a cikin zakka, amma sai Abubakar ya jefar da nau’i guda daga cikin waxannan nau’o’in mutane bayan da Umar ya zuga shi ya yi haka.‛ (Kashful Asrari, 131). Kuma har yau ya jefa musu kalmar kafirci: ‚Babu shakka su (Sahabbai) sun baiwa Annabi haqqinsa yadda ya kamata (ba’a yake yi). Annabi wanda ya wahala, ya sha fama kuma ya jure dukkan musifu domin shiryar da su, sa’an nan ya cika (a lokacin rasuwarsa) alhali yana jin kalmomin Xan Khaxxabi waxanda aka gina a kan kafirci da zindiqanci.‛ (Kashful Asrari, 137).
Wannan mugunyar aqida kuma har yau, a kanta ne ‘yan Shi’ar Nijeriya suke kamar yadda muka sha ji da kunnuwanmu kuma muka sha gani da idanunmu. Muna roqon Allah Maxaukaki ya shirye su, ya arzuta su da kyakkyawar tuba kafin zuwan ajalinsu.
Sahabban Annabi (SAW), Allah ya yarda da su, ba su buqatar mu yi wani bayani domin kuvutar da su da barrantar da su daga abin da ‘yan Shi’a suka dangana musu na kafirci da ridda da zalunci; saboda babu wani mai da’awar Musulunci da yake tababar imaninsu da xaukaka da falalarsu sai fa wanda Allah ya makantar da
82
basirarsa. ‚Kuma wanda Allah ya vatar to, ba shi da wani mai shiryarwa.‛ (Suratu Ghafir: 33). Amma za mu kawo wasu ayoyi na Alqur’ani waxanda suke nuna cewa qudure aqidar Shi’a dangane da Sahabbai qaryatawa ne ga Alqur’ani, qaryata Alqur’ani kuwa kafirci ne. Ba za mu kafa hujja da Hadisi ba a nan; saboda ‘yan Shi’a ba sa karvar hadisan da malaman Sunna suka ruwaito koda sun zo a cikin Bukhari da Muslim. Amma za mu kafa hujja da ayoyi ne, tare da fatan cewa waxanda ba su riga suka yi nisa ba za su komo ga barin qudure wannan mugunyar aqida.
Allah ya yarda da Sahabbai. Ubangiji Maxaukaki ya ce, ‚Kuma magabata na farko daga Muhajirina da Ansar da waxanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda da su, su kuma sun yarda da shi, kuma ya yi masu tattalin gidajen Aljanna: qoramu suna gudana a qarqashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo.‛ (Suratut Tauba: 100). Waxanda Allah ya yarda da su ya tanadar musu Aljanna ta ya za’a ce sun kafirta ko sun yi ridda?
Allah ya yi gafara a gare su tare da Annabi. Ya ce, ‚Lallai ne, haqiqa, Allah ya karvi tubar Annabi da
83
Muhajirina da Ansar waxanda suka bi shi, a cikin sa’ar tsanani, daga bayan zukatan wani vangare daga garesu sun yi kusa su karkata, sa’an nan (Allah) ya karvi tubarsu. Lalle shi ne mai tausayi, mai jin qai gare su.‛ (Suratut Tauba: 117). Ma’anar ya karvi tubarsu shi ne ya yi musu gafara. To idan Allah ya yi musu gafara ya wani zai ce sun kafirta ko sun yi ridda ko sun yi zulunci?
Allah ya yarda da su alhali yana sane da abinda yake cikin zukatansu. Ya ce, ‚Lalle ne, haqiqa, Allah ya yarda da muminai a lokacin da suke yi maka mubaya’a a qarqashin itaciyar nan domin ya san abinda ke cikin zukatansu, sai ya saukar da natsuwa a kansu, kuma ya saka musu da wani cin nasara makusanci.‛ (Suratul Fathi: 18). Waxanda suka yiwa Annabi (SAW) mubaya’a a qarqashin wannan itaciya da Allah ya ambata su dubu da xari huxu ne. Allah ya ambata cewa ya yarda da su alhalin yana sane da abinda yake cikin zukatansu kuma ya kira su muminai. To ta yaya ‘yan Shi’a za su ce Sahabban Annabi duka sun yi ridda bayan rasuwarsa sai mutum bakwai kawai? Allah wanda yake ganin abinda yake cikin zukatansu, da ya san za su yi ridda bayan Annabi, ya zai saukar a cikin littafinsa mai
84
tsarki cewa ya yarda da su? Ko kuwa maganar Allah tana tashi ne? Ya ce ya yarda da su; ku kuma ku ce sun yi ridda? Subhanallah! Wannan wane irin xanyen hukunci ne? Jayayya da Allah ko kuwa qaryata littafinsa? ‚Ya Ubangijinmu! Kada ka karkatar da zukatanmu bayan har ka shiryar da mu, kuma ka ba mu rahama daga gunka. Lalle ne, kai, kai ne mai yawan kyauta.‛ (Suratu Ali Imrana: 8).
Aqidar Raja’a
Rafilawa na qudure komowar wasu mutane zuwa duniya bayan mutuwarsu kuma wannan wai zai faru ne a qarshen duniya, a lokacin da Mahadinsu na ‘yan Shi’a zai bayyana.
Wani malaminsu, wanda ya rubuta littafi musamman a kan wannan aqida, ya yi bayaninta a taqaice kamar haka: ‚Ka sani cewa, ita raja’a a asali ana nufi da ita komowar mamata zuwa duniya, kamar a ce ke nan su sun fita daga cikin ta kuma sun komo gareta.‛ (Alraja’a na Ahmad binu Zainiddin Al’ahsa’i, 41).
85
Wani malamin nasu kuma da ake cewa Zanjani ya yi qarin bayani a kan aqidar inda ya bayyana nau’in mutanen da za su komo. Ya ce, ‚Raja’a tana nufin tashin wasu mutane (daga kabari) yayin bayyanar Mahadi (A.S), waxanda suke majivintansa ne, masu qaunar sa, don su rabanta da taimakon sa da mara masa a yayin kafuwar daularsa. Da kuma wasu mutanen waxanda suke maqiyansa ne (za’a tashe su) domin ya yi musu uquba kuma domin su haxu da abinda suka cancanta na azaba da kisa a hannun ‘yan Shi’a, kuma domin a xanxana musu qasqanci da wulaqanci da ganin xaukakar kalmarsa. Kuma raja’a a wurinmu, mu Imamiya ‘yan dozin, tana kevanta da waxanda suka tsarkake imani da kuma waxanda suke kan kafirci tsagwaronsa. Sauran ba’a maganarsu.‛ (Aqa’idul Ithnai Ashariya na Ibrahim Almusawi Alzanjani, 2/228).
Wannan yana nufin cewa, a bisa wannan aqida, nau’i biyu na mutane za su komo bayan mutuwa. Na farko su ne abokan gabar ‘yan Shi’a, watau Sahabbai da Tabi’ai, waxanda suka yi mulki a kan su kuma suka zalunce su, za’a komo da su domin su xanxani kuxarsu, su gamu da sakamakon zaluncinsu kuma su wulaqanta
86
tun a nan duniya. Na biyu su ne imaman Shi’a da manyan mabiyansu waxanda suka mutu da fushin Sahabbai a zukatansu, za’a komo da su domin su huce fushinsu, su rama gayya kuma su more mulki a qarqashin daular Mahadinsu wacce aka haramta musu a rayuwarsu ta farko. Don haka suka ruwaito dangane da Abubakar da Umar (R.A) kamar haka: ‚Idan shugabanmu Sahibuz Zaman (yana nufin Mahdi) ya bayyana, zai je Madina sai ya fito da su (watau Abubakar da Umar) daga qaburburansu, ya yi musu azaba a kan dukkan abinda ya afku na zalunci a wannan duniya a zamanin farko wanda ya haxa da kisan da Qabila ya yiwa Habila; da jefa (Annabi) Yusufu cikin rijiya da ‘yan uwansa suka yi; da jefa (Annabi) Ibrahim cikin wuta da Lamarudu ya yi; da fitar da (Annabi) Musa (daga Misra) yana mai jin tsoro, yana mai sauna; da soke taguwar (Annabi) Salihu; da bautar masu bautar wuta. Sai su samu rabo mafi girma daga nau’o’in wannan azaba duka.‛ (Al’anwarul Nu’umaniya, 1/141).
Malaman Rafilawa sun yi qoqarin samawa wannan mugunyar aqida tasu gindin zama a cikin addinin Musulunci, don haka suka dangana ta zuwa ga
87
wata aya. Sun ruwaito daga imaminsu na huxu, Ali binul Hussain binu Ali binu Abi Xalib, cewa ya faxi dangane da fassarar wannan aya: ‚Lallai ne wanda ya farlanta Alqur’ani a kanka, haqiqa, mai mayar da kai ne zuwa makoma.‛ (Suratul Qasas, 85). Ya ce, ‚Annabinku (SAW) zai komo, haka nan Sarkin Musulmi (watau Ali) da imamai (A.S.).‛ (Tafsirul Qummi, 2/147).
Kuma sun baiwa aqidar muhimmanci ainun ta yadda mutum ba ya zama xan Shi’a na gaskiya sai ya qudure ta. Sun ruwaito daga Imam Ja’afar, ya ce, ‚Ba ya daga cikinmu wanda bai yi imani da raja’armu ba kuma ya yi iqirari da mutu’armu.‛ (Ilmul Yaqin fi Usulid Din, 2/827). Har yau, dangane da muhimmancinta, Ahsa’i yana cewa: ‚Ka sani cewa ita raja’a wani sirri ne daga Allah kuma yin quduri da ita shi ne ainihin fa’idar imani da gaibi.‛ (Alraja’a, 11).
Rafilawa baki xaya sun haxu a kan wannan aqida kamar yadda babban malaminsu Muhammad binu Muhammad binu Nu’uman Almufid ya tabbatar. (Duba littafinsa, Awa’ilul Maqalat, 48).
88
Aqidar Taqiya
Ma’anar Taqiya shi ne bayyana savanin abinda yake zuci, watau mutum ya faxi savanin abinda ya qudure a zuciyarsa ko ya aikata wani aiki tare da nuna cewa ya yarda da aikin amma a zuciyarsa yana ganin aikin ba dai – dai ba ne, bai dace ba, ko kuma haramun ne. Zai yi haka domin yaudara, ko kaucewa wani sharri, ko kuvutar da kai daga hannun abokan gaba.
Khumaini ya bayyana ma’anar taqiya kamar haka: ‚Taqiya ma’anarta ita ce mutum ya faxi magana wacce ta savawa ainihin abinda yake akwai ko ya aikata wani aiki wanda yake sava wa mizanin Shari’a. Zai yi haka saboda tsare jininsa, ko mutuncinsa, ko dukiyarsa.‛ (Kashful Asrari, 147).
Taqiya tana da matsayi mai girma da falala da muhimmanci a cikin tafarkin Shi’anci. Dangane da wannan, Kulaini ya ruwaito daga Abu Ja’afar, ya ce: ‚Taqiya tana daga addinina da addinin iyayena. Kuma babu imani ga wanda bai da taqiya.‛ (Usulul Kafi, 2/219). Har yau, yana ruwaitowa daga Abu Abdullahi wanda ya ce: ‚Kashi tara daga cikin goma na addini
89
yana cikin taqiya. Kuma babu addini ga wanda bai da taqiya.‛ (Usulul Kafi, 2/217).
Rafilawa sun kafa hujja a kan aqidar taqiya da wannan aya: ‚Kada muminai su riqi kafirai masoya baicin muminai. Kuma wanda ya yi wannan, to bai zama a cikin kome ba daga Allah, face fa domin ku yi tsaro daga gare su da ‘yar kariya.‛ (Suratu Ali Imrana, 28). ‚Tsaro da kariya‛ da aka ambata a cikin wannan aya ga shi suka laqe, suna cewa taqiya da suke yi, watau bayyana savanin abinda yake cikin zukatansu, domin tsare kansu ne daga abokan gabansu, kuma qarya da yaudara da suke yi kariya ce suke yi ga kawunansu da dukiyoyinsu. Sai dai babu hujja gare su a cikin wannan aya domin abinda ayar take nufi shi ne Musulmi ya voye abinda bai iya bayyanawa na addininsa a wajen kafirai; amma ba ya bayyana addininsu ko ya nuna ya yarda da shi ba. Kuma zai yi haka ne kawai idan ya ji tsoron rasa ransa ko asarar dukiyarsa da makamancin wannan. Su kuwa ‘yan Shi’a suna nuna yarda da aqidun waxanda suka sava musu, kamar Ahlus Sunna, ko da tsoro ko babu. Wannan kamar yadda Shaihinsu Alxusi ya ruwaito daga Imam Ja’afar Assadiq, ya ce: ‚Ba ya daga
90
cikinmu wanda bai sanya taqiya ba wajen ma’amalarsa da wanda ya amincewa don ta zama xabi’arsa wajen ma’amalarsa da wanda yake tsoro.‛ (Amali Alxusi, 229).
Daga nan za mu fahimci cewa taqiya munafunci ne tsagwaronsa da yaudara wacce ‘yan Shi’a suke amfani da ita wajen voye miyagun aqidojinsu da nuna yarda da aqidojin Ahlus Sunna domin su yaudari mutane, su zambace su, su vatar da su, kuma da wannan ne aka yaudari yawancin matasa masu qarancin sani waxanda a yau suke iqirari cewa su ‘yan Shi’a ne a Nijeriya.
A taqaice waxannan su ne aqidojin Rafilawa guda shida waxanda da su ne suka sha bamban da sauran al’umma kuma a kansu suka gina alaqarsu da sauran jama’ar Musulmi kuma da fahimtarsu ne zamu iya tantance matsayinsu a cikin al’umma.
91
Babi Na Uku
Matsayin Shi’a a Cikin Al’umma
92
Ko ba’a faxi ba, wanda duk ya dubi aqidojin Shi’a kamar yadda muka yi bayanin su a babin da ya gabata, zai iya sanin matsayin ‘yan Shi’a a idanun sauran al’umma. Ahalus Sunna wal Jama’a, waxanda – wal hamdu lillahi – su ne agalabiyar Musulmin duniya, suna duban qungiyar Rafilawa a matsayin ‘yan bidi’a, vatattu waxanda suka qudure miyagun aqidoji da suka savawa Alqur’ani da Sunna da hankali lafiyayye. Haka kuma suna ganin cewa, alal aqalli, wasu daga cikinsu sun fice daga Musulunci xungurum.
A xaya vangaren kuma, su ma ‘yan Shi’a, saboda aqidojin nan da suka qudure, dole ne ya zama suna da wani matsayi wanda suka tsaya a kansa dangane da alaqarsu da sauran al’umma da wata mahanga wacce da ita ne suke hangen sauran Musulmi. Waxan nan abubuwa guda biyu, watau matsayin Rafilawa a wajen al’umma da akasi, su ne abinda za mu duba a cikin wannan babi.
93
Shi’a da Ahlul Baiti
Da yake Rafilawa suna da’awar son Ahalul Baiti, watau iyalin gidan Manzon Allah (SAW), da jivintar su wanda a kan haka suka gina shika-shikan tafarkinsu, to bari mu fara da duba dangantaka tsakaninsu da wannan babban gida da kuma zavavvun mutane da Allah ya yiwa baiwa da zama ‘yan wannan gida.
‘Yan Shi’a suna da’awar son iyalin gidan Annabi (SAW) da zuri’arsa, amma sun kasa su kashi uku. Na farko Ali wanda yake qani ne ga Annabi (SAW) watau xan baffansa ne, mahaifinsa da mahaifin Annabi ubansu xaya, da Faxima wacce ita ce qarama a cikin xiyan Annabi mata guda huxu: Zainab, Ruqayya, Ummu Kulthum da kuma ita Faxima xin. Wannan kashi, Ali da Faxima da ‘ya’yansu, in banda guda Ummu Kulthum (watau ta biyu), da jikokinsu da zuri’arsu su ne ‘yan gaban goshin Rafilawa waxanda suke qauna, suke jivinta suna matuqar girmamawa har ya zuwa haddin bauta.
Kashi na biyu su ne matan Manzon Allah (SAW) uwayen muminai, musamman waxanda suka fi shahara a
94
cikinsu kamar Aisha xiyar Abubakar da Hafsa xiyar Umar, Allah ya yarda da su baki xaya. Waxannan ‘yan Shi’a na qin su matuqar qi, suna la’anatar su, suna qudure kafircinsu kuma suna da yaqini, a ganinsu, cewa su ‘yan wuta ne, masu dauwama a cikin ta.
Kashi na uku su ne sauran xiyan Annabi mata waxanda muka ambata a sama, Zainab, Ruqayya da Ummu Kulthum da zuri’o’insu. Waxannan koda yake suma ‘ya’yan Annabi (SAW) ne na tsatsonsa, amma ‘yan Shi’a suna yin burus da su, ba sa ko ambaton su, babu imamai a cikin zuri’arsu kuma ba su da wata daraja ko matsayi na musamman. Kuma a cikin wannan kashi suka sanya xiyar Ali da Faxima wacce muka toge a sama, watau Ummu Kulthum (ta biyu). Koda yake Ummu Kulthum Ali da Faxima ne suka haife ta, kuma Hussaini binu Ali ne ya saki nono ya ba ta, amma Rafilawa ba su sa ta a jerin zuri’ar Annabi (SAW) masu daraja ba. Laifinta shi ne wata qaddara da ta faxa mata ta auri Sarkin Musulmi Umar binul Khaxxabi (RA). Don haka ‘yan Shi’a suka kore ta daga jerin zuri’ar Ali da Faxima.
95
Daga nan mai karatu zai fahimci cewa da’awar Shi’a ta son Ahalul Baiti da jivintar su da’awar qarya ce wacce aka gina ta a kan jahilci da munafunci da son zuciya. Idan da a ce wannan da’awar gaskiya ce, ta ya ya za su bambance tsakanin Aisha matar Annabi da Faxima xiyarsa? Ko ta ya za su bambance tsakanin xiyan Annabi mata waxanda dukkaninsu uwarsu xaya ubansu xaya? Kuma ta ya za su bambance tsakanin Hassan da Hussaini da kuma qanuwarsu Ummu Kulthum waxanda uwa xaya, uba xaya suka haife su?
Abinda muka ambata a nan na soyayya da jivintar da ‘yan Shi’a suke da’awa ga Ahlul Baiti, mun kawo shi a dunqule ne amma bayaninsa filla-filla ya gabata. Dangane da kashi na farko, Ali da Faxima da zuri’arsu, mun ga matsayin da Rafilawa suka ba su a inda muka yi magana a kan aqidar imama. Mun ga yadda suka girmama su, suka kambama su, suka ajiye su a wani matsayi, wanda yake sama da matsayin annabawa da manzanni, sa’annan daga bisani suka ba su sifofin allantaka.
Dangane da kashi na biyu kuwa, watau matan Annabi (SAW) uwayen muminai, musamman Aisha da
96
Hafsa, mun gabatar da bayani, a cikin babin aqidar Shi’a da Sahabbai, yadda Rafilawa suke la’antar su tare da mahaifansu, Abubakar da Umar, a cikin addu’arsu da suke cewa Du’a’u Sanamai Quraish, watau Addu’ar Gumakan Quraishawa Biyu. Sai dai muna so mu qara wani abu a nan wanda yake nuna cewa har Manzon Allah (SAW) bai tsira ba daga ta’annuti da jafa’in Rafilawa. Wannan shi ne abinda suka ruwaito cewa: ‚A lahira za’a qona al’aurar Annabi (SAW), watau zakarinsa, saboda auren Aisha da ya yi.‛ Ibn Taimiya ne ya hakaito wannan xanyar magana tasu a cikin Fatawa nasa (mujalladi na 28, shafi na 262). Kuma tabbacin wannan ya zo a littafin Kashful Asrari wa Tabri’atil A’immatil Axhari na Sayyid Hussain Almusawi, wanda a da xan Shi’a ne kuma ya tuba. Ya rubuta cewa, xaya daga manyan malaman hauza (hauza a wurin ‘yan Shi’a kamar zawiya ne a wurin ‘yan xariqa) mai suna Sayyid Ali Garawi ya ce, ‚Lallai Annabi (SAW) babu makawa sai al’aurarsa ta shiga wuta saboda ya auri wasu mata mushirikai.‛ Yana nufin A’isha da Hafsa. (Duba Kashful Asrari na Musawi, 21-22). Wannan magana wacce ‘yan Shi’a na da suke yin ta, kamar yadda Ibnu Taimiya ya
97
hakaito kuma ‘yan Shi’a na wannan zamani suke yin ta, kamar yadda Musawi ya hakaito, ba wani Musulmi da zai yi shakkun kafircin wanda yake yin ta. Ubangiji muna neman tsarinka daga kafirci da munafunci da vata.
Su kuwa kashi na uku, watau sauran xiyan Annabi mata, Zainab da Ruqayya da Ummu Kulthum, ‘yan Shi’a suna yin burus da su, kamar yadda muka bayyana a sama, ba sa ko ambaton su. Amma da yake mun sanya Ummu Kulthum, xiyar Faxima kuma qanuwar Hassan da Hussaini, a cikin wannan kashi, bari mu tunawa mai karatu da abinda Ni’imatullahi Aljaza’iri, wani babban malamin Shi’a, yake faxi, ‚Abin xaure kai shi ne yadda Ali (A.S) ya aurawa Umar binul Khaxxabi xiyarsa Ummu Kulthum tare da cewa miyagun ayyuka sun bayyana daga gare shi (shi Umar) kuma ya yi ridda daga Musulunci fiye da riddar ko wane mai ridda.‛ (Al’anwarul Nu’umaniya 1/81). Watau auren Umar shi ne laifin Ummu Kulthum kuma shi ya sa ta rasa daraja koda yake ita ma xiyar Ali da Faxima ce, kamar Hassan da Hussaini.
98
Ahlul Baiti da Shi’a
Iyalin gidan Annabi (SAW) da zuri’arsa, kamar sauran malaman Ahlus Sunna, suna xaukar qungiyar Rafilawa a matsayin ‘yan bidi’a vatattu, waxanda suka yi nesa da gaskiya da shiriya. Kuma suna zargin su mafi tsananin zargi suna barranta daga garesu saboda qarerayin da suka dangana musu a cikin ruwayoyinsu na shifcin gizo. Dukkanin imaman Shi’a, waxanda suke daga Ahlul Baiti, suna barranta daga Rafilawa da kuma miyagun aqidoji da suke dangana musu. A nan za mu kawo xan misali kaxan na maganganun imaman Ahlul Baiti dangane da Rafilawa masu riya cewa su masoyansu ne, masu jivintar su.
Maganar Ali Binu Abi Xalib
An ruwaito yana faxawa ‘yan Shi’arsa, alhali yana qosawa da jahilcinsu da taurin kansu da rashin biyayyarsu. ‚Ya mazare masu kamar maza, ya masu hankulan jarirai da qwaqwalen ma’abota mundaye. Na so a ce inama ban tava ganin ku ba; ban san ku ba. Saninku wallahi ya jawo nadama, ya haifar da fargaba.
99
Allah wadaranku! Kun cika zuciyata da baqin ciki, kun loda kirjina da fushi kuma kun shayar da ni maxin takaici. Kun vata mun tsari ta hanyar savawa da basarwa har Quraishawa suna cewa: Xan Abi Xalib namiji ne gwarzo, amma bai da dabarar yaqi. To ina dabara ga wanda ba a yiwa biyayya?!‛ (Nahjul Balaga na Sharif Alradi, 70-71).
Maganar Hassan binu Ali
An ruwaito daga Amru binul Asam, ya ce: Na ce da Hassan Shi’a suna riya cewa Ali za’a tashe shi (bayan mutuwarsa) kafin ranar Alqiyama. Sai ya ce, ‚Sun yi qarya. Na rantse da Allah waxan nan ba Shi’a ba ne. Da mun san za’a tashe shi da ba mu aurar da matansa ba kuma da ba mu raba gadonsa ba.‛ (Duba Almusnad na Imam Ahmad binu Hanbal, 1/148).
Maganar Hussaini binu Ali
Hussaini ya faxi dangane da ‘yan Shi’a na qasar Iraqi, waxanda suka nemi ya zo qasarsu za su taimake
100
shi, amma bayan ya zo sai suka bashe shi, suka miqa shi ga abokan gabansa waxanda suka kashe shi. Ya ce, ‚Ya Ubangiji! Lallai mutanen Iraqi sun ruxe ni, sun yaudare ni. Ya Ubangiji! Ka watsa taronsu, ka kashe su kisa.‛ (Siyaru A’alamil Nubala, na Zahabi, 3/302).
Maganar Ali binu Hussain
An ruwaito ruwaya ingantacciya daga gareshi yana cewa: ‚Ya ku mutanen Iraqi, ku so mu son Musulunci, kada ku so mu son gumaka. Son ku bai gushe ba gare mu har ya zama aibu a kanmu.‛ (A duba littafin Hilyatul Auliya na Abu Nu’aim Al’asbahani, 3/137).
Maganar Muhammad binu Ali
Muhammad binu Ali Albaqir, wanda Shi’a suke lasafta shi a matsayin imaminsu na biyar, yana cewa: ‚Lallai a Iraqi akwai wasu mutane suna riya cewa suna son mu, amma kuma suna zagin Abubakar da Umar sa’annan su ce ni na umarce su da yin haka. Ku ba su labari cewa ni ina barranta zuwa ga Allah Maxaukaki
101
daga garesu. Na rantse da Allah ni barrantacce ne daga garesu. Na rantse da wanda ran Muhammadu yake hannunsa, in da za’a naxa ni (Sarkin Musulmi) da na nemi kusanci ga Allah ta hanyar kashe waxan nan mutane. Kada ceton (Annabi) Muhammad ya same ni idan ban kasance ina roqa musu (Abubakar da Umar) gafara da rahama ba. Amma maqi yan Allah (masu zagin su) sun rafkana ga barin su.‛ (Al’intisar Lil Sahbi Wal Ali na Ibrahim binu Amir Arruhali, 117).
Maganan Ja’afar binu Muhammad
An ruwaito daga Abduljabbar binu Abbas Alhamdani cewa Ja’afar binu Muhammad, imamin Rafilawa na shida, a riyawarsu, ya zo wurinsu a lokacin da suke shirin barin Birnin Madina. Ya ce, ‚Ku, in Allah ya so, kuna daga cikin managartan mutanen qasashenku. Ku faxawa mutanen garinku cewa, wanda duk ya riya cewa ni imami ne ma’asumi wanda ya wajaba a yi masa xa’a, to ni na barranta daga gare shi. Kuma wanda duk ya riya cewa ni ina barranta daga Abubakar da Umar, to
102
ni na barranta daga gare shi.‛ (Siyaru A’alamil Nubala, 6/259).
A taqaice waxannan wasu ne daga maganganun shiyagabannin Ahlul Baiti waxanda suke nuna matsayinsu ga Rafilawa da qarerayi da suke laqa musu da kuma miyagun aqidoji da suke danganawa gare su. Babu tantama waxannan maganganu suna nuna barrantar Ahlul Baiti daga ‘yan Shi’a waxanda suka xauki sonsu da jivintarsu a matsayin wani mayafi wanda suke lulluve munafincinsu da mugunyar manufarsu ta rushe addini da shi.
Shi’a da Ahlus Sunna
A cikin abinda ya gabata na bayani, mun ga munafuncin Shi’a a fili, da yadda suka fake da qaunar Alhul Baiti domin rusa addini daga cikinsa da kuma yadda asirinsu ya tonu da shaidar shiya gabannin Ahlul Baiti kansu.
A yanzu za mu karkata akalar alqalami don mu duba dangantakar Rafilawa da sauran shiyagabannin Ahlus Sunna.
103
‘Yan Shi’a da xai ba su tava voye matuqar gabarsu da qiyayyarsu ga magabatan wannan al’umma ba da limamanta da malamanta, tun daga kan Sahabban Annabi (SAW) har ya zuwa yau. Kuma idan mai karatu ya yi tunani dangane da wannan qiyayya zai ga cewa asalinta ya samo tushe daga Yahudawa da Majusawa, waxanda Musulunci ya rushe daulolinsu na zalunci da addinansu na qarya don haka suka qudure gaba kuma suka lashi takobi sai sun ga bayan wannan addini. Amma da yake ba su da qarfi an riga an rinjaye su a fagen fama, to sai suka xauki hanyar munafunci domin cimma manufarsu. Sai suka yafa mayafin son Ahalul Baiti, kuma a lokaci guda suna sukan galibin Sahabbai da malaman Tabi’ai da Tabi’an Tabi’ai, waxanda su ne suka naqalto wannan addini, da nufin cewa idan suka rusa su to addini ya rushe. Wani abu da yake qara tabbatar da wannan shi ne cewa, ‘yan Shi’a suna qin mutum gwargwadon hidimarsa ga Musulunci. Qiyayyarsu ta fi tsanani ga waxanda suka fi gabatar da hidima mai girma ga Musulunci. Wannan ya sa suka fi qin Abubakar da Umar fiye da kowa.
104
Mun riga mun gabatar da bayanin qiyayyar Rafilawa ga Sahabbai, da yadda suka kafirta su kuma suka zarge su da manyan ayyukan kafirci, kamar sauya Alqur’ani da sauransu. A nan za mu kawo misalai kaxan na sukansu ga manyan malaman Tabi’ai.
Sukansu ga Muqatil
Sun soki Muqatil, xaya daga manyan malaman Tabi’ai waxanda suka xauki ilmi wajen Sahabbai. Sun jefe shi da qarya da qaga hadisi. Suka ce, ‚Malaman hadisi sun haxu a kan cewa shi maqaryaci ne.‛ Babu shakka malamai a nan malamansu suke nufi, kuma hadisi suna nufin irin ruwayoyinsu na almara.
Sukansu ga Muhammad binu Sirina
Binu Sirina wani malamin Tabi’i ne wanda ya sha zagi da sokan Rafilawa saboda hidima da ya gabatar ga Sunnar Annabi (SAW). Sun zarge shi da la’antar Sarkin Musulmi Ali (R.A), suka ce, ‚Malami ne da yake koyar da ‘ya’yan Hajjaju. Da yawa yana jin sa yana la’antar Ali, amma ba ya yi masa inkari.‛
105
Sukansu ga Zuhuri
Muhammad binu Muslim Alzuhuri na xaya daga mashahuran malaman Tabi’ai waxanda suka yi hidima ga addinin Musulunci ta hanyar tattara Sunnar Annabi (SAW) da tace ingatacciyarta daga mai rauni. A sakamakon haka, ya sha zagin Shi’a, sukansu da vatancinsu. Sun jefe shi da qaga hadisi da laqa qarya ga Annabi da kuma qin Sarkin Musulmi Ali binu Abi Xalib (R.A). Suka ce, ‚Ya kasance yana qaga hadisi da umarnin xiyan Marwana kuma shi da Abdulmalik suna la’antar Ali.‛
Marwana shi ne binul Hakam binu Abul Aas. Khalifa ne daga khalifofin Banu Umayya, dangin Sarkin Musulmi Usman waxanda Rafilawa suke matuqar adawa da su. Zuri’arsa da yawa sun zama khalifofi; Abdulmalik yana cikinsu.
Banda zargin la’antar Ali da qaga hadisi, yan Shi’a kuma sun zargi Zuhuri da kisan kai. Suka ce, ‚Kuma ya kashe wani bawa nasa.‛
106
Sukansu ga Sha’abi
Sun soki Amir binu Shurahbila Assha’abi, xaya daga manyan malaman Fiqihu da aka yi a duniya. Sun soke shi da barin sallah da wasan dara da ‘yar canke. Suka ce, ‚Sha’abi ya kasance bai damuwa a tayar da sallah shi kuwa yana zaune, yana dara da ‘yar canke. Ya kasance yana dara, idan wanda ya san shi ya wuce, sai ya voye fuskarsa da hannun rigarsa.‛ Kuma sun jefe shi da satar dukiyar Baitul Mali.
Banda waxannan, Rafilawa sun soki xaruruwan malaman Tabi’ai, suka jefe su da miyagun abubuwa kamar qarya, sata, kisan kai, fasiqanci da lalata da sauransu. Malaman da suka soka sun haxa da Sufyanu Althauri, Sa’id binu Musayyib, Sa’id binu Jubair, Hassan Albasri, Khalid Alwasixi, Mansur binul Mu’utamir, Masruq, Ibrahim Alnakha’i, da wasu gomomi da xaruruwa banda waxannan. Mai son qarin bayani dangane da sukan Rafilawa da zage-zagensu ga malaman Tabi’ai sai ya duba littafin Assiraxul Mustaqim ila Mustahiqqi Attaqdim, na babban malaminsu mai suna Zainuddin Ali binu Yunus Al’amili Annabaxi. Soke-
107
soken da muka ambata a sama mun naqalto su daga mujalladi na uku na littafin, shafi na 244 – 254.
Wani abin tsokaci da bai kamata mai karatu ya tsallake shi ba shi ne, dukkan abubuwan da ‘yan Shi’a suka soki waxannan manyan malamai da su abubuwa ne waxanda suke vata adalcin mutum, sai ya zama ba adali ba don haka ba za’a karvi ruwayarsa ba. Wannan ita ce manufarsu: vata Sunnar Manzon Allah (SAW) ta hanyar vata waxanda suka karvo ta daga Sahabbai.
Sukansu ga Imaman Mazhabobi
Kamar yadda Rafilawa suka soki malaman Tabi’ai, haka nan suka soki almajiransu, Tabi’an Tabi’ai da imaman mazhabobi guda huxu. Ga xan misali.
Sukansu ga Imam Abu Hanifa
Suka ce, ‚Abu Hanifa ya halasta qaga hadisi da danganta shi ga Annabi (SAW) a kan qarya idan ya dace da ra’ayin mazhabansa.‛ Haka nan, sun qalawa Abu Hanifa qarya suka ce wai ya ce, ‚Da Manzon Allah
108
(SAW) ya riske ni da ya yi riqo da yawancin maganganuna.‛
Sukansu ga Imam Malik
Sun soki Imam Malik da cewa yana yiwa Sahabbai jafa’i kuma yana shagala da jin kixe – kixe. Suka ce, ‚Malik ya kasance yana ambaton Ali da Usman da Xalha da Zubair, sa’an nan ya ce: Wallahi ba su yi yaqi ba sai a kan abinci da ya yi yami.‛ Kuma suka ce, ‚Muhammad binul Hassan ya je gidan Malik domin ya xauki ilmin hadisi sai ya ji sarewa da goge daga gidan, sai ya yi masa inkari. Sai (Malik) ya ce: Mu ba mu ganin laifin wannan.‛
Sukansu ga Imam Shafi’i
Sun yi wa Imam Shafi’i qazafi, suka jefe shi da luwaxi. Suka ce, ‚Shafi’i ya kasance ba ya koya ilmin hadisi face a gefensa akwai saurayi mara gemu, mai kyawun fuska.‛
109
Sukansu ga Imam Ahmad
Sun soki Imam Ahmad binu Hanbal, suka yi masa qage. Suka ce, ‚Jahili ne mai tsananin gaba (da Ahalul Baiti). Iya magana kaxai gare shi (amma ba ilmi ba); don haka ba’a lasafta shi daga malaman Fiqihu.‛ Kuma suka ce, ‚Ahmad binu Hanbal ya kasance yana cewa: Mutum bai zama Ahalus Sunna sai ya qi Ali koda kaxan.‛ (Domin waxan nan soke – soke, qaryace – qaryace da zage – zage, duba Assiraxul Mustaqim ila Mustahiqqi Attaqdim na Annabaxi, 3/213 – 225).
Sukan Rafilawa ga Malaman Hadisi
Su ma malaman Hadisi ba su tsira ba daga sukan ‘yan Shi’a da qagensu da qazafinsu. A haqiqanin gaskiya, babu wani malamin Hadisi wanda ya yi hidima ga Sunna wanda ba su zage shi ba. A nan za mu isu da misalai biyu kawai.
Sukansu ga Imam Bukhari
Sun soki limamin malamai, Sarkin Musulmi a fannin Hadisi, wanda ya tattara littafin da ya fi ko wane
110
littafi inganci bayan Alqur’ani, Muhammad binu Isma’il Albukhari, Allah ya yi masa rahama. Suka ce, ‚Ba mu ga wanda ya fi shi shahara ba a wajen gama-gari (suna nufin Ahlus Sunna), ko xaukakar daraja, kamar mushen da ya buga, ko mele da ya bayyana kan fuska. Ya voye gaskiya ya nesanta ta, ya bayyana qarya ya matso da ita.‛ Duba ka ga irin wannan kamantawa da suka yi masa da mushe da mele, za ka san mugunyar qiyayya dake zukatan ‘yan Shi’a ga manyan bayin Allah, waxanda suka yiwa addininsa aiki. Da a ce ‘yan Shi’a ba su da wani laifi sai qin Bukhari da ya ishe su aibu.
Sukansu ga Imam Muslim
Sun soki na biyun biyun, mai littafi na biyu wajen inganci a fannin Hadisi, Imam Muslim binu Hajjaj Annaisaburi, Allah ya yi masa rahama. Suka ce, ‚Bukhari da Muslim sun voye hadisai masu yawan gaske waxanda suke magana a kan falalar Ahlul Baiti, tare da cewa hadisan ingantattu ne a bisa sharaxinsu.‛ (A duba Assiraxul Mustaqim na Annabaxi, 3/226-232).
111
Abinda ya gabata xan misali ne qanqane na soke – soken Rafilawa ga malaman al’umma da magabatanta. Kuma ina rantsuwa da Allah cewa duk abinda na kawo a cikin wannan xan littafi na zage-zagen ‘yan Shi’a da soke-sokensu da qarerayinsu da qazafinsu ga magabatan wannan al’umma da malamanta bai kai kashi biyar cikin xari ba na abinda yake qunshe cikin xima-ximan littafansu waxanda ke cike da sharri da fajirci da qin Allah da Manzonsa da yin zagon qasa ga wannan addini. ‚Allah ne marinjayi a kan al’amarinsa, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba.‛ (Suratu Yusuf: 21).
Ahlus Sunna da Shi’a
Ya gabata cewa malaman Sunna suna duban Rafilawa a matsayin ‘yan bidi’a, vatattu, waxanda suka yi nesa da tafarki madaidaici kuma masu haxarin gaske ga Musulunci da Musulmi. Mun riga mun ji maganganun malaman Ahlul Baiti da imamansu dangane da ‘yan Shi’a. A nan za mu kawo maganganun malaman Musulunci dabam-daban na zamuna daban-daban, da gargaxinsu a kan sharrin Shi’a da haxarinta.
112
Maganar Sufyanu Althauri
An karvo daga Muhammad binu Yusuf Alfiryabi, ya ce: ‚Na ji Sufyanu alhali wani mutum ya tambaye shi dangane da mai zagin Abubakar da Umar, sai ya ce: Ya kafirta da Allah mai girma. Sai ya tambaye shi: Muna yi masa sallah? Ya ce: A’a ko kusa! Ya kuma tambaya: Amma yana cewa La’ilaha illallahu, ya za mu yi da shi? (Sufyanu) ya ce: Kada ku tava shi da hannayenku. Ku tattage shi da katako har ku turbuxe shi a kushewarsa.‛ (Siyaru A’alamil Nubala na Zahabi, 7/253).
Maganar Imam Abu Hanifa
Ya ce, ‚Bin tafarkin Ahlus Sunna wal Jama’a shi ne mutum ya fifita Abubakar da Umar da Ali da Usman. Kuma kada ya vaci ko xaya daga cikinsu.‛ (Al’intisar Lil Sahbi wal Ali na Arruhali, 127). Mai karatu zai lura da bambanci tsakanin ladabi a cikin maganganun malaman Sunna da batsa dake cikin soki-burutsun ‘yan Shi’a. A nan Imam Abu Hanifa Rafilawa yake suka, amma bai zage su ba, bai ko ambaci sunansu ba.
113
Maimakon haka sai ya yi gargaxi dangane da mummunan aikinsu kuma ya koyar da savaninsa wanda yake kyakkyawa. Ya ce, ‚Ka fifita Sahabban Annabi (SAW) kuma kada ka vaci xayansu.‛
Maganar Imam Malik
An ruwaito daga Imam Malik ya ce, ‚Wanda yake zagin Sahabban Annabi (SAW) bai da rabo, ko kuma cewa ya yi: bai da kaso, a cikin Musulunci.‛ (Kitabus Sunna na Khallal, 1/493). Ladabin dake cikin wannan magana ba sai an tona ba. Gwada ta da maganganun malaman Shi’a ka sha mamaki.
Almajirin Imam Malik mai suna Ashhabu ya ce: An tambayi Malik dangane da Rafilawa, sai ya ce, ‚Kada ka yi magana da su kuma kada ka karvi ruwaya daga wurinsu domin suna yin qarya.‛ (Minhajus Sunna na Ibnu Taimiya, 1/61).
Maganar Imam Shafi’i
Ruwaya ta inganta daga gare shi ya ce, ‚A cikin ‘yan bidi’a kaf, ban tava ganin wanda ya fi Rafilawa
114
qarya ba da shaidar zur.‛ (Al’inabatul Kubra na Ibnu Baxxata, 2/545).
Maganar Imam Ahmad
An karvo daga Abdullahi binu Ahmad ya ce: Na tambayi babana dangane da mutumin da ya zagi xaya daga Sahabban Annabi (SAW). Sai ya ce, ‚Ba na ganin yana kan Musulunci.‛ (Kitabus Sunna na Khallal, 1/493).
Kuma har yau, an tambaye shi dangane da mutumin da yake da maqwafci xan Shi’a: yana iya yi masa sallama? Sai ya ce, ‚A’a, sam! Kuma idan shi ya yi masa sallama kada ya amsa.‛ (Kitabus Sunna na Khallal, 1/494).
Maganar Imam Bukhari
A cikin littafin Khalq Af’alil Ibad, Imam Bukhari ya rubuta dangane da Rafilawa: ‚Duka xaya ne a gare ni in yi sallah a bayan Bajahame ko Barafile ko a bayan Bayahude ko Banasare. Kuma ba’a yi musu sallama, ba’a dubo su (idan ba su da lafiya), ba’a auratayya da su,
115
ba’a karvar shaidarsu kuma ba’a cin yankansu.‛ (Duba Al’intisar Lil Sahbi Wal Ali, 132).
Maganar Imam Xahawi
Ya faxi a cikin Aqidarsa, ‚Kuma muna son Sahabban Manzon Allah (SAW); ba ma taqaitawa wajen son xayansu, kuma ba ma barranta daga xayansu. Muna qin wanda yake qin su kuma yake ambaton su ba da alheri ba. Mu ba ma ambaton su sai da alheri. Muna qudure cewa sonsu addini ne da imani da ihsani, kuma qinsu kafirci ne da munafunci da zalunci.‛ (Al’aqidatul Xahawiya, tare da Sharhin Ibnu Abil Izzi, 689).
Maganar Alqali Iyal
Sanannen malamin mazhabar Malikiyya, wanda ya shahara da littafinsa Ashafa, Alqali Iyal, yana cewa: ‚Haka nan kuma muna yanke hukunci da kafircin gulatun Rafilawa waxanda suka ce imamai sun fi annabawa falala.‛ (Asshifa bi Ta’arifi Huquqil Musxafa na Iyal, 2/1078).
116
Maganar Ibnu Taimiya
Shaihul Islam, Ahmad binu Abdulhalim binu Abdulsalam binu Taimiya ya sha fama da ‘yan Shi’a, ya yi gogayya da su kuma ya yaqe su da harshensa da alqalaminsa. Ya yi rubuce – rubuce don fallasa bidi’arsu da tona asirinsu, kamar babban littafinsa Minhajus Sunnatin Nabawiya fi Naqdi Kalamil Shi’ati Wal Qadariya.
Daga cikin maganganunsa dangane da su, yana cewa: ‚Allah ya sani, kuma Allah ya isa masani, cewa a cikin qungiyoyin bidi’a duka, masu dangana kansu da Musulunci, babu wanda ya fi su sharri da jahilci da qarya da zalunci. Babu wanda ya fi su kusa da kafirci da fasiqanci da savo, haka nan babu wanda ya fi su nisa da haqiqanin imani.‛ (Minhajus Sunna, 1/160).
Dangane da jahilcinsu da munafuncinsu, yana cewa: ‚Waxannan Rafilawa (wanda duk ka gani a cikinsu) imma dai munafuki ne ko jahili. Ba’a samun Barafile ko Bajahame sai wanda ya zam munafuki ko wanda ya jahilci abinda Manzo (SAW) ya zo da shi. Ba’a samu a cikinsu wanda yake masani ne da abinda
117
Manzo (SAW) ya zo da shi tare da imani da shi. Lallai savawar su ga abinda Manzo (SAW) ya zo da shi da qaryarsu a kansa, ba sa vuya sai ga wanda ya kai matuqa a jahilci da bin son zuciya.‛ (Minhajus Sunna, 1/161).
Dangane da qaryarsu, yana cewa: ‚Malamai masana a fannin Hadisi da ruwaya sun haxu a kan cewa Rafilawa sun fi dukkan qungiyoyin bidi’a qarya. Qarya a cikinsu ta daxe; saboda haka malaman Musulunci suna sane da kevantarsu da yawan qarya.‛ (Minhajus Sunna, 1/66).
Maganar Muhammad binu Abdilwahhab
Imam Muhammad binu abdilwahhab, sanannen mujaddadi na qasar Makka, yana faxi dangane da Rafilawa bayan ya kawo maganarsu cewa yana halatta mutum ya auri mace tare da goggonta a lokaci guda. Ya ce, ‚Da irin wannan magana tasu za ka san cewa Rafilawa sun fi kowa barin abinda Allah ya yi umarni da shi da aikata abinda ya haramta. Kuma yawancinsu sun samu daga xigon maniyi na zina wanda aka saka a cikin mahaifa ta haramun. Don haka suke dukkaninsu masu
118
miyagun aqidu da miyagun ayyuka, kamar yadda aka ce komai yana komawa ga tushensa.‛ (Duba Al intisar Lil Sahbi Wal Ali, 149).
Maganar Mujaddadi Xanfodiyo
Shaihu Usmanu Danfodiyo, Allah ya yi masa rahama, shi ma ba’a bar shi a baya ba wajen sukan ‘yan Shi’a da bayanin halinsu da matsayinsu, koda yake a zamaninsa babu su a qasar nan amma yana sane da su da miyagun aqidojinsu. Bayan ya ruwaito maganar Hafiz Ibnu Hajar inda yake cewa: ‚Wanda duk ya kafirta Sahabbai ko ya ce al’umma ta vata, to shi kafiri ne,‛ sai ya ce, ‚Na ce: Haka nan duk wanda ya yi shakkar kafircinsa, shi ma kafiri ne.‛ (Duba littafin Tahaqiqul Isma li Jami’i Xabaqati hazihil Umma na Usmanu Xanfodiyo, 8).
Duba ka gani, mai karatu, da idanun basira yadda Shaihu Mujaddadi ya kafirta mai shakkun kafircin xan Shi’a, za ka fahimci cewa kafircin ‘yan Shi’a yana da kaushi ainun.
119
Daga abubuwan da muka kawo a wannan babi na matuqar qiyayyar Rafilawa ga magabatan wannan al’umma, wanda ya haxa da Sahabbai da Tabi’ai da Tabi’an Tabi’ai da sauran malaman al’umma da limamanta a tsawon zamani, da kuma gargaxi da kashedi da malaman al’umma suka yi dangane da wannan qungiya tun daga kan Sahabbai da imaman Ahlul Baiti har ya zuwa yau, mai karatu zai fahimci matsayin Shi’a a cikin al’umma cewa su wani ciwon daji ne da aka dasa a jikin al’umma da hannun Yahudawa da Majusawa waxanda Musulunci ya buwaye su a fagen fama don haka suka koma yaqarsa ta hanyar munafunci.
Mugun Nufin Rafilawa ga Al’umma
Rafilawa suna qudure mugun nufi ga Musulmi da Musulunci kuma wannan yana bayyana a fili daga abinda yake rubuce a cikin littafansu da abinda ke fitowa daga bakin malamansu. Manufarsu ta qarshe ita ce halaka Ahlus Sunna baki xaya da rushe xakin Ka’aba da Masallacin Annabi a Madina da mayar da alqiblar Musulmi zuwa birnin Kufa. Wannan yana nufin soke
120
Musulunci ke nan gaba xaya da shafe shi don haka suka ce idan Mahadinsu ya bayyana zai yi hukunci irin na iyalin Dawudu, watau Bani Isra’ila.
Mahadin Shi’a zai fara da Larabawa, domin su ne tushen addini, ya gama da su. Muhammad Baqir Almajalisi, xaya daga cikin manyan malaman Rafilawa masu yawan talifi, ya ruwaito cewa idan Mahadinsu ya bayyana zai zubar da jinin Larabawa kuma ya hakaito shi yana cewa, ‚Babu abinda ya rage tsakaninmu da Larabawa sai yanka.‛ (Biharul Anwari na Majalisi, 52/318 da 349).
Dangane da sauran Musulmi Ahalus Sunna waxanda ba Larabawa ba, ‘yan Shi’a suna da fatawa mai qarfi daga imaminsu na shida Abu Abdullahi Ja’afar Alsadiq, kan halaccin jininsu. Wani mai ruwayarsu da ake cewa Dawudu binu Farqad ya ce: Na ce da Abu Abdillahi (A.S) me za ka ce dangane da kisan nasibi (watau Ahalus Sunna)? Sai ya ce, ‚Jininsa halal ne sai dai ina jiye maka tsoro. Idan ka samu iko ka rusa masa gini a ka ko ka nutsar da shi a ruwa don kada a samu shaida, to ka aikata.‛ (Biharul Anwari na Majalisi, 27/231). Da yake sharhi a kan wannan ruwaya, imamin
121
Shi’a na wannan qarni, Ayatullahi Ruhullahi Khumaini ya yi qari kamar haka: ‚Idan ka samu iko ka karvi dukiyarsa, karve ta ka aiko mana da khumusi.‛ (Kashful Asrari fi Tabri’atil A’immatil Axhari na Sayyid Hussain Musawi, 89). Wannan qarin bayani daga Khumaini yana nuna cewa wannan aqida ta ‘yan Shi’a tana nan ba ta sauya ba; abinda kurum yake hana su aiwatar da ita shi ne rashin iko.
Wani abinda yake qara tabbatar da haka shi ne abinda Khumaini ya faxawa Sayyid Hussain Musawi a lokacin da ya ziyarce shi a birnin Teheran, bayan nasarar juyin juya halin Rafilawa na Iran a shekara ta 1979. Musawi ya ce: A wani zama na musamman tare da Imam ya ce mini: ‚Sayyid Hussain, lokaci ya yi na zartar da wasiyar imamai, amincin Allah ya tabbata a gare su. Za mu zubar da jinin nasibawa (Ahlus Sunna), mu karkashe ‘ya’yansu maza, mu raya matansu. Ba za mu bar xaya daga cikinsu ya kuvuta ba daga wannan uquba. Da sannu dukiyoyinsu za su zama kevantattu ga Shi’ar Ahalul Baiti. Kuma za mu shafe Makka da Madina daga doron qasa saboda waxannan birane biyu sun zama mafakar ‘yan Wahhabiya. Kuma lallai ne
122
Karbala, qasar Allah mai tsarki, ta zama ita ce alqiblar mutane a cikin sallah. Za mu tabbatar da burin imamai, aminci ya tabbata a gare su.‛ (Kashful Asrari na Musawi, 91-92).
Kafin mu ci gaba, bari mu qara tunawa mai karatu cewa a koda yaushe Rafilawa suka ruwaito irin wannan tavargaza suka dangana ta ga imamai, ya sani cewa imamai barrantattu ne daga wannan qarya wacce take nuna kafirci da munafinci da qin Allah da Manzonsa da Musulmi baki xaya. Malaman Shi’a jikokin Yahudawa da Majusawa suna fakewa da son imamai da Ahalul Baiti, suna xaukar wannan a matsayin wani mayafi wanda suke lulluve kafircinsu da zindiqancinsu da shi. Amma faxin Khumaini cewa za su rushe Makka da Madina saboda sun zama mafakar ‘yan Wahhabiya, to wannan dalili da ya bayar na rushe Ka’aba qarya ce kawai. Tun kafin a haifi Muhammad xan Abdulwahhab ko a san Wahhabiyanci, Rafilawa suna da aqidar rushe Ka’aba da Masallacin Annabi (SAW) na Madina. Sai dai a nan muna so mu jawo hankalin mai karatu da ya lura cewa qin Wahhabiyanci da ‘yan Wahhabiya yana cikin abubuwan da suka haxa ‘yan Shi’a da ‘yan Xariqa
123
Sufaye waxanda tushensu na bidi’a da vata xaya ne. Nan gaba da yardar Allah za mu tattauna dangantaka tsakanin waxan nan qungiyoyin bidi’a guda biyu a cikin wani babi na musamman mai taken Shi’anci da Sufanci Tagwaye ne.
Wani mugun nufi da ‘yan Shi’a suka daxe da shi a zuci, kuma suke da niyar zartar da shi har gobe, shi ne rushe Masallaci mai Alfarma, watau Xakin Ka’aba, da Masallacin Annabi (SAW) a Madina da kuma sauya alqibla zuwa Karbala. Majalisi ya ruwaito kamar haka: ‚Lallai Mahadi zai rushe Masallaci mai Alfarma har sai ya mayar da shi ga harsashensa. Kuma zai rushe Masallacin Annabi zuwa harsashensa.‛ (Biharul Anwari na Majalisi, 52/338; kuma a duba Kitabul Gaiba na Abu Ja’afar Muhammad binu Hassan Alxusi, 282). Har yau, a wani wurin dabam, Majalisi ya ruwaito kamar haka: ‚Farkon abinda zai fara da shi – yana nufin Mahadi – shi ne ya fitar da waxannan biyun (watau Abubakar da Umar daga kabarinsu) suna xanyu shataf (kamar yanzu aka bunne su) ya watse su a iska, sa’an nan ya rushe Masallacin.‛ (Biharul Anwari, 52/386).
124
Ita Karbala da suke burin mayar da ita sabuwar alqibla bayan rushe Ka’aba wuri ne kusa da birnin Kufa (a yanzu tana qasar Iraqi) inda a nan ne aka kashe Sayyidina Hussaini xan Ali binu Abi Xalib (R.A). A gwargwadon aqidar Shi’a, kasancewar Hussaini ya yi shahada a wannan wuri shi ya ba wurin falala da xaukaka waxanda Rafilawa suka yi ta kambamawa har daga qarshe suka fifita shi a kan garin Makka da Xakin Ka’aba. Daga qarerayin da suka xafama wannan wuri domin su qawata shi ga jahilai, sun ce wai masallacin annabawa ne kuma za’a kawo dutsen Hajarul Aswadu wurin bayan rushe Ka’aba. Sun ruwaito xaya daga imamansu yana huxuba, yana cewa: ‚ Ya ku mutanen Kufa, lallai Allah mai girma da xaukaka ya ba ku abubuwan da bai ba wani ba na falala. Masallacinku shi ne xakin (Annabi) Adamu da (Annabi) Nuhu da (Annabi) Idrisu kuma shi ne masallacin (Annabi) Ibrahimu… Kuma kwanuka ba za su tafi ba sai an kafa (dutsen) Hajarul Aswadu a cikin sa.‛ (Alwafi na Kashani, 1/215).
Girmama Karbala da xaukan ta a matsayin qasa mai tsarki da fifita ta a kan Ka’aba qaryatawa ne qarara
125
ga Alqur’ani ma girma. Allah Maxaukaki yana cewa: ‚Kuma lalle ne, Xaki na farko da aka aza domin mutane, haqiqa, shi ne wanda ke Bakka mai albarka kuma shiriya ga talikai.‛ (Suratu Ali Imrana: 96).
Kuma masallacin Ibrahim wanda ya gina da umarnin Allah shi ne Xakin Ka’aba, kamar yadda Allah ya bayyana: ‚Kuma a lokacin da muka iyakance wa Ibrahim wurin Dakin (muka ce masa), ‚Kada ka haxa kome da ni ga bauta, kuma ka tsarkake Xakina, domin masu xawafi da masu tsayuwa da masu ruku’u da masu sujada. Kuma ka yi yekuwa ga mutane da wajabcin Hajji, su je maka suna masu tafiya da qafafu da kuma a kan kowane maxankwarin raqumi masu zuwa daga kowane rango mai zurfi.‛ (Suratul Hajji: 26-27). Kuma Ubangiji Maxaukaki ya ce, ‚Kuma a lokacin da Ibrahim yake xaukaka harsashin gini ga Xakin, da Isma’ila (suna cewa), ‚Ya Ubangijinmu, ka karva daga gare mu, lalle ne kai, kai ne mai ji, mai sani.‛ (Suratul Baqara: 127). Kuma dangane da alqibla, yana cewa, ‚Lalle ne, muna ganin jujjuyawar fuskarka a cikin sama. To lalle ne, mu juyar da kai ga Alqibla wadda kake yarda da ita. Sai ka juyar da fuskarka wajen Masallaci Tsararre.‛ (Suratul
126
Baqara: 144). Watau Masallaci mai Alfarma, Xakin Ka’aba. Kuma ya ce, ‚Kuma daga inda ka fita, to, ka juyar da fuskarka a wajen Masallaci Tsararre, kuma inda kuke duka, to, ku juyar da fuskokinku a wajensa.‛ (Baqara: 150).
Wannan shi ne abinda Alqur’ani mai tsarki yake faxi dangane da qasa mai tsarki da kuma alqiblar Musulmi wacce ba ta canjawa kuma ba ta sauyawa har abada. Daga wannan kuma babu wata qasa mai tsarki sai Baitil Maqadis wanda Allah yake cewa dangane da shi: ‚Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar dare da bawansa da dare, daga Masallaci mai Alfarma zuwa ga Masallaci mafi nisa, wanda muka sanya albarka a gefensa.‛ (Suratul Isra:1). Sai fa Masallacin Annabi (SAW) na Madina. Waxan nan su ne masallatai guda uku masu alfarma waxanda ambatonsu ya zo a cikin hadisin da Manzo (SAW) yake cewa: ‚Ba’a xaura sirada (domin tafiya) sai zuwa masallatai uku kawai: Masallaci mai Alfarma, da Masallaci Mafi Nisa, da Masallacina wannan.‛ (Bukhari da Muslim).
Don haka Karbala ba ta da wata alfarma kuma ba ta da tsarki, sa’annan babu bambanci tsakaninta da ko
127
wace irin gama-garin qasa a duniya. Muna roqon Allah ya buxe basirarmu tare da Shi’awa waxanda ba su yi nisa ba. Ya bayyana mana gaskiya ya ba mu ikon bin ta. Waxanda suka yi nisa kuma, Allah ya isar wa Musulunci sharrinsu.
Har yau, wani mugun nufi da Rafilawa suka daxe da shi a zuci kuma suke da niyar aiwatar da shi, shi ne kashe Musulmi Ahalus Sunna mafi munin kisa ta yadda ba abinda zai rage a cikinsu sai kaxan. Qasurgumin malamin ‘yan Shi’a wanda suke yi wa laqabi da Shaikhul Xa’ifa, watau Shaihin Qungiya, mai suna Abu Ja’afar Muhammad binu Hassan Alxusi, ya ce, ‚Wannan al’amari (yana nufin mulkin Rafilawa) ba zai tabbata ba sai ushuri tara na mutane sun tafi.‛ Duba ka gani, malam mai karatu, wannan qeta da mugun nufi da baqin alkaba’i da yake a zukatan malaman Shi’a da manyan mabiyansu. Mulkinsu ba zai tabbata ba sai sun kashe ushuri tara na mutane, watau tis’in bisa xari ke nan (90%). Ruwayar Majalisi ta fi ban tsoro da kaxa zuciya da tsuma jiki. Ga yadda ya hakaito daga imaminsu na shida, Abu Abdullahi, ya ce, ‚Da mutane sun san abinda Mahadi zai yi idan ya bayyana da mafi yawansu sun yi
128
fata kada su gan shi saboda yawan mutane da zai kashe… Har mutane da yawa za su riqa cewa: Wannan ba ya cikin iyalin Muhammad; da yana cikin iyalin Muhammad da ya yi jin qai.‛ (Biharul Anwari na Majalisi, 52/303; akwai ruwayar kuma a cikin Kitabul Gaiba na Alxusi, 135).
Idan mai karatu yana so ya san su wane ne waxannan mutanen waxanda wannan shu’umin Mahadi, Mahadin Yahudawa da Majusawa, zai kashe, to sai ya koma ga maganar Ayatullahi Khumaini da muka naqalto a baya kaxan inda ya sarraha da cewa Ahalus Sunna suke nufi. Muna fata Allah ya raba mu da ganin wannan baqin Mahadi mai baqar aniya da mugunyar manufa.
Har ila yau, wani mugun nufi da ‘yan Shi’a suka daxe da shi a zuci kuma suke da niyar tabbatar da shi a aikace shi ne sauya addinin Musulunci da wani addinin sabo da sauya Shari’arsa da wata shari’a sabuwa da kuma sauya littafinsa da wani littafin sabo. Majalisi ya ambata a cikin littafinsa kamar haka: ‚Mahadi zai bayyana da al’amari sabo, da littafi sabo, da hukunci sabo.‛ (Biharul Anwari, 52/354). Idan kana da wani kokwanto dangane da wannan sabon al’amari, bari ka ji
129
ruwayar Kulaini, Bukharin ‘yan Shi’a, daga Abu Abdullahi, imamin Rafilawa na shida, ya ce: ‚Idan Mahadin iyalin Muhammadu ya bayyana, zai yi hukunci da hukuncin Dawudu da Sulaimanu kuma ba zai tambayi shaida ba.‛ (Usulul Kafi na Kulaini, 1/397). E, ba zai tambayi shaida ba; saboda tambayar shaida yana daga cikin sifofin Musulmi, shi kuwa wannan Mahadin Bani Isra’ila ne ya yafa mayafin iyalin Muhammadu (SAW), Ahlul Baiti, domin vad da bami.
A cikin abinda muka gabatar a wannan babi na mugun nufin Rafilawa ga addinin Musulunci da Musulmi akwai faxakarwa ga dukkan wanda Allah ya buxe basirarsa domin ya fahimci irin sharrin dake tattare da tafarkin Shi’anci da kuma haxarin dake fuskantar dukkan jama’ar musulmin da Rafilanci ya yaxu a cikinsu. Ga Allah muke kai koken lamarinmu.
Baqin Tarihin ‘Yan Shi’a
Rafilawa suna da baqin tarihi wanda yake cike da cin amanar Musulmi da yaudarar su da munafintar su da zubar da jininsu, domin su, kamar yadda Ibnu Taimiya
130
ya ce, ‚A koda yaushe suna neman taimako da kafirai da fajirai wajen biyan buqatunsu kamar yadda suke taimakon kafirai da fajirai wajen biyan nasu buqatun.‛ (Minhajus Sunnah, 2/195). Wannan shi ne halin Rafilawa a tsawon tarihinsu, a ko wane zamani, kuma a ko wane wuri. A nan Nijeriya, an ruwaito madugunsu, Ibrahim Yaqub Alzakzaki, yana faxawa Kirista: ‚Ba da ku muke faxa ba,‛ yana nufin da Musulmi suke yaqi waxanda yake kira xagutai kamar yadda malamansa da magabatansa suka kira Abubakar da Umar (R.A). Da za mu tafi muna buga misalai a kan miyagun ayyukan ‘yan Shi’a waxanda suke nuna qiyayyarsu ga Al’ummar Muhammadu (SAW) da sai littafin ya yi tsawo ainun. Amma za mu isu da misalai uku kawai.
A wajejen qarshen daular Abbasiya a qarni na bakwai bayan hijira, an yi wani sarki Mushriki mai suna Holako, sarkin Tattar. Wannan sarki ya yaqi daular Musulmi mai faxi, ya riqa cin gari bayan gari. Duk garin da ya ci yana rushe shi baki xaya, ya kashe mazauna garin, ya qone gidaje da gonaki da dabbobi, ba ya rage kome. Saboda tsananin varnar waxannan kafirai, har wasu mutane a zamanin sun zaci ko yajuju da majuju ne
131
suka bayyana. Amma duk da haka, babban birnin daular Musulmi, watau Bagdada, tana yiwa wannan sarkin kwarjini saboda girmanta da yawan mutanen dake cikinta da kuma qarfin sojan dake tsaron ta. A wannan lokaci, duk duniya babu birni kamar Bagdada. Don haka da ya iso qasar Farisa sai ya tsaya yana tararrabi, ya kawo wa Bagdada hari ko a’a.
A wannan lokaci Sarkin Musulmi shi ne Musta’asim, Khalifa na qarshe a daular Abbasiya. Babban wazirinsa mai suna Muhammad binu Ahmad binu Alqami xan Shi’a ne amma masu mulki sai suka yi sakaci da shi tun yana saurayi, ya yi ta hawa muqamai har ya kai matsayin waziri. Saboda iya munafinci da amfani da taqiya, Binu Alqami ya samu amincewar kowa a wannan daula. Amma duk tsawon shekaru, shi dama yake jira ta rusa daular. Sai zuwan Holako da rundunarsa ya ba shi wannan dama.
Binu Alqami ya aikewa Holako da bayanan sirri a voye, ya yi bayanin raunin daular kuma ya yi alqawarin taimakon maharan da sharaxin cewa za su kafa daular Shi’a bayan sun kawar da Khilafar Abbasiya. Lokacin da rundunar Tattar suka iso Bagdada suka kafa sansani a
132
bayan gari, Khalifa Musta’asim ya tsorata ainun, amma sai wazirinsa ya kwantar masa da hankali kuma ya nemi izini ya fita zuwa sansanin abokan gaba domin neman sulhu da su. Bayan ya je ya qara tabbatar da yarjejeniyarsa ta sirri da Holako, sai ya dawowa sarkin Musulmi da wata qarya. Ya ce Holako ya yi farin ciki da zuwansa, ya amince da sulhu da barin yaqi kuma harma yana son ya aurar da xiyarsa ga xan sarkin Musulmi, Yarima mai jiran gado Abubakar. Sarki ya yi murna, aka sa ranar da za a je xaurin aure kuma daula duka ta fita zuwa sansanin Holako domin yin shagali.
Babu wanda aka bari a baya, Sarki da Yarima da manyan wazirai da kwamandojin soja da malamai da limamai da alqalai da attajirai da duk wani mai faxi a ji sun fita baki xaya. Isarsu sansanin Holako ke da wuya da ma ya shirya. Sai ya sa aka kange mafita duka aka yanke shugabannin nan baki xaya, sai abokinsu waziri Binu Alqami kawai ya tsira. A yammaci guda sai Bagdada, da sauran al’umma, suka zama jiki babu kai. Su kuwa yajuju da majuju suka shiga aiki. Kwana arba’in suna kisa, suna qone gidaje da kasuwanni da masallatai da makarantu da xakunan karatu (laburare) sai
133
da kogin Dajla ya rikixe ya zama ja saboda jini. Suka kame mata da yara, suka yi ta zina da mata sharifai Hashimawa a cikin masallatai. Wannan shi ya kawo karshen daular Abbasiya wacce ta yi shugabancin duniya xaruruwan shekaru kuma daga nan Musulmi ba su sake samun wannan matsayi ba na shugabancin duniya. Mutum miliyan xaya da dubu xari takwas (1,800,000) ne suka rasa rayukansu a wannan kisan kiyashi wanda tarihi bai tava ganin irinsa ba. (Domin garin wannan qissar, sai a duba Albidaya wal Nihaya na Ibnu Kathir, 9/154; da Almuntaqa min Minhajil I’itidal na Muhammad binu Usman Alzahabi, 298).
Marubucin tarihi xan Shi’a mai suna Mirza Muhammad Baqir Khunasari, ya kawo wannan qissa a cikin littafinsa, Raulatul Jannati, yana yabon Waziri Binu Alqami a kan wannan xanyen aiki da ya yi, kuma ya ce waxanda suka rasa rayukansu duka suna cikin wutar Jahannama. (Duba Raulatul Jannati na Khunasari, 578). Ayatullahi Khumaini ma ya yaba wa wannan xan ta’adda, maci amana, kuma ya xauki wannan mummunan aiki nasa a matsayin babbar hidima ga Musulunci. Don haka ba ya ambaton sa sai ya ce:
134
Raliyallahu Anhu, watau Allah ya yarda da shi! (Duba Kashful Asrari na Sayyid Hussain Musawi, 90). Wannan yana nuna cewa qissar ba qage aka yi wa ‘yan Shi’a ba; su ma sun san da ita, sun yi na’am da ita, kuma sun tabbatar da ita cikin littafansu.
Misali na biyu da za mu bayar shi ne abinda ya faru, kuma yake ci gaba da faruwa, a ‘yan shekarun nan a duniyar Musulmi. Lokacin da ‘yan Taliban suka kafa gwamnatinsu ta Musulunci a qasar Afganistan, Jumhuriyar Islama (!) ta Iran, wacce take ta haxa iyaka da Afganistan, maimakon ta taimakawa wannan sabuwar gwamnati ta ‘yan Taliban sai ta sa qafar wando xaya da su. Abubuwa sun kai lokacin da Iran ta girke dubunnan sojoji a kan iyakarta da Afganistan, tana barazanar mamaye qasar. Babu irin zagon qasa da qafar ungulu da kutunguilar siyasa wacce masu mulkin Iran Rafilawa ba su yiwa ‘yan Taliban ba saboda su Taliban masu bin tafarkin Sunna ne.
Haka al’amura suka tafi tsakanin waxan nan maqwaftan qasashe biyu har lokacin da aka kai hare-haren 11 ga watau Satumba, 2001 kuma daga bisani qasar Amurka ta kai hari a kan Afganistan. Sai Iran ta
135
wasa wuqar yankan qauna, ta shirya domin huce fushi a kan ‘yan Taliban da ‘yan Qungiyar Alqa’ida waxanda laifinsu kawai shi ne cewa su Ahalus Sunna ne kuma sun kafa gwamnatin Musulunci kamar yadda Iran ita ma take riya cewa ta kafa. A yayin da yaqin zalunci wanda kafira, algunguma kuma annamimiya qasar Amurka ta kai wa Musulmin Afganistan ya yi tsanani, sai masu mulkin Iran suka bi sahun munafukai irin su Musharraf wanda ba shi da sharafi da sauran shugabannin qasashen Musulmi waxanda suka mara ma George Bush la’ananne baya a kan yaqinsa da Musulunci wanda ya kira yaqi da ta’addanci. Xaruruwan ‘yan Taliban da ‘yan Alqa’ida waxanda suka haura iyaka zuwa cikin Iran don neman mafaka, sai mahukuntan qasar suka kame su suka garqame a gidan yari. Daga baya sun miqa yawancinsu ga Amurka, wasu kuma har yanzu suna tsare a gidajen jarun na Iran, ana ajiye da su a matsayin takardun karta na siyasar duniya inda mai riqe da Sarki da Mata da Rayya yake cinyewa duka, kuma a biya shi buwa!
Abinda muka ambata a nan abu ne sananne wanda duk mai kula da al’amuran yau da kullum ya san shi. A cikin watan Yuli, 2004 gidan talabijin na
136
Aljazeera ya yi hira da wasu da aka sako daga gidan maza na qare-kukanka, Guantanamo Bay, inda suka bayyana cewa hukumomin Iran ne suka cafke su suka miqa su ga Amurka.
Misali na uku a nan gida Nijeriya za mu ba da shi. Kamar yadda za mu gani a nan gaba a cikin wannan littafi, in Allah ya yarda, yawancin ‘yan Shi’ar Nijeriya suna xaukar wanda bai yarda da Zakzaki a matsayin shugaba, ya yi masa mubaya’a ba, cewa shi ba Musulmi ba ne. Wannan kuma ya dace da koyarwar tafarkin Shi’anci wanda yake xaukar duk wanda ba xan Shi’a ba a matsayin ba Musulmi ba ne, kuma a kan wannan Rafilawan Nijeriya suke ma’amala da sauran Musulmi Ahalus Sunna. Don haka inda duk suke da qarfi za ka ga a koda yaushe suna ta da hankalin Musulmi, ta hanyar taso da fitintinu waxanda a wani yayi sukan kai ga zubar da jini. Akwai misalai da dama a birnin Zaria, wanda shi ne kamar cibiyarsu, inda suka kashe mutane xai-xaiku waxanda laifinsu kawai shi ne suna koyawa mutane Sunnar Annabi kuma suna gargaxi ga barin bin bidi’o’i na Shi’a da wasunsu, kamar yadda suka kashe
137
Malam Ayuba, wani mai koyar da matan aure a Tudun Wada, Kaduna.
‘Yan Shi’ar Nijeriya suna da al’adar barazana ga masallatai da makarantu, musamman inda ake koyar da Sunnar Annabi (SAW), kamar yadda suka yi barazana ga limamin Masallacin Low Cost, Zaria wanda yake koyar da Sahihul Bukhari, da limamin Masallacin Babban Dodo ‚A‛ a Zaria wanda yake koyar da Sahih Muslim, da ladanin Masallacin Babban Dodo ‚B‛ a Zaria wanda yake yawan ba da nasiha bayan sallah. Duka waxannan malamai ‘yan Shi’a sun yi barazanar xaukar rayukansu.
Har yau, Rafilawan Nijeriya suna da al’adar qwace masallatan mutane su mayar da su nasu qarfi da yaji. Sai mutane sun gina masallacinsu, idan suka raina musu qura, sai kawai su xebo makamai su shiga masallacin su kore kowa, su gaje duk abinda suka samu a cikin masallacin, kamar yadda suka yi a Sakkwato, suka so su qwace wani sabon masallacin Jumma’a da aka gina, Masallacin Sarkin Musulmi Hassan Dan Mu’azu. Sai da aka yi ta fitina wata da watanni sa’an nan suka haqura. Wannan shi ne halin ‘yan Shi’a a duk inda suka samu qarfi, suka miqe qafa. Kuma wannan shi ya sa
138
muke ganin cewa yaxuwar tafarkin Rafilawa a qasar nan matsalar tsaro ce kamar yadda take matsalar addini.
139
Babi Na Huxu
Fiqihun ‘Yan Shi’a
Kamar yadda Rafilawa suka sha bamban da sauran Musulmi a aqidojinsu haka nan kuma sun sha bamban a yawancin hukunce-hukuncen Fiqihu da mas’alolin ibada da ma’amala.
Akwai irin waxannan bambance-bambance da dama amma zan taqaice a wannan babin. Ga misali, a wajen alwala ba sa wanke qafafu sai dai su jiqa hannayensu su shafe su. Suna jinkirta sallar magariba har sai taurari sun fito. A wajen azumin Ramadan kuwa, ba sa damuwa da ganin wata; da qidayar kwanaki suke sanin shigar wata ko fitarsa. Rafilawa suna haramta cin yankan Ahlul Kitabi, watau Yahudu da Kirista alhali
140
kuwa Allah ya halasta shi da nassin Alqur’ani (Duba Suratul Ma’ida :5). Wasu ‘yan Shi’a suna haramta cin naman raqumi wai saboda Innar Muminai Aisha (R.A) ta hau raqumi ta yaqi Ali (R.A). Har yau, suna haramta cin wani nau’in kifi na musamman. Rafilawa suna halasta bautar kabari da ziyarorin shirka da bidi’a. A vangaren ma’amala kuma, Rafilawa suna halasta auren mace tare da goggonta a lokaci guda, da saduwa da mace ta baya da kuma auren wucin gadi.
Wannan na qarshen, watau auren wucin gadi ko kuma mutu’a kamar yadda suke kiran sa, zan xan faxaxa bayani a kansa kaxan domin in tabbatarwa da mai karatu cewa tafarkin Rafilawa tafarki ne wanda maqiyan Musulunci suka qago shi domin rusa addinin Musulunci da al’ummar Musulmi.
Mutu’a: Auren Wucin Gadi
Mutu’a ko kuma auren wucin gadi, watau auren da ba na dun-dun-dun ba, ma’anarsa shi ne namiji ya qulla jinga da mace cewa zai sadu da ita sau xaya ko sau biyu ko sau uku, ko kuma na tsawon awa xaya ko kwana
141
uku ko wata bakwai ko shekara kaza, a kan kuxi kaza ko ladan abu kaza.
Auren mutu’a yana daga cikin aurace-auracen Jahiliya kuma an yi aiki da shi a farkon Musulunci kana daga bisani aka haramta shi. An karvo ruwaya daga Ali binu Ali Xalib (R.A), cewa ‚Manzon Allah (SAW) ya hana auren mutu’a da cin naman jakin gida a lokacin (yaqin) Khaibar.‛ (Bukhari da Muslim).
Amma ‘yan Shi’a sun ci gaba da halasta mutu’a kuma sun qago ruwayoyin qarya waxanda suka nuna falalarta da xumbin ladan wanda ya yi ta da kuma darajarsa a aljanna. Babu shakka sun yi haka domin su vata al’ummar Musulmi ta hanyar yaxa lalata da varna da alfasha a tsakaninsu kuma don su jawo hankalin jahilai, musamman matasa, zuwa ga tafarkinsu.
Falalarta
Akwai xaruruwan ruwayoyi a cikin littafan Rafilawa da suke izna da su waxanda suke nuna falalar auren wucin gadi. Ya zo a cikin littafin Man La Yahduruhul Faqih, xaya daga littafansu guda huxu
142
mafiya inganci, sun laqa ma Ja’afar Sadiq, imaminsu na shida, cewa ya ce: ‚Lallai mutu’a addinina ce kuma addinin iyayena. Wanda ya yi aiki da ita ya yi aiki da addininmu kuma wanda ya yi inkarinta ya yi inkarin addininmu, kuma ya yi riqo da wanin addininmu.‛ (Man La Yahduruhul Faqih na Ibnu Babawaihi Alqummi, 3/366). Ya zo a wannan littafi har yau, sun dangana ga Annabi (SAW) cewa wai ya ce: ‚Wanda ya yi mutu’a sau xaya zai amince fushin Allah, wanda ya yi mutu’a sau biyu za’a tashe shi tare da zavavvun bayi, wanda ya yi mutu’a sau uku zai haxa kafaxa da ni a aljanna.‛ (Duba littafin Alqummi na bisa, juzu’i guda shafi guda). A wata ruwayar mai kama da wannan, sun qaga ma Manzon Allah (SAW) cewa wai ya ce: ‚Wanda ya yi mutu’a sau xaya za ta zama (gare shi) kamar darajar Hussaini (A.S); wanda ya yi mutu’a sau biyu darajarsa kamar darajar Hassan (A.S) ce; wanda ya yi mutu’a sau uku darajarsa za ta kasance kamar darajar Ali (A.S); kuma wanda ya yi mutu’a sau huxu darajarsa kamar daraja ta ce.‛ (Duba Tafsirin Minhajus Sadiqin na Sayyid Fatahallah Kashani, 2/493). Da yake mata suna da qarin kunya a kan maza, wataqila za su buqaci a qara
143
xan ingiza su kaxan kafin su faxa ramin alfasha. Don haka Alqummi, wanda suke yiwa laqabi da Alsaduq (mai yawan gaskiya!) ya kitsa musu tasu ruwaya ta musamman. Ya ce, ‚Lokacin da aka yi isra’i da Annabi (SAW) zuwa sama, ya ce: Jibrilu ya ruske ni ya ce: Ya Muhammad, Allah mai girma da xaukaka yana cewa: Lallai ni na gafartawa masu yin mutu’a daga matan al’ummarka.‛ ( Man La Yahduruhul Faqih, 3/463).
Ladanta
Abinda ya gabata dangane da falala da xaukakar darajar mai yin auren mutu’a ne, amma dangane xa dumbin ladan da zai samu, bari mu saurari Alsaduq ya qara shara mana ita. Ya ce: an tambayi Abu Abdullahi, watau imamin Shi’a na shida a riyawarsu: Shin mai mutu’a yana da lada? Sai ya ce, ‚In yana nufin yardar Allah da haka (mutu’ar) ba zai yi magana da ita ba (matar) kalma guda face Allah ya rubuta masa lada da ita (kalmar), kuma idan ya kusance ta sai Allah ya gafartar masa zunubi, kuma idan ya yi wanka Allah zai gafarta
144
masa da gwargwadon ruwan da ya shuxe a kan gashinsa.‛ (Man la Yahduruhul Faqih, 3/366).
Gargaxi ga Wanda Ya Qi Yin Ta
Bayan bayanin falala da garavasar mutu’a, in da akwai wani mai taurin kai wanda ya qi xibar wannan garavasa, to sai a yi masa gargaxi kuma a tsoratar da shi. Wannan shi ne abinda Malam Kashani ya yi yayin da ya ruwaito daga Annabi (SAW) cewa wai ya ce: ‚Wanda ya fita daga duniya bai yi mutu’a ba zai zo ranar Alqiyama yana yankakke (watau naqisin halitta).‛ (Tafsirin Minhajus Sadiqin na Kashani, 2/489). A harshen Shari’a irin wannan gargaxi ana yin sa ne ga wanda ya aikata kaba’ira, watau babban zunubi, kamar shaidar zur da tserewa a wajen yaqi da sava ma iyaye. Saboda haka za mu fahimta a nan cewa, qin yin mutu’a dai – dai yake da aikata kaba’ira. Kuma wannan babu mamaki idan muka dubi waccan ruwaya da ta gabata wacce take cewa, ‚Wanda ya yi inkarinta ya yi inkarin addininmu.‛
145
Watau ke nan mutu’a ita ce addinin ‘yan Shi’a don haka Sayyid Hussain Almusawi, wanda a da xan Shi’a ne kuma Allah ya shirye shi ya tuba, yake cewa manyan malaman Rafilawa na wannan zamani kamar su Sayyid Assadar da Alburujardi da Asshirazi da Alqazwini da Alxibaxiba’i da Abu Harith Alyasiri da kuma uban tafiya Imam (!) Khumaini duka suna yin mutu’a, kuma suna yin ta da yawa ba kaxan ba. (Duba littafinsa Kashful Asrari Fi Tabri’atil A’immatil Axhari, 34-35). Haka nan, Rafilawan Nijeriya suma suna yin mutu’a ainun kuma da ita ne suke jawo hankalin jahilai, musamman matasa maza da mata, zuwa ga wannan tafarki nasu mai nufin rushe durakun al’umma.
Xaurin Auren Mutu’a
Domin ka san cewa mutu’a qofar zina ce kawai aka buxewa mutane, bari ka ji yadda ake xaura auren ta. Auren mutu’a ba ya buqatar wakilin ‚ango‛ ko walin ‚amarya‛, ba ya buqatar shaidu; ba’a ma buqatar kowa ya sani kuma bai buqatar wani vata lokaci. Da zarar an haxu sai a yi a gama! Sun ruwaito cewa wani ya tambayi
146
Ja’afar Sadiq: ‚Ya zan ce da ita idan na kaxaita da ita? Sai ya ce: Ka ce: Ina auren ki auren mutu’a a bisa littafin Allah da Sunnar Annabinsa; ba kya gado, ba’a gadon ki; kwana kaza kaza, ko shekara kaza kaza, a kan dirhami kaza kaza, sai ka ambata mata ladan da kuka yi yarjejeniya a kai, kaxan ne ko da yawa.‛ (Duba Furu’ul Kafi na Kulaini 5/455). Ina son mai karatu ya lura da yadda mai tambayar ya yi tambayarsa: ‚Ya zan ce da ita idan na kaxaita da ita?‛ Watau sai an kaxaita ake cinikin!
Sadaki ko Lada?
Abin sha’awa ne yadda malaman Shi’a ba sa kiran sadakin auren mutu’a da sunan sadaki, sai dai su ce ujura, watau lada. Duk littafan da na duba ba inda suka kira shi da sunan sadaki. Wataqila a cikin wannan akwai matashiya, amma fa ga mai hankali!
Bari mu kira shi yadda suka kira abinsu: Mene ne ladan auren mutu’a? Suka ce an tambayi Abu Ja’afar ya ce, ‚Dirhami zuwa sama.‛ (Furu’ul Kafi, 5/457). Xansa kuwa, Ja’afar, ya ce, ‚Tafi xaya na gari ko tafi xaya na
147
dabino.‛ (Furu’ul Kafi, 5/457). Lallai Rafilawa sun san darajar mata! Me zai hana irin Majusawa, dangin Yahudawa su mutunta mata!
Da Wa Ake Mutu’a?
Shin mutu’a sai da Musulma? A’a sam! A cikin daren ‘yan Shi’a ko kyankyaso ma nama ne. Don haka suka rawaito daga imaminsu na shida Ja’afar Sadiq (Allah ya isar masa qarerayin da aka laqa masa) wai ya ce, ‚Babu laifi mutum ya yi mutu’a da Bamajusiya.‛ (Duba Tahzibul Ahkam na Alxusi, 7/256). Kuma ana yi da Banasariya (Kirista) da Bayahudiya, kamar yadda suka ruwaito daga imaminsu na takwas, Abul Hassan Ali binu Musa Rida, (Al’istibsar na Alxusi, 3/144). Haka nan ana yi da karuwa domin, kamar yadda suka ce, sai ya hana ta karuwanci! (Duba Tahazibul Ahkam, 7/253; kuma a duba Tahrirul Wasila na Khumaini, 292).
Ana Yi da Matar Aure!
Dangane da yin mutu’a da matar aure (matar wani) akwai ruwayoyi guda biyu masu ban mamaki
148
waxanda ya kamata mai karatu ya gan su da idanunsa. Ta farko an karvo daga Falalu Maulan Muhammad binu Rashid, ya ce da Ja’afar Sadiq: ‚Ni na auri wata mace auren mutu’a sai ya xarsu a raina cewa tana da miji. Da na bincika sai na samu ashe tana da miji. Sai Ja’afar ya ce: Don me ka bincika?!‛ (Tahzibul Ahkami, 7/253). A wata ruwayar, sai ya ce, ‚Wannan (binciken) ba ya kanka. Abinda yake kanka kawai shi ne ka gaskata ta dangane da kanta.‛ (Furu’ul Kafi, 5/462).
Ruwaya ta biyu kuwa ita ma Kulaini da kansa (watau Bukharin mutanen) shi ne ya ruwaito ta. An karvo daga Abanu binu Taglub ya ce: ‚Na ce da Abu Abdullahi (watau Ja’afar Sadiq) ni ina tafiya kan hanya sai in ga mace kyakkyawa kuma ba ni da tabbas ko tana da miji ko karuwa ce. Sai ya ce: Wannan (binciken) ba ya kanka. Abinda yake kanka kawai shi ne ka gaskata ta dangane da kanta.‛ (Furu’ul Kafi, 5/462).
Watau babu ruwan xan Shi’a idan ta motsa masa; ko matar wa yana kamawa. Shin muna iya cewa waxanda suke zaune tare da Rafilawa suna cikin hatsari? Amma ba wannan ne kawai hatsarin ba; ga wanda ya fi shi.
149
Ana Yi da Qaramar Yarinya!
Ana yin mutu’a da qaramar yarinya wacce ta kai shekara goma. An tambayi Abu Abdullahi, ‚Ko mutum na iya yin mutu’a da yarinya qarama? Sai ya ce: E, sai dai idan qarama ce ainun ta yadda ana iya yaudararta. Aka ce: Nawa ne idan ta kai ba’a yaudararta? Ya ce: Shekara goma.‛ (Furu’ul Kafi, 5/463; da Tahzibul Ahkami na Alxusi, 7/255).
Imam Khumaini, shugaban Rafilawan duniya na wannan zamani, ya yi wani xan ijitihadi a nan. Ya ce qaramar yarinya da jaririya duka ana iya yin mutu’a da su amma ba da haqiqanin saduwa ba, sai dai da sumbata da runguma da kuma abinda ya kira cinyantaka, watau mutum ya sa zakarinsa a tsakanin cinyoyinta. Sai mai karatu ya gafarce ni saboda ruwaito wannan xanyar magana, maras daxin ji, amma haka Imamin ya faxi, kuma haka almajirinsa, Sayyid Hussain Almusawi, ya ruwaito daga gare shi. (A duba Tahrirul Wasila na Khumaini, 2/241; da Kashful Asrari na Musawi, 37).
150
Wannan ijtihadi na Imam Khumaini ba a ilmance kawai ya tsaya ba; a’a ya aiwatar da shi a aikace. Sayyid Hussaini Almusawi ya ba da labarin mutu’a da Khumaini ya yi da wata yarinya mai shekara huxu ko biyar a duniya, a lokacin da yake zaman gudun hijira a qasar Iraqi kafin juyin juya halin da ya shugabanta a Iran, a shekara ta 1979. Mai son ganin wannan labari filla –filla, sai ya duba Kashful Asrari na Almusawi, shafi na 35-37.
Ba wani abu ya sa na bi diddigin wannan mas’ala ba sai don mai karatu ya san cewa mutanen da gaske suke. Allah ya yi mana Alam Nasharaha!.
Mai Mutu’a, Matanka Nawa?
Amsa ta gaskiya, tsakani da Allah, ita ce: Ba iyaka! Rafilawa sun ruwaito daga imaminsu na biyar, Abu Ja’afar, ya ce: ‚Mutu’a ba da mata huxu ba ne kawai; domin ita (mace mai mutu’a) ba’a sakin ta kuma ba ta gado, ba’a gadon ta. Ita mai jinga ce kawai.‛ (Al’istibsar na Alxusi, 3/147). Har yau, sun ruwaito daga imaminsu na shida, Abu Abdillahi, cewa an tambaye shi dangane da mutu’a: Ana iyakance ta da
151
mata hudu? Sai ya ce, ‚Ka auri dubu; su ‘yan jinga ne kawai.‛ (Al’istibsar, 3/147; da Tahzibul Ahkami, 7/259).
Aron Farji
Imaman Shi’a da manyan malamansu sun halasta aron farji. Sayyid Hussain Musawi ya yi bayanin ma’anar aron farji kamar haka: ‚Aron farji ma’anarsa shi ne mutum ya bayar da matarsa ko baiwarsa ga wani mutum dabam sai ya halasta gare shi ya ji daxi da ita ko kuma ya yi duk abinda ya ga dama da ita. Idan mutum ya yi nufin tafiya sai ya bar matarsa a wajen maqwafcinsa, ko abokinsa, ko kuma duk mutumin da ya zava, sai ya halasta a gare shi ya yi abinda ya ga dama da ita a tsawon tafiyar mijinta.‛ (Kashful Asrari, 46-47).
Don halasta wannan varna, malaman Shi’a suna dangana ruwayoyi ga imamansu bisa qarya. Daga cikin irin waxan nan ruwayoyi, akwai abinda suka dangana ga Abu Abdulalhi. Alxusi ya karvo daga Abul Hassan Axxari’i, ya ce: ‚Na tambayi Abu Abdillahi (A.S) dangane da aron farji, sai ya ce: Babu laifi.‛
152
(Al’istibasar na Alxusi, 3/141). Har yau, Alxusi ya karvo daga Zuraratu, ya ce: ‚Na tambayi Abu Ja’afar (A.S) dangane da mutum ya halasta ma xan uwansa farjin baiwarsa. Sai ya ce: Babu laifi; abinda ya halasta masa daga gare ta ya halasta gare shi.‛ (Al’istibsar, 3/136). Babban malamin Hadisi (!) a wurin Rafilawa, Bukharinsu, watau Kulaini shi ma ba’a bar shi a baya ba. Ya karvo daga Muhammad binu Mudarib, ya ce: ‚Abu Abdullahi (A.S) ya ce mini: ‚Ya kai Muahammad, riqi wanan baiwa ta yi maka hidima kuma ka shafe ta (ka sadu da ita). Idan za ka tafi, sai ka komo mana da ita.‛ (Furu’ul Kafi na Kulaini, 2/200).
Duba ka gani xan uwa mai karatu, Allah ya tsarshe ni tare da kai daga sharrin ‘yan Shi’a da vatansu, yadda Rafilawa suka kai matuqa wajen qoqarin yaxa lalata da alfasha a tsakanin jama’a ta hanyar halasta zina da qira qarya a dangana ta ga zavavvun bayin Allah. Wannan ya sa Imam Muhammad binu Abdulwahhab yake cewa dangane da su: ‚To waxannan ‘yan Shi’a sun fice daga Sunna, kai sun ma fice daga Musulunci xungurum. Sun afka cikin zina, sun buxewa kansu qofofin zina a farji da dubura. Wa suka fi su cancanta su
153
zama ‘ya’yan zina?!‛ (Al’intisar Lil Sahbi Wal Ali na Ibrahim binu Amir Alruhali, 149).
154
Babi Na Biyar
155
Yaxuwar Shi’a a Nijeriya
Asalin yaxuwar Shi’a a Nijeria ya fara a tsakanin matasa, yawanci ‘yan makaranta, masu aikin yaxa addinin Musulunci waxanda aka san su da sunan ‘Yan Uwa Musulmi. Wannan suna fassara ce kai tsaye ta sunan wata Qungiya, Alikhwanul Muslimun, wacce Imam Hassan Albanna ya kafa a qasar Masar a cikin shekarun 1930. Babbar manufar qungiyar shi ne mayar da Musulmi zuwa ga hukunce – hukuncen Musulunci a kafatanin fagagen rayuwarsu wanda ya haxa da fagen siyasa, tattalin arziqi, tarbiya da zamantakewa da kuma dangantakarsu da waxanda ba Musulmi ba. Qungiyar ta yaxu a yawancin qasashen Musulmi ciki har da Nijeriya.
Tare da qungiyar ‘Yan Uwa Musulmi akwai qungiyar Xalibai Musulmi ta Nijeriya, watau M.S.S. wacce aka kafa ta shekaru 50 da suka wuce. Waxannan qungiyoyi biyu sashen su ya haxe da sashe kuma suna yin nashaxinsu a jami’o’i da manyan makarantun qasar nan. A wani yayi nashaxinsu yana shafar ‘yan makarantun sakandare ta hanyar tarukan horaswa da suke shiryawa xaliban qananan makarantu a lokacin hutu.
156
Masu shagala da aikin da’awa a qarqashin inuwar waxan nan qungiyoyi yawancinsu matasa ne maza da mata masu karatun fannonin ilmi dabam – daban, kamar Kimiya da Likitanci da Tattalin Arziki, kaxan ne daga cikinsu suke karanta Musuluncin kansa. Wannan ya sa, koda yake suna da son Musulunci ga kuma gafin quruciya, amma suna da qarancin ilmin addini. Saboda haka a lokacin da Shi’a ta shigo nan qasar, a kan doron juyin juya hali na Musulunci (!) na qasar Iran da kirarinsa mai xaukar hankali na kafa jumhuriyar Islama da zartar da hukunci da Shari’a, sai yawancin waxannan samari suka hau jirgin Shi’a da tikitin juyin Islama. Daga cikin waxannan samari akwai Malam Ibrahim Ya’aqub Alzakzaki.
Alzakzaki da Yaxuwar Shi’a
Sunan Zakzaki ya fara fitowa a farkon shekarun 1980 lokacin da, bayan kammala karatunsa a fannin Tattalin Arziqi daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, ya qi ya je aikin bautar qasa, watau N.Y.S.C. saboda, kamar yadda ya ce, shi ba ya bautawa qasa; Allah kaxai
157
yake bautawa. Duk da raunin wannan magana da rashin fahimtar addini da take nunawa a fili, wannan mataki da Zakzaki ya xauka ya ba shi farin jini kuma ya mayar da shi tamkar wani gwarzo a idanun matasa waxanda wutar son addini take ci a zuciyarsu amma qwaqwalensu sun yi duhu duxum da jahilci. Zakzaki ya wayi gari ana lasafta shi daga cikin shugabannin xalibai da matasa masu sha’awar addini.
Ba’a daxe da haka ba, sai mahukuntan qasar Iran masu bin tafarkin Rafilanci, a cikin qoqarinsu na neman goyon bayan Musulmin duniya musamman a kan yaqinsu na shekaru takwas da qasar Iraqi, suka riqa gayyatar malamai daga ko wane vangare na duniyar Musulmi domin su halarci bikin shekara – shekara da suke yi don tunawa da nasarar juyin juya halinsu. Zakzaki na daga cikin waxanda aka gayyata daga Nijeriya.
Mahukuntan Iran waxanda suke xaukar nauyin baqinsu zuwa da komowa, suna nunawa baqin karamci, suna girmama su ainun kuma ga alama suna ba su xan goro a matsayin sallama. Banda wannan, suna qoqarin cusa ma baqin nasu ra’ayin Rafilanci ta hanyar laccoci,
158
muhalarori, tarukan qarawa juna sani da kuma kyautar littafai masu yawa. Ga alama ta wannan hanya sun yi nasarar ribace wasu da shigar da su tafarkinsu kamar Zakzaki, wasu kuwa sun gane makircinsu sai suka raba gari da su. Daga cikin waxanda aka gayyata daga Nijeriya kuma amma ba’a yi nasarar janye su zuwa Rafilanci ba akwai Malam Abubakar Tureta daga Kaduna da Malam Abubakar Jibril daga Sakkwato wanda ya zama a sahun gaba wajen yaqar Rafilanci a Nijeriya.
Alaqar Zakzaki da Iran ta ci gaba da yin qarfi a hannu guda, a xaya hannun kuma shahararsa ta bunqasa, kuma magoya bayansa sun yawanta a yayin da ya buxe rassa a yawancin jihohin arewacin qasar nan, yana kira da sunan gwagwarmayar kafa hukuncin Musulunci da yaqar waxanda ya kira xagutai.
Mabiyan Zakzaki sun yi ban gaskiya da shi ainun, sun yarda da shugabancinsa har suna ganin wanda duk bai xauke shi a matsayin shugaba ba kamar shi ba Musulmi ba ne, suna cewa wanda ya mutu bai yi masa mubaya’a ba to ya mutu mutuwar Jahiliya. Shi kuwa ya yi amfani da amince masa da suka yi, ya riqa gabatar
159
musu da koyarwar Shi’a da aqidojinsu sannu a hankali kuma koda yaushe aka tsorata su da kusancin shugabansu da Iran, sai ya ba su tabbacin cewa shi babu abinda ya haxa shi da Iran sai gwagwarmaya da yaqar Amurkawa da Yahudawa da xagutai. Amma kuma a hannu guda, Zakzaki ya ci gaba da shigo da alamu da bukukuwan Rafilawa kamar babbaqun rawuna, bikin Ashura, da sauransu.
Haka nan gogan naka ya ci gaba da taqiya, yana yaudarar almajiransa da magoya bayansa har ranar da dubunsa ta cika. Wata mujalla daga cikin irin mujallun da ake bugawa a qasar Iran ana aikowa da su Nijeriya ta buga wata maqala wacce a cikinta aka ci zarafin Sahabin Annabi (SAW) mai shuhura watau Abu Huraira (R.A). Wannan ya tayar da hankalin wasu daga cikin mabiyan Zakzaki inda suka nemi ya fito fili ya la’anci wannan maqala amma ya qiya. Wannan shi ya buxe idanun da yawa daga cikin mabiyansa waxanda a da jahilci da bin son zuciya ya rufe idanun nasu. Daga nan aka samu wani reshe a cikin mabiyan Zakzaki wanda ya yi ta matsawa malamin lamba a kan ya fito fili ya bayyana matsayinsa dangane da ko Shi’a yake yi ko a’a. Zakzaki
160
ya ci gaba da noqewa har dai daga bisani tusa ta qurewa bodari kuma gaskiya ta yi halinta. A cikin shekarar 1995 aka yi uwar watsi bayan wani taron qure qarya da aka yi wa Zakzaki a hedkwatarsa a Zaria. Mabiyansa da yawa, ciki har da manyan almajiransa, suka valle, suka yi shelar barrantarsu da Zakzaki da tafarkinsa na Rafilanci kuma suka kafa tasu qungiya ta yunqurin jaddada Musulunci a kan tafarkin Ahlus Sunna, Jama’atu Tajdidil Islam (J.T.I.), a qarqashin shugabancin Malam Abubakar Mujahid. A yanzu asirin Zakzaki ya tonu kuma taqiya ta qare, amma kash! Biri ya riga ya yi varna.
Dalilan Yaxuwar Shi’a a Nijeriya
Akwai dalilai masu yawa da suka taimaka wajen yaxuwar tafarkin Rafilanci a nan qasar. Za mu duba muhimmai daga cikinsu.
Dalili Na Farko: Gazawar Malamai
Dalili na xaya kuma mafi muhimmanci, shi ne gazawar malamai a shugabancin jama’a da shiryar da su,
161
da yi musu jagora da katangance su daga vata. Domin famintar wannan dalili za mu kasa malamai gida uku.
1. Malaman zaure, ko kuma malaman buzu kamar yadda ake kiran su a wasu wurare. Wannan kashi a cikin malamai su ne mafi girma, mafi alqadari kuma mafi qima a idanun mutane. Amma duk da girma da qimarsu da muke gani, za mu rufe ido mu faxi gaskiya game da su domin gaskiya ta fi ko wane mai qima qima.
Matsala ta farko da malaman zaure, yawancin su, shi ne imma dai suna da qarancin sani ko kuma ilminsu ya sava Sunna. Xauki ilmin Tauhidi ga misali, wanda shi ne mafi muhimmanci kuma mafi xaukakar dukkan ilman Musulunci. Har yanzu malamanmu na buzu ba su rungumi tafarkin Sunna ba a babin Tauhidi; Tauhidinsu imma Ash’ariya ne ko kuma Tauhidin masu Ilmul Kalam wanda yake da tushensa a wajen Mu’utazilawa ko Falasifawa.
A fannin Fiqihu, wanda shi ne fannin da malaman zaure suka yi fice, yawancinsu a Fiqihun Malikiya kawai suka tsaya. Idan mutum ya duba cewa banda sauran mazhabobi uku fitattu, watau Hanafiya, Shafi’iya da Hanbaliya, akwai mazhabobin Zahiriya da
162
Zaidiya, banda mazhabobin xaixekun malamai waxanda ba su samu yaxuwa ba kamar mazhabar Thauri da Auza’i da sauransu, sai mutum ya ga cewa babu shakka malamanmu kaxan suka xebo a Fiqihun Musulunci. Ba’a maganar fannin Usulul Fiqhi. Kuma ko a Malikiya ma, wasu littafai ne qididdigaggu suke laqema, wasu manyan littafan mazhabar yawancinsu ba su karanta su, kamar Tafsirin Qurxubi da Tafsirin Abubakar Ibnul Arabi, da Altamhid na Ibnu Abdilbarri da Bidayatul Mujtahid na Ibnu Rushd, da sauransu. A nan ba kuxin goro muke yiwa malaman ba; amma muna bayyana halin yawancinsu ne.
A fannin Tafsiri kuwa, ya ishe ka manuniya cewa a qasar Hausa duka idan mutum ya ce, ‚Na tafi wajen jalalaini,‛ to wajen karatun tafsiri yake nufi saboda tafsiri shi ne jalalaini kuma jalalaini shi ni tafsiri. Wannan yana nuna yadda malamanmu suka tsaya a kan littafin Tafsirul Jalalaini na Jalaluddinil Mahalli da Jalaluddinis Suyuxi kawai a koyo da koyarwarsu na fannin Tafsiri. Idan aka duba cewa wannan littafi bai kai matsayin moxa guda ba a cikin kogi dangane da abinda aka rubuta a fannin Tafsiri, sai a ga cewa tabbas abinda malamanmu suka
163
rasa ya fi abinda suka samu a cikin wannan fanni. Bari batun ilmin Usulul Tafsir. A nan ma, ba kuxin goro muke yi wa malaman ba; amma hukunci a kan mafi yawa ake yin sa, mafi qaranci togewa ne.
Matsalar Luga a wajen malaman buzu makomarta ita ce ga matsalar manhaja da tsarin koyarwa. Koyon Luga yana da rukunai uku: karatu da rubutu da furuci. Ga alama malaman zaure karatu kaxai suke yi saboda a tsarin karatun zaure babu zancen a bayar da aiki a rubuto, watau abinda ake cewa da Larabci ‚tamrinat‛ ko ‚tamarin‛, ko kuma da Turanci ‚exercises‛. Wannan ya sa koda yake malaman zaure yawanci suna da babbar taska ta xaixekun kalmoni, ‚vocabulary‛, amma magana da Larabci tana yi musu wuya, haka nan rubutawa. Kuma koda yake ana iya lura cewa malaman buzu gwanayen rubutun waqa ne da Larabci, makomar wannan, wata qila, shi ne cewa ita waqa ‘yar kyaikwayo ce.
Haka nan a fannonin Hadisi da Tarihi da Sira da Firaq; malaman buzu, in ka xauke su gaba xaya, suna da qarancin rabo a cikin waxan nan ilmai. Rashin ilmin Firaq, watau ilmin qungiyoyin bidi’a da aqidojinsu, shi ya sa malaman zaure suka rasa ta yi a gaban kogin
164
Rafilanci yayin da ya yi ambaliya domin ya tafi da matasan Musulmi. Manyan littafan da aka rubuta a ilmin Firaq kamar Almilal wal Nihal na Shahrastani da Maqalatul Islamiyina wa Ikhtilaful Musallina na Imam Abul Hassan Al’ash’ari da Alfarqu bainal Firaq na Shaihul Islami Abdulqahir Albagdadi da Alfisal fil Milal wal Ahwa’i wal Nihal na Ibnu Hazm Al’andalusi da sauransu, yawancinsu ko sunayensu ba su tava ji ba. Wannan ya sa wai suka xauka cewa Shi’anci wani wasan yara ne wanda za su bari in sun girma. Idan aka ce su bincika abinda yake faruwa a tsakanin Rafilawa sai su ce, haba wannan hayaniyar quruciya ce suke yi, za su bari ne. Sai ga shi waxannan malamai waxanda suka tashi zaune tsaye a saboda wasu ‘yan qungiyoyi da suka ce wai suna zagin waliyai, sai gashi ana zagin Sahabban Annabi (SAW) sun yi shuru. Saboda haka suka kyautata alwala amma suka gaza sallah!
Abinda ya gabata dangane da ilminsu ne; amma idan muka duba ayyukansu sai mu ga abin mamakin. Mun gabatar da bayani cewa a cikin malaman Musulunci a nan qasar, malaman zaure su ne mafi yawa, mafi alqadari kuma mafi qima a idanun mutane. Abinda ya sa
165
suka zama haka shi ne cewa su magadan Jihadin Shaihu Danfodiyo ne. Amma a yau, ayyukansu da halayensu sun sava da na malaman Jihadi. Malaman Jihadi sun yi ilmi mai zurfi, kuma littafan da suka bari suna shaidawa da haka, amma malamanmu na yau abin ba haka yake ba. Shaihu Usmanu ya rubuta kimanin littafai 90, Shaihu Abdullahi kimanin 70; Muhammad Bello xan Shaihu kimanin 80; Nana Asma’u kimanin 55; amma malamanmu na yau, saboda gafala rubutun ma laifi suka xauke shi. Idan ka ce su rubuta littafi sai su ce wai ba su gama da waxanda aka riga aka rubuta ba; idan kuma kai ka rubuta sai su ce ka yi karambani. Alhali Shaihu Usmanu, a cikin littafinsa Najmul Ikhwani, yana kira ga Musulmi da su riqa karanta littafan malaman zamaninsu, saboda malaman ko wane zamani su suka fi sanin matsalolin wannan zamanin, kuma wajibinsu ne su nemawa matsalolin magani.
Malaman jihadi sun yi wa’azi, malaman buzu ba sa yin wa’azi sai kaxan. Malaman jihadi sun yaqi bidi’a, malaman zaure su bidi’ar suke yaxawa kuma duk wanda yake yaqi da bidi’a to su shi ne abokin gabarsu. Malaman jihadi sun nesanci sarakai da masu mulki, na
166
yanzu kuwa shige musu suke yi. Malaman jihadi sun yi jihadi kuma sun jaddada addini, malamanmu na yau ba su san ko inda za’a kama bakin zaren ba. Malaman Jihadi sun tsaya tsaiwar daka, sun yi gwagwarmayar tabbatar da gaskiya da tsai da adalci, malamanmu na yau cewa suke yi yanzu zamanin yin shiru ne da lazimtar cikin gida, kamar yadda wani babban malamin zaure ya faxawa Shaihu Abubakar Mahmud Gumi. (Duba littafinsa, Where I Stand, 51). Malaman jihadi sun gina al’umma, malaman buzu sai aikin gina gidajensu na gado. Ko wane malami ya qasaita sai ka ji ya naxa khalifa, wai xan da zai gaje shi. Ko waye ya ce musu ilmi gado ne? Malaman jihadi sun ce a yi sana’a (duba Ahkamul Makasib na Muhammad Bello) su kuwa yawancinsu ba sa sana’ar, balle su ce wani ya yi, sai cin abinda suke kira albarkacin makaranta!! Wani malamin ma har faxa yake yi don me za’a ce Musulmi su daina bara!! Kuma qarya yake yi; shi ‘ya’yansa ba sa bara.
Wannan shi ne halin yawancin malaman zaure kuma shi ne tushen kusan dukkanin matsalolin da muke fama da su a yau. Don haka babu mamaki idan ba su taka
167
rawa ta ku-zo- ku-gani ba wajen hana yaxuwar Shi’anci a qasar nan.
2. Kashi na biyu na malaman shi ne wanda za mu kira da sunan Ustazai. Wannan kashi ya haxa da dukkan waxanda suka yi karatun addini amma a zamanance, kamar waxanda suka halarci makarantun Haya Muslim kuma suka yi karatun diflomomi ko digri na fannin nazarin addinin Musulunci ko shari’a a manyan makarantu da jami’o’in qasar nan. Kuma ya haxa da waxanda suka yi karatu a jami’o’in qasashen Larabawa da sauran qasashen Musulmi. Waxannan yawanci suna da kyakkyawar manhaja ta koyon karatu kuma ilminsu yana da faxi da zurfi koda yake wasunsu, kamar waxanda suka fita daga jami’o’in qasarnan, ilmin nasu faxi gareshi kawai amma ba zurfi. Sai dai duk da haka suna samun kyakkyawan harsashi wanda yake ba da dama ga duk wanda yake so cikinsu da ya zurfafa. Suna tsakuro wani abu kusan daga ko wane fanni muhimmi na addinin Musulunci kamar Alqur’ani da Hadisi (waxan nan ba su da qarfi a manhajojin jami’o’in Nijeriya); Fiqihu da Usulul Fiqihi, Falsafa da Tauhidi (a makarantun Nijeriya yawanci Tauhidin Ash’ariya ake
168
koyarwa); Tarihi da Sira; da kuma fannonin Luga dabam – daban irin su Adab, Nahwu, Sarfu, Balaga da ressanta uku, Aruli, da sauransu. Samun qaqqarfan harsashe na luga yana zama tamkar wani mabuxi ga ustazai wanda suke buxe taskokin ilmi da shi.
Kamar yadda ustazai suka sha bamban a wajen ilminsu, da mai zurfin ilmi da mai cikin cokali, haka nan suka sha bamban wajen ayyukansu da halayensu da sadaukar da kansu ga addini. Akwai masu aqidar Salaf, masu bin Sunna da yaqar bidi’a, kamar yadda akwai ‘yan gargajiya wajen aqidarsu da fahimtarsu da rungumar bidi’a. Daga cikin waxannan na biyun akwai waxanda suka fito daga gidajen malaman zaure, waxanda suka fito daga gidajen sarautar gargajiya da masu karkata ga xariqun sufaye. A cikin ustazai akwai masu yin wa’azi da waxanda ba sa yi, da masu yaqar bidi’a da ‘yan ba-ruwanmu da waxanda suka sadaukar da kawunansu domin koyar da mutane da aikin da’awa da waxanda ba sa koyarwa sai dai a aji inda ake biyan albashi.
Yawanci waxanda suka wayar da kan Musulmi dangane da tafarkin Rafilanci, suka bayyana vacinsa da sharrinsa da vatansa, suka yi fama don dakatar da
169
yaxuwar Shi’anci a tsakanin Musulmi daga cikin wannan kashi suke. Daga cikinsu akwai waxanda suka yi amfani da koyarwa da wa’azi wajen yaqar Shi’a kamar Shaihu Abubakar Mahmud Gumi, wasu sun yi amfani da huxuba kamar Shaihu Abubakar Jibril Sakkwato, wasu sun yi amfani da alqalumansu kamar Shaihu Aminuddini Abubakar Kano wanda ya fassara littafin Alkhuxuxul Arida na Muhibbud Dini Alkhaxib zuwa harshen Hausa wanda a karon farko ya fallasa asirin Shi’a ga jamhurun Musulmi waxanda ba sa karatun Larabci to Turanci.
3 Saboda rashin kalmar da ta fi, za mu kira kashi na uku na malaman da sunan Burazozi wanda wannan hausancewa ne na kalmar ‚brothers‛ ta Turanci wace take nufin ‘yan uwa. Abinda nake nufi da burazozi, ko kuma ‘Yan Buraza kamar yadda aka fi sanin su, su ne mutane, yawanci matasa, waxanda suke da son Musulunci a zuci amma kuma galibi suke da qarancin saninsa. Yawanci suna sanin Musulunci ta hanyar sauraron laccoci a wurin taruka, karanta qasidu da maqalu a cikin jaridu na yau da kullum da kuma mujallu masu kulawa da al’amuran Musulmi. Yawancinsu xalibai ne masu karatun fannoni dabam-daban a manyan
170
makarantu da jami’o’i kamar fannonin kimiya, fasaha, tattalin arziki, likita, lauya da sauransu. Kaxan ne daga cikinsu suka karanta Musulunci kuma a mataki na qasa ainun, imma I.R.K. a makarantun sakandare ko kuma qaramar faifa ta aro a jami’a.
Kamar yadda na faxi a baya, yawancin waxannan matasa ne masu tsananin son addini da kishin sa amma kuma babu wadatar ilminsa. Idan ka haxa qarancin sani da tsananin kishi da gafin quruciya sai ka samu wani kwaxo mai haxari. Kuma da yake yawanci suna jin Turanci, harshen da a da shi ne ake yin amfani, kuma ake burga, da shi a makarantu, wannan sai ya ba su damar shaqe wuyan makirfon da faxi a saurare su, koda abinda za su faxi xin ba shi da nauyi ainun. Wani babban abinda yake qara tauye su shi ne rashin jin Larabci kuma kamar yadda aka sani duk wanda bai jin Larabci to ba ya shan kunun Musulunci sai dai ya sha farau – farau. Wannan kashi na ‚malamai‛ daga cikinsu ne yawancin ‘yan Shi’a suka fito, ciki har da madugunsu Malam Zakzaki.
171
Wannan bayani duka ba yana nufin cewa wannan kashi na malamai bai yiwa Musulunci kome ba; a’a. A haqiqa ‘Yan Buraza sun toshe wata babbar kafa a makarantunmu wacce, musamman a shekarun 1970 da 1980, ba mai iya toshe ta sai su. Sun taimaka ainun wajen tsayar da ibadoji, kamar sallah da azumi, a makarantu, sun tari qalubalen qungiyoyin Kirista kuma sun taimaka wajen yaqar malamai da xalibai masu karkata ga tafarkin Gurguzu a jami’o’inmu a lokacin da Kwaminisanci yake yaqar addinai da al’adu a qasashe masu tasowa.
Dalili na Biyu: Jahilci
A yayin da malamai suka gaza sai jahilci ya samu filin baje koli. Juyin juya hali na qasar Iran ya faranta ran al’ummar Musulmi ganin yadda tutar Musulunci ta xaukaka da yadda daular kafirci mafi girma, Amurka, ta kunyata. Wannan ya sa Musulmi da yawa suka sha’afa da a qidar mutanen Iran a lokacin da suka riqa duban su a matsayin wani abin koyi da ya kamata kowa ya yi koyi da su. Da yawa
172
daga Musulmi sun zaci cewa bajintar mutanen Iran da nasarar da suka samu ta ‘yantar da kansu daga zaluncin Amurkawa da danniyar Turawan yammacin duniya baki xaya, sanadinta shi ne aqidar Rafilanci da suka qudure. Wasu jahilai kuma suka riqa zaton cewa munafunci da suke gani a wurin wasu sarakai da shugabannin qasashen Musulmi masu bin tafarkin Sunna tushensa shi ne aqidarsu ta Sunna wace babu bore, ba gwagwarmaya, kuma babu qundumbala a cikinta. Wannan sai ya sa Musulmi da yawa, musamman matasa, masu tsananin son Musulunci da qin kafirci da jin takaicin halin qasqanci da koma baya da al’umma suke ciki, suka riqa ganin sun sami mafita a cikin koyi da mutanen Iran.
Wani abu da ya qarawa mutanen Iran farin jini da haiba a idanun Musulumi waxanda zukatansu suke cike da son Musulunci amma qwaqwalensu wayam, shi ne wasu kalmomi masu qyalli da qyal-qyali da suka riqa amfani da su kamar gwagwarmaya, barranta daga xagutai, gogayya da kafircin duniya, yaqi da waxanda suka kangarewa Allah Ta’ala, fatattaqar Yahudawa da ‘yanto masallacin Baitul
173
Maqdis, kafa jumhuriyar Islama, yin shahada wajen xaukaka addinin Allah, da irin waxannan kalmomin take da kirari waxanda Rafilawa suka yi ta burgewa da su.
Ga alama irin waxannan kalmomi su suka burge Zakzaki da maqarrabansa inda suka yi ta maimaita su kamar yadda akun kuturu take kyaikwayon abinda aka gaya mata ba tare da ta san ma’anarsa ba. Da waxannan kalmomi su ma suka ja gayya, inda komai na Iran ya zama abin yayi, kama daga babbaqun rawunansu zuwa manyan alkebbunsu, kai har da sunayensu da laqabansu, da tafiyarsu da maganarsu. Hotunansu da jaridunsu da mujallunsu da uwa uba littafansu suka cika ko ina. A cikin wannan ruxu, mugunyar aqidarsu ta yi saraf ta shige qwaqwalen dake haihai. Da haka ne Shi’a ta yaxu a Nijeriya a qarqashin inuwar gazawar malamai da gafalarsu.
Dalili na Uku: Talauci
Talauci shu’umin abu ne. Yana zama haxari ga lafiyar mutum da tunaninsa; ga halayensa da xabi’unsa; ga
174
zamantakewar iyali da zaman lafiyar al’umma; kuma abinda ya fi kome haxari, talauci yana iya mayar da Musulmi kafirai. Wannan ya sa Manzon Allah (SAW) a koda yaushe yake addu’a yana neman tsari daga talauci, kamar yadda aka ruwaito yana cewa, ‚Ya Ubangiji, ina neman tsarinka daga talauci da qaranci da qasqanci.‛ (Abu Dawuda da Nasa’i). Kuma yana cewa, ‚Ya Ubangiji, ina neman tsarinka daga kafirci da talauci.‛ (Abu Dawuda). Duba ka gani yadda ya gama tsakanin kafirci da talauci za ka fahimci cewa haxarin talauci yana da girma. (Domin ganin haxarin talauci da muninsa, sai a duba Mushkilatul Faqar wa kaifa Alajahal Islam na Yusuf Alqaradawi, 12-25.)
Talauci ya taka mugunyar rawa ta fuska biyu wajen yaxuwar tafarkin Shi’anci a tsakanin matasa Musulmi a Nijeriya. Fuska ta xaya ita ce kasancewar matasa da iyayensu yawanci suna fama da talauci da rashin abin yi, don haka Rafilanci wanda yake cike da hayaniya da zanga-zanga da sauransu, sai ya zama wata mafita ce ga matasa da za su fita daga zaman banza da suke fama da shi kuma su sami abin yi wanda zai shagaltar da su daga matsalolin rayuwa waxanda suka dabaibaye su. Fuska ta
175
biyu ita ce kasancewar da’awar ‘yan Shi’a da harakarsu ta xauki salon zuga talakawa a kan masu mulki da attajirai ta yadda koda yaushe suke maimaita magana a kan xagutai da azzalumai wanda ya sa talakawan Musulmi, waxanda a haqiqa an zalunce su xin, suka rufawa ‘yan Shi’a baya domin huce fushi da fatan rama gayya a qarqashin daular Rafilawa wacce suke fatan kafawa.
Yana da wuya a yi bayani filla-filla yadda gwamnatin qasar Iran ta yi amfani da kuxi wajen yaxa tafarkin Rafilanci a Nijeriya, amma kowa ya san da walaki wai goro a miya. A lokacin da yake kan ganiyarsa, kafin Shi’ancinsa ya fito fili rabin mabiyansa su valle masa, Malam Zakzaki tare da gwamnoninsa na jihohi, watau amir-amir da ya kafa a jihohi, duka suna rayuwa maya-maya, irin rayuwar attajirai masu hannu da shuni. Banda katafaren gidan da ya gina a garinsu Zaria, malamin kuma yana more kayan alatu kamar zunduma-zunduman motoci, kayan sadarwa na zamani, karikicen lantarki da sauransu. Wannan kuma shi ne halin manyan maqarrabansa waxanda suke a hedkwatarsa a Zaria da kuma waxanda suke a jihohi. Saboda haka muke ganin
176
cewa mutanen, kasancewar ba sa yin aikin gwamnati ko kamfani tunda wannan a ganinsu aikin xagutu ne, ba za su rasa samun xan hasafi ba daga wasu kafafe da vangarori wanda da shi ne suke tafiyar da harkokin qungiyarsu kuma su samu tsabar da suke watsawa ‘yan tsaki. Kuma idan muka dubi talaucin da mutanen qasar nan suke fama da shi, musamman Musulmi, tun daga farkon shekarun 1980, lallai tsaba na iya kai ‘yan tsaki ko ina, in ya so ta baro su.
Dalili na Huxu: Tavarvarewar Zamantakewa
Wani dalili da ya taimaka wajen yaxuwar Rafilanci shi ne tavarvarewar yanayin zamantakewa a tsakanin jama’a sakamakon sauye-sauye da suka faru a rayuwar al’ummarmu. Waxannan sauye-sauye sun haxa da qaura daga rayuwar karkara zuwa rayuwar maraya, tasirin rayuwar wasu al’ummai a kanmu, raunin dangantaka tsakanin rukunan al’umma: tsakanin iyaye da ‘ya’ya, manya da yara, shugabanni da talakawa, malamai da mabiya, da sauransu.
177
A yanzu kulawar iyaye ga yaransu ta yi qaranci ta yadda uba bai sanin inda xansa yake yin harkokinsa, ko da suwa yake hulxa. Don haka bai san abinda ya koyo, ko ra’ayin da ya xauko ba. Ikon da manya ke da shi a kan yara a yanzu ya yi rauni. A da ana cewa yaro na kowa ne, kuma babban mutum ko dattijo yana iya tsawatawa yara koda bai san su ba kuma dole su saurare shi. Amma a yanzu ana ganin yara suna cin karensu ba babbaka, babu mai ce musu ku ci kanku. A yau, talakawa sun daina mutunta shugabanni waxanda suka rasa kwarjininsu saboda qarya da sata (‘yan siyasa), jahilci da kwaxayi (sarakan gargajiya). Mawadata sun rasa ban girman matalauta waxanda suke ganin son abin duniyarsu ya yi yawa kuma sun hana su haqqinsu na zakka. Malamai suma girmansu ya faxi a lokacin da mutane suka lura cewa suna gudu bayan abin duniya kuma sun miqa wuya ga masu mulki da mawadata, sa’annan sun bar matsayinsu na magadan annabawa. Wannan sakwarkwacewa a cikin alaqar rukunan al’umma junansu da juna ya bar matasa da gama-garin mutane a sake ba kariya, kuma wannan hali ya baiwa baraden Dujal, kamar shugabannin Rafilawa, damar su baje kolinsu kuma su ci
178
karensu ba babbaka. A sakamakon haka, magoya bayansu sai qara yawa suke yi koda yake abinda suke kira zuwa gare shi halaka ne da vata.
Dalili na Biyar: Gazawar Masu Mulki
Tsare Addini, hifzud dini, yana cikin manyan manufofin Shari’ar Musulunci, kuma tabbatar da shi aikin hukuma ne. Daga cikin hanyoyin tsare addini akwai kiyaye shi daga dukkan abinda zai iya gurvata shi ko ya vata kyawunsa kamar bidi’o’i da camfe-camfe da tsurface-tsurface da duk wani abu da ya savawa Alqur’ani da Sunna.
Abin takaici ne cewa tsarin siyasar da muke bi a yau tsari ne wanda babu ruwansa da addini. Saboda haka masu mulki suke ko-in-kula da abinda ya shafi addini sai fa idan ya zama zai amfani manufofinsu da maslahohinsu na siyasa. A sakamakon haka, Musulunci ya zama ba shi da gata, ko wane jahili ko wani mugun malami Dujal sai ya shiga harkar addini ya yi abinda ya ga dama. Wani abin mamaki kuma shi ne, ko a jihohin da suke amfani da Shari’a a yanzu, abin bai canja ba. Koda yake an kafa
179
ma’aikatun kula da harkokin addini a waxannan jihohi, amma ga alama waxannan ma’aikatu ba su xauki yaqi da bidi’o’i a matsayin xaya daga cikin manyan ayyukansu ba. Wannan kuwa ba abinda yake nunawa sai rashin fahimtar aikinsu ko rashin sanin makamar aikin. Idan Ma’aikatar Kula da Harkokin Addinin Musulunci ba ta yaqi bidi’a da masu yaxa bidi’a ba, to mene ne amfaninta?
Ya kamata gwamnatocin jihohin Musulmi, kai har ma da gwamnatin tarayya, su fahimci haqiqanin Rafilanci da xabi’arsa. Yaxuwar Shi’anci matsala ce ta tsaro, ba wai kurum matsala ce ta addini ko ta zamantakewa ba. Babu inda za’a samu Shi’a ta yaxu a tsakanin Musulmi ba tare da sun kawo fitina da tashin hankali da zubar da jini ba. Wannan shi ne abinda tarihi yake shaida da shi kuma shi ne abinda muke gani a yau a dukkan qasashen da suke da ‘yan Shi’a masu yawa kamar Pakistan, Iraqi, Lebanon da sauransu. Saboda haka zai zama tamkar wani kyakkyawan riga kafi ne idan Musulmin Nijeriya suka yiwa kansu qiyamallaili, suka tsayar da yaxuwar Shi’a tun al’amarinta bai faskara ba. Kuma abin farin ciki shi ne, har yau ba’a makara ba; amma an yi kusa!
180
Yanayin Yaxuwar Shi’a a Yau
Tun zuwan Shi’a Nijeriya, qungiyar ta taka matakai uku na yaxuwa kamar haka:
Na xaya, matakin yaxuwa a lokacin taqiya da munafinci da yaudara. Wannan shi ne lokacin da shugabannin Shi’a suka yi ta kira da sunan gwagwarmaya da sabunta addini da kafa hukuncin Musulunci. A wannan yayi, qungiyar ta yaxu yaxuwa mai yawa a lokaci qanqani sakamakon qishirwar matasa ta sauyi da kuma rashin sanin haqiqanin abinda da’awar ta qunsa a wannan mataki.
Mataki na biyu, shi ne lokacin da Malam Zakzaki ya fito fili ya bayyana cewa lallai Shi’a yake yi bayan taqiya ta tsawon shekara goma sha biyar ko sama da haka. A wannan lokaci qungiyar ta rabe biyu kusan a tsakiya, inda a shekarar 1995 aka samu vullar qungiyar Jama’atu Tajdidil Islam wacce ta yi shelar barrantarta daga tafarkin Rafilanci kuma ta yiwa shugabancin Zakzaki tutsu. Qoqarin matasa dake vangaren J.T.I. da qungiyar Izala da kuma malamai da almajirai masu bin
181
tafarkin Salafiya, qoqarin waxannan gaba xaya wajen tona asirin Shi’a ya kawo tsaiko ga yaxuwarta, musamman a birane inda a da a nan ne ta fi yawan mabiya.
Ga alama a yanzu, Shi’a tana shiga mataki na uku na yaxuwa, inda masu aikin yaxa ta suka mayar da hankali zuwa qauyuka da yankunan karkara. A cikin ‘yan shekarun nan, biyu zuwa biyar, Rafilanci yana yaxuwa kamar wutar daji a qauyuka saboda qarancin ilmi da wayewa ta addini da kuma cewa yawancin masu wa’azi suna tattara qarfinsu a birane, sai kaxan ke fita dawa. Wnnan ci gaba, ko kuma ci baya za mu ce, da aka samu yana da haxarin gaske. Dalili shi ne, dama Shi’anci jahilci ne, kamar yadda mai karatu ya riga ya gani, to idan aka haxa shi da jahilcin dake akwai a karkara, to an samu itace jiqe jagab da kananzir, babu abinda ya rage sai qyastun wuta! Idan haka ta faru, Allah ya tsare, za mu wayi gari a wani yanayi wanda varnar Maitatsine da ta’addancin Kiristoci za su zama tamkar wasan yara. Allah ya kiyashe mu fargar jaji.
182
183
Rufewa: Shi’anci da Sufanci Tagwaye Ne
Mutane suna mamakin auren zobe dake tsakanin ‘yan Shi’a da Sufaye ‘yan Xariqa a qasar nan. Abin mamakin shi ne, a lokacin da wasu qungiyoyi suka bayyana suna kira zuwa ga raya Sunna da yaqar bidi’a, malaman xariqa sun tashi zaune tsaye, suka kai gwauro suka kai mari wajen yaqar waxan nan qungiyoyi saboda wai suna zagin waliyai. Sai gashi a lokacin da Rafilawa suka
184
bayyana suna zagin Sahabban Annabi (SAW) kuma suna kafirta su, malaman xariqa ba su ce ko ‚as‛ ba. Banda ma kawai ba su ta da kara wajen yaqar su ba, amma sun rungume su hannu biyu-biyu, sun haxa kai da su, kuma har ma a wasu wurare suna tafiya tare da su kamar yadda abin yake a Kano tsakanin ‘yan Shi’a da ‘yan xariqar Qadiriya. Abin mamakin shi ne, yaya mai ta da jijiyar wuya, ya yi jidali har ya kai ga zubar da jinni saboda an zagi waliyai zai yi shiru ya qyale masu zagin Sahabbai? Shin waliyai sun fi Sahabbai ne ko kuwa ya aka fara?
Sai dai wannan mamaki zai gushe idan mai karatu ya fahimci cewa Shi’anci da Sufanci fuska biyu ne na kwabo guda, watau kwabon bidi’a. Ko kuma mu ce, Shi’anci da Sufanci tagwaye ne, uwarsu guda ita ce bidi’a, ubansu guda shi ne jahilci.
Babu shakka Shi’anci da Sufanci sun samo asalinsu ne a cikin bidi’a wacce aka qaga aka laqa ga wannan addini. Kuma akwai abubuwa da dama na aqidu, tunane-tunane da ra’ayoyi da waxannan tafarkai biyu na vata suka haxu a kai. Koda yake ba manufarmu ba ne gudanar da muqarana, ko gwaji, tsakanin waxannan ressa biyu na
185
itaciyar bidi’a, amma za mu ambata kaxan daga irin abubuwan da suka haxu a kai.
Na xaya: Tauhidi. A babin Tauhidi, qungiyoyin biyu sun haxu a kan bin Tauhidin Mutakallimuna da Falasifa maimakon Tauhidin Salaf na Sunna. Ga misali, suna yin tawilin wasu sifofi na Ubangiji Maxaukaki tare da juya baya ga wasu hadisai ingatattu a wannan babin. (Domin sanin Tauhidin Salaf, sai a duba littafinmu Tauhidi: Haqqin Allah a kan Bayinsa wanda zai fito ba da jimawa ba, in Allah ya yarda. A yanzu ya fito.)
Na biyu: Rungumar bidi’a. ‘Yan Shi’a da ‘yan xariqa suna tarayya wajen aikata bidi’a, watau bautawa Allah da abinda bai yi izini ko umarni da shi ba, sai dai son zuciya kawai, da kuma aiki da abinda ya savawa Alqur’ani da Sunna.
Na uku: mayar da asali ga Ali binu Abi Xalib. Shi’a da xariqa suna mayar da tushensu ga sahabin Annabi, Ali binu Abi Xalib, Allah ya yarda da shi. A cikin wannan littafi mun ga yadda Rafilawa suka yi ittifaqi a kan cewa shi ne imami na farko a cikin jerin imamansu goma sha biyu, kuma sauran imaman duka zuri’arsa ne. Wasu a cikinsu suka ce shi ne ya kamata ya zama annabi sai dai
186
wai mala’ika Jibirilu ya yi kuskure ya kaiwa Muhammadu (SAW) manzanci. Wasu ma suka ce shi ubangiji ne kuma suka bauta masa, kamar yadda bayani ya gabata.
Su kuwa ‘yan xariqa sun kafa dangantakarsu da Ali (RA) a kan wata tatsuniya wacce suka kitsa dangane da wata riga da suke kira khirqa. Suka ce asalin wannan riga ta Annabi Ibrahimu ce, mala’ika ne ya kawo masa ita daga aljanna a lokacin da kafirai suka jefa shi a wuta. Kuma wai sanya ita wannan riga ne ya hana shi qonewa a wutar. To wannan riga, a faxinsu, ita ce annabawa suka yi ta gadon ta har ta iso ga Annabinmu Muhammadu (SAW). To da yake bayan Annabi Muhammadu babu wani annabi, sai dai waliyai, to sai ya duba babban waliyi daga cikin Sahabbansa,shi ne Ali, sai ya ba shi ita. Wannan riga, in ji su, tana nan har gobe, manyan waliyai suna gadon ta. Kuma da yake asalin rigar ta aljanna ce, to tana nan ba ta tsufa balle ta ruve ko ta lalace. Wannan shi ne labarin khirqa, rigar aljanna. Sufaye da yawa sun yarda da samuwar wannan riga, kuma har yau idan wani malamin xariqa ya raina wayon almajiransa sai ya fito
187
musu da wata tsohuwar falmaran irin ta Larabawa sai ya ce khirqa ce.
Da wannan almara Sufaye suka haxa tushensu da Ali (RA). Kamar yadda a wurin ‘yan Shi’a Ali yake uban imamai, haka nan a wurin ‘yan xariqa yake uban waliyai. (Domin bayanin wannan riga da dangantakarta da qungiyoyin biyu, sai a duba Minhajus Sunna na Ibnu Taimiya, 4/242-245.)
Na huxu: Fifita imamai (a vangaren Shi’a) da fifita shaihunnai (a vangaren ‘yan xariqa) a kan annabawa da manzanni. A cikin babi na biyu a wannan littafi, inda aka yi magana a kan aqidar imama, bayani ya gabata yadda Rafilawa suke fifita imamansu a kan annabawa da manzanni da mala’iku makusanta, kuma a wani yayi su ba su sifofin allantaka. Sufaye a nasu vangaren, wasu, ba dukkaninsu ba, suna fifita waliyansu da shaihunnansu a kan annabawa ta hanyar cewa suna samun wasu ilmai da sane-sane kai tsaye daga Ubangiji ko ta hanyar mala’ika, amma ba ta hanyar annabi ba. Kuma su ma suna baiwa shaihunnansu sifofin allantaka kamar yadda muke gani a cikin wasu waqoqi da suke dangana musu. Ga misali,
188
wani mawaqin xariqar Qadiriya yana faxi dangane da shaihinsa kamar haka:
Yana kallo aka yo sama,
Yana kallo aka yo qasa,
Subhanaka Abdulqadiri,
Ya tsere sa’a, ba su cimma ba.
(Duba littafina, Matsayin Sufanci da Xariqa a Musulunci, 12-17.)
Wai ma Subhanaka! Wa ake cewa Subhanaka in ba Allah ba?
Na biyar: Yi ma Annabi (SAW) rinto da haxa shi tarayya da imamai da shaihunnai a cikin abinda Allah ya kevance shi da shi na daraja. Ga misali, ya inganta cikin hadisai cewa Allah zai baiwa Annabi (SAW) Maqamal Mahmudi ranar alqiyama, inda zai zama shugaban al’umman farko da na qarshe kuma a ba shi ceto mai gamewa. Rafilawa da wasu ‘yan xariqa, kamar suna yiwa Annabi qyashi, sai suka dangana wannan matsayi babba da daraja mai girma ga imaminsu da shaihinsu. Rafilawa suka ce ranar alqiyama za’a yi shela ga al’umman farko da na qarshe na mutane da aljanu, za’a nuna musu Ali binu Abi Xalib a ce shi ne shugabansu
189
kuma za’a kafa masa mimbari na haske ya hau ya yi huxuba ga talikai baki xaya. Su kuma ‘yan xariqar Tijjaniya, suka ce shaihinsu, Ahmad Tijjani, shi ne zai samu wannan daraja ta shugabancin talikai ranar alqiyama. (Domin maganar ‘yan Shi’a, sai a duba Kashful Gumma na Arbali, 1/141; kuma domin maganar ‘yan Tijjaniya, sai a duba Aldurratul Kharida sharhin Yaqutatul Farida na Shaihu Nazifi, 1/105.)
Na shida: Imamai da shaihunnai sun san gaibu. Rafilawa suna qudure cewa imamansu sun san gaibu kuma suma Sufaye, wasu daga cikinsu ba duka ba, suna qudure cewa shaihunnansu sun san gaibu. Wani lokacin su ‘yan xariqa ba su fitowa fili sai su rave da Annabi (SAW), suna cewa wai ya san gaibu. Idan an musa , sai jayayyar ta tsaya nan; idan kuma an karva, sai su qara taku guda gaba, su ce waliyai ma sun san baibu. Babu shakka ba wanda ya san gaibu sai Allah, kamar yadda ya faxi a cikin littafinsa mai tsarki: ‚Ka ce: Babu wanda ya san gaibi a cikin sammai da qasa face Allaha.‛ (Suratun Naml: 65). Da annabawa da manzanni da mala’iku babu wanda yake sanin wani abu na gaibu sai fa abinda Allah ya so ya sanar da shi, kamar yadda yake cewa: ‚Kuma ba
190
su kewayewa da kome daga ilminsa face da abinda ya so.‛ (Suratul Baqara: 255).
Na bakwai: Makauniyar biyayya ga imamai da shaihunnai. ‘Yan Shi’a da ‘yan xariqa suna yiwa imamansu da shaihinnansu makauniyar biyayya, inda suke bin su a kan al’amuran addini da na duniya ba tare da bayyanannar hujja ba. Rafilawa suna qudure cewa imamansu ma’asumai ne, watau ba sa kuskure kuma kome suka faxi dai-dai ne. (Duba babi na biyu: Aqidar Imama). Su kuwa Sufaye ba su cewa waliyansu ma’asumai ne, amma suna umartar almajiri ko muridi da ya kasance a gaban malaminsa tamkar gawa a hannun mai wankinta. Idan aka duba da kyau, sai a ga bambancin qalilan ne.
Misali mafi kusa shi ne na shugaban ‘yan Shi’a na jihar Kebbi, Malam Sunusi, wanda gwamnatin jihar da kuma Sarkin Gwandu suka gayyace shi a rubuce domin yi masa tambayoyi, amma bai amsa gayyatar ba wai sai ya samu izini daga shugabansu na qasa, Malam Alzakzaki. Da ‘yan jarida suka tambaye shi dalili sai ya ce, ‚Shi hukumar addini kaxai ya yarda da ita.‛ (Duba jaridar Weekly Trust, Augusta 14-20, 2004 shafi na 45).
191
Wannan yana nuna cewa babu wani abu da xan Shi’a zai iya yi sai ya samu izinin Alzakzaki wanda ga alama suna xaukar sa a matsayin ma’asumi.
Na takwas: Hore almajirai da mabiya da cin guminsu bisa qarya. Malaman Shi’a da shaihunnan xariqa sun haxu a kan wannan, watau iya hore mabiyansu da cin guminsu da bautar da su wajen biyan bukatunsu da kimtsa maslahohinsu. Idan suka kafawa mutum qahon zuqa, to sai dai Allah ya cece shi. Malaman Shi’a suna da haraji qayyadajje a kan mabiyansu wanda suke kira khumusi, watau kashi xaya cikin biyar wanda dai-dai yake da kashi ishirin cikin xari: 20 %. Duk abinda xan Shi’a ya mallaka na kuxi ko kadara, to malamai suna da khumusi. Ga alama madugun Shi’a na Nijeriya, Malam Ibrahim Alzakzaki, yana more wannan kaso, ganin yadda mabiyansa suke rawar qafa su kawo masa dukiya inda duk ya sauka.
Na tara: Addini da qarya. ‘Yan Shi’a da ‘yan xariqa sun haxu a kan wannan illa. Dukkaninsu suna gaskata hadisan qarya maudu’ai, suna yin aiki da su a addini kuma suna qago su domin tallata bidi’arsu da tallafa mata. Su ‘yan Shi’a dama addininsu baki xayansa a kan
192
qarya aka gina shi, kuma a cikin qungiyoyin bidi’a kaf babu masu qaryarsu. Su kuwa ‘yan xariqa ana iya cewa suna da dama-dama idan aka gwada su da Rafilawa, amma su ma ba su da dama wajen qaga hadisai da kitsa almarori, musamman na karamomin waliyai.
Na goma: Imani da Ilmin Voye. Qungiyoyin Rafilawa da Sufaye sun yi ban gaskiya da ilmin voye. Shi ilmin voye, wanda wani yayi suke kira Ilmul Baxini ko Ilmul Ladunni, wani ilmi ne na addini wanda ba’a koyar sa a wajen kowa sai imamin Shi’a ko shaihin Sufaye. Wani abin sha’awa shi ne, duka qungiyoyin biyu suna mayar da tushen wannan ilmi ga Sayyidina Ali (RA), inda suke da’awar cewa sun gado shi daga wurinsa. Ta hanyar wannan ilmi ne suke yaxa bidi’o’insu da qarerayinsu da vatansu. Ko ba’a faxi ba, wannan ja’irin ilmi bai zama hujja a kan kowa sai vatacce kuma Ali binu Abi Xalib barrantacce ne daga gare shi. Wannan ilmin wahayin Shaixan ne kawai da wasuwasinsa.
Na sha xaya: Bautar kabari. Wani abu kuma da ya haxa ‘yan Shi’a da ‘yan xariqa shi ne ziyarorin shirka da bidi’a zuwa qaburburan annabawa da salihan bayi, kai har ma da dujalai da azzaluman sarakuna da sauransu.
193
Duk abinda Shari’a ta hana dangane da kabari, kamar gina shi ko yin gini a kansa; gina masallaci a kansa ko a kusa da shi da yin sallah a wurinsa; kewaya shi (yin xawafi da shi); shafar sa don neman albarka da sumbatar sa; xebo qasarsa da haki ko ganyensa domin magani; da duk wani abu da ya shafi biki ko girmamawa a makwantai da kusheyi – duka wannan Sunnar Annabi (SAW) ingantacciya ta hana kuma amma ‘yan Shi’a da ‘yan xariqa suna yi. (Duba Nurul Albabi na Shaihu Xan Fodiyo da Tahzirus Sajid min Ittikhazil Quburi Masajid na Albani.)
Na sha biyu: Qin ‘yan Wahhabiya. Rafilawa da Sufaye suna nuna matuqar qiyayya ga waxanda suke kira ‘yan Wahhabiya, watau mabiyan Muhammad binu Abdilwahhab. A can baya mun kawo maganar Khumaini inda yake cewa ‘yan Shi’a za su rusa Makka da Madina saboda waxannan birane, a faxinsa, sun zama mafakar ‘yan Wahhabiya. Su kuwa ‘yan xariqa idan suka ce da mutum xan Wahhabiya to sun gama da shi, domin abinda suke nufi da wannan suna wai mai qin Annabi (SAW). Kuma sun yaxa wannan ma’ana a tsakanin jahilai ta
194
yadda aka wayi gari mutum ya fi ganin sauqin a ce masa Bayahude da a ce masa xan Wahhabiya.
Amma mene ne haqiqanin Wahhabiya? Shi Muhammad binu Abdilwahhab malami ne wanda ya yi tajdidin addini kuma ya yaqi bidi’a kamar yadda Shaihu Usman Xanfodiyo ya yi tajdidi kuma ya yaqi bidi’a. Abinda ya sa waxannan qungiyoyin bidi’a guda biyu suke qin sa da mabiyansa shi ne ya hana bautar kabari kuma ya rushe wasu qaburbura da ake ziyarar shirka zuwa gare su. Mabiyan xan Abdulwahhab ba sa kiran kansu ‘yan Wahhabiya kamar yadda ‘yan Tijjaniya da ‘yan Qadiriya suke kiran kansu da waxannan sunaye. Amma su suna kiran kansu da sunan Ahlus Sunna ko Salafiyawa, watau masu bin Alqur’ani da Sunna gwargwadon fahimtar magabatan al’umma: Sahabbai da Tabi’ai da waxanda suka bi su da kyautatawa. Haka nan, mabiyan xan Abdulwahhab ba sa bin sa a kan ta’assubanci, watau ba sa cewa sai shi ko qafar katako! Amma suna bin sa inda maganganunsa da ra’ayoyansa suka dace da hujja da dalili, kamar yadda suke bin sauran malaman Musulunci a kan wannan sharaxi: dacewa da hujja da dalili.
195
Kuma kamar yadda ‘yan Shi’a da ‘yan xariqa suka haxu a kan qin ‘yan Wahhabiya (Ahlus Sunna), haka suka haxu a kan qin duk mai bin Sunna kuma yana kira zuwa gare ta. Wannan ya sa a lokacin da wasu qungiyoyi suka fito suna kira zuwa ga Sunna kuma suna yaqar bidi’a, sai ‘yan xariqa suka yaqe su da duk abinda Allah ya hore musu na iko. Xaya daga irin hujjojin da suka bayar na yaqar su shi ne wai suna zagin waliyai. Amma da ‘yan Shi’a suka bayyana suna zagin Sahabban Manzon Allah, suna kafirta su, sai yawancin Sufaye suka rungume su, ba sa ko son a ambaci laifinsu. Wannan sai ya tona asirin malaman xariqa, a lokacin da munafincinsu da cin amanarsu ga Musulunci suka bayyana a fili.
Bayan bayanai da muka gabatar a wannan littafi, a yanzu muna da qarfin guiwa cewa mai karatu ya samu masaniya dangane da haqiqanin addinin ‘yan Shi’a. Mun ga tushensu, tarihinsu da rabe-raben ressansu. Mun ga manyan aqidojinsu guda shida waxanda suka yi tarayya a kai kuma waxanda da su ne suka yi hannun riga da sauran Musulmi. Haka zalika mun ga matsayin Shi’a a cikin al’umma da baqin tarihinsu mai cike da garari da
196
mugun alkaba’i ga al’ummar Musulmi. Haka kuma, mun ga Fiqihunsu da yadda suke halasta abinda Allah ya haramta domin neman yaxa alfasha da fasadi a bayan qasa. Sa’an nan daga bisani mun ga yadda wannan shu’umar qungiya ta samu shigowa wannan qasa, kuma ta yaxu sakamakon gafalar malamai, gazawar masu mulki da jahilcin mabiya.
Bayan haka, ina ganin mai karatu zai yarda da ni idan na ce wajibin al’umma ne baki xaya su tashi su yaqi wannan qungiya. Dalili saboda, da farko ita qungiyar vata ce, wacce ta yi nesa da Musulunci littafinsa da Sunnarsa. Na biyu, saboda ita tushen fitina ce wacce idan ta ci gaba da yaxuwa to dole ne ta kai ga tashin hankali da zubar da jinni a tsakanin jama’a. Abinda muka riga muka gani na kashe-kashe da ‘yan wannan qungiya suka yi a wurare daban-dabam a qasar nan ya isa shaida.
Saboda haka, muna ba da shawarwari guda biyu kamar haka:
Ga Malamai. Shawararmu ga malamai ita ce su yi amfani da hikima wajen wa’azi da kira da wayarwa, saboda yawancin masu kiran kansu ‘yan Shi’a yaudarar su ake yi; amma ba su san haqiqanin qungiyar ba. Da
197
yawansu idan suka fahimci haqiqaninta za su bar ta da yardar Allah.
Ga Hukuma. Shawararmu ga mahukunta su yi amfani da iko da Allah ya ba su don kare addini da rayuka da dukiyoyin talakawansu. Wannan haqqi ya fi nauyi a kan gwamnatocin jihohi da suke aiwatar da Shari’a. Wajibi ne waxannan gwamnatoci su xauki matakan
Rufe makarantun ‘yan Shi’a waxanda suke yaxa miyagun aqidojinsu ga yaran al’umma a cikinsu.
Hana ‘yan Shi’a koyarwa a makarantun hukuma da masu zaman kansu, tun daga nazare har zuwa jami’o’i.
Qwace kadarorinsu, kamar gidaje da suke voye makamai kuma suna vata yara mata da sunan mutu’a a cikinsu.
Bincike da gano hanyoyin da suke samun kuxaxe daga qasashen waje, kamar gwamnatin qasar Iran da wasu qungiyoyi a qasar Lebanon da sauransu.
Kakkave hannun ofishin jakadancin qasar Iran a Nijeriya daga harkokin Musulmin qasar nan da
198
katse duk wata hanyar sadarwa tsakaninsa da ‘yan Shi’a.
A qarshe, muna roqon Allah Maxaukaki da ya shiryi al’ummar Annabi baki xaya. Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce, ya ba mu ikon bin ta; ya nuna mana qarya qarya ce, ya ba mu ikon nesantar ta. Tsarki ya tabbatar maka, ya Ubangiji, tare da godiya a gare ka. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai kai. Ina neman gafararka, ina tuba zuwa gare ka.
199
‚Wanda duk ya kafirta Sahabbai ko ya ce al’umma ta bata, to shi kafiri ne. Haka nan duk wanda ya yi shakkar kafircinsa, shi ma kafiri ne.‛
Shehu Mujaddadi Danfodiyo
‚Wanda yake zagin Sahabban Annabi (S.A.W) bai da rabo a Musulunci.‛